Yadda Walkiya Ta Fado kan Mata Mai Ciki Ta Mutu har Lahira a Bauchi

Yadda Walkiya Ta Fado kan Mata Mai Ciki Ta Mutu har Lahira a Bauchi

  • Mata uku ciki har da mai juna biyu da wata mai shayar da jariri sun rasa rayukansu sakamakon wata walƙiya da ta bugi wani gida a jihar Bauchi
  • Lamarin ya faru ne a kauyen Gambiri da ke karamar hukumar Bauchi, yayin da jaririn wata daga cikin matan ya tsira da ransa
  • Rundunar 'yan sandan Bauchi ta tabbatar da aukuwar lamarin, yayin da al'ummar yankin suka shiga jimami sakamakon mutuwar matan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Bauchi – Mata uku ciki har da wata mai juna biyu da wata da ta haihu kwanaki bakwai da suka gabata sun mutu bayan wata walƙiya ta bugi dakin da suke zaune a kauyen Gambiri da ke karamar hukumar Bauchi.

Lamarin ya faru ne da misalin karfe 5:29 na yammacin ranar Litinin, wanda ya jefa al'ummar yankin cikin alhini da jimami.

Kara karanta wannan

Yadda dalibin tsangaya ya tsallake rijiya da baya lokacin da abokansa 4 suka rasu a Kano

Yadda ake walkiya a sama
Lokacin da aka yi walkiya a wani yanki na kasar Spain. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Daily Trust ta rahoto cewa daya daga cikin mazauna yankin, Abubakar Hussain, ya tabbatar da cewa an binne gawarwakin wadanda suka mutu da misalin karfe 11:00 na safiyar ranar Talata.

Waye walƙiya ta kashe a Bauchi?

Abubakar Hussain ya bayyana sunayen biyu daga cikin wadanda suka rasu a matsayin Hauwa Juli, wadda ta haihu kwanaki bakwai kafin aukuwar lamarin, da kuma diyarta mai suna Fatima.

Ya ce mace ta uku mai suna Habiba, wadda ke dauke da juna biyu, 'yar'uwar Hauwa Juli ce. Sai dai a cewarsa, jaririn da Hauwa Juli ta bari ya tsira daga wannan mummunan lamari.

Hussain ya ce:

"Abin mamaki guda da ya faru shi ne yadda Allah Madaukakin Sarki ya kare sabon jaririn Hauwa Juli daga wannan masifar."

Ya kara da cewa mutuwar matan ta girgiza mazauna Gambiri matuka, inda al'ummar yankin suka shiga jimami tare da dakatar da wasu daga cikin harkokinsu.

Kara karanta wannan

Sojoji sun ɗana tarko, an daƙile harin garkuwa da mutane a Zamfara

Taswirar jihar Bauchi
Taswirar jihar Bauchi a Najeriya. Hoto: Legit
Source: Original

Bayanin 'yan sandan Bauchi

Da aka tuntubi rundunar 'yan sandan jihar Bauchi, kakakin rundunar, SP Nafiu Habib, ya tabbatar da aukuwar lamarin.

Ya ce:

"Haka ne, gaskiya ne cewa wata walƙiya ta kashe mutane uku a kauyen Gambiri."

Batun lalata layin dogo

A wani labarin kuma, rundunar 'yan sandan jihar Bauchi ta ce ta samu nasarar kwato wasu kayan aikin layin dogo da aka lalata a unguwar Doya da ke cikin birnin Bauchi.

A cewar wata sanarwa da rundunar ta fitar, jami'anta sun samu bayanan sirri kan zargin lalata kadarorin layin dogo a ranar 17 ga watan Agustan 2026.

Jami'an 'yan sanda sun bi sawun kayan da aka sace zuwa wani gida da ke unguwar Doya, inda suka kwato kayan tare da cafke wani mutum mai suna Abubakar Sanusi.

A sakon da ta wallafa a Facebook, rundunar ta ce bincike na ci gaba domin gano tare da cafke sauran wadanda ake zargi da hannu a lamarin.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sama da 100 sun tafka ta'asa yayin wani hari a Katsina

An kashe wata mata a otel

A wani labarin, mun ruwaito cewa wata mata mai matsakaicin shekaru ta rasa rayuwarta bayan da wani mutum ya yi zargin sare mata kai a cikin wani dakin otal da ke karamar hukumar Girei a jihar Adamawa.

Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne bayan matar da wani mutum suka sauka a wani otal mai suna Novex a ranar Juma'a.

Kakakin rundunar 'yan sanda, SP Suleiman Nguroje, ya tabbatar da cewa an cafke wanda ake zargi, yayin da bincike ke gudana domin gano cikakkun bayanai kan lamarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng