Mata, Manoma Sun Kife a Kwale Kwale, an Bazama Neman Su a Ruwan Jigawa
- Mutum ɗaya ya rasa ransa yayin da mutane 39 suka ɓace bayan wani kwale-kwale ɗauke da manoma da ma'aikata ya kife a Jigawa
- Yawancin fasinjojin da ke cikin kwale-kwalen mata manoma ne da ke kan hanyarsu ta zuwa gonaki lokacin da hatsarin ya faru
- 'Yan sanda, hukumar ba da agajin gaggawa da mazauna yankin sun fara aikin ceto domin gano sauran fasinjojin da suka ɓace
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jigawa – Rundunar 'Yan Sandan Jihar Jigawa ta tabbatar da mutuwar mutum ɗaya tare da ɓacewar wasu mutum 39 bayan wani kwale-kwale da ke ɗauke da fasinjoji sama da 40 ya kife a ƙauyen Malamawar Yan Dutse da ke Ringim.
Rahotanni sun nuna cewa hatsarin ya faru ne da misalin ƙarfe 4:30 na yammacin ranar Lahadi lokacin da kwale-kwalen ke kan hanyarsa, inda mafi yawan fasinjojin mata manoma da ma'aikatan gona ne.

Source: Getty Images
'Yan sanda sun wallafa a Facebook cewa lamarin ya jefa al'ummar yankin cikin alhini yayin da iyalan waɗanda ke cikin kwale-kwalen ke ci gaba da jiran labarin makomar 'yan uwansu.
'Yan sanda sun fara bincike
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin rundunar 'yan sandan Jihar Jigawa, SP Shi'isu Adam, ya ce rundunar ta samu rahoton hatsarin cikin gaggawa, inda ta tura jami'anta tare da sauran hukumomin agaji zuwa wurin da abin ya faru.
A wata tattaunawa ta wayar tarho, ya bayyana cewa an samu nasarar gano gawar mutum ɗaya, yayin da ake ci gaba da aikin bincike da ceto domin gano sauran mutum 39 da har yanzu ba a san inda suke ba.
Ya ce rundunar na aiki tare da sauran hukumomin agaji domin bincikar yankin gaba ɗaya, tare da alƙawarin sanar da jama'a duk wani sabon bayani da zarar an samu.
SEMA ta yi karin haske
Punch ta wallafa cewa daraktan tsare-tsare na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Jigawa (SEMA) ya tabbatar da faruwar hatsarin.
Ya bayyana cewa yawancin waɗanda abin ya shafa mata manoma ne da ma'aikatan gona da ke kan hanyarsu ta zuwa gonaki lokacin da kwale-kwalen ya kife.
A cewarsa, har yanzu ba a tantance ainihin musabbabin hatsarin ba, domin ana ci gaba da gudanar da bincike.

Source: Original
Ya ƙara da cewa jami'an ceto na ci gaba da aiki domin gano adadin mutanen da aka ceto da kuma waɗanda suka ɓace, yana mai cewa ba za a iya tabbatar da cikakken adadin waɗanda abin ya shafa ba har sai an kammala aikin.
Ana aikin ceto matan
Shugaban kwamitin ba da agajin gaggawa na ƙaramar hukumar Ringim, Habibu Dauda, ya ce wadanda suka iya ruwa da mazauna yankin sun haɗa kai da jami'an agaji wajen gudanar da aikin ceto.
Ya buƙaci al'umma da su kwantar da hankalinsu tare da gujewa yaɗa rahotannin da ba a tabbatar da sahihancinsu ba.
Mutum 500 sun nutse a ruwa
A wani labarin, mun ruwaito cewa ana fargabar fiye da mutum 500 daga ƙabilar Rohingya sun rasa rayukansu bayan wasu kwale-kwale biyu da ke ɗauke da su sun nutse a Myanmar.
Rahotanni sun nuna cewa kwale-kwalen sun tashi daga jihar Rakhine a ƙarshen watan Yunin 2026, inda suka ɗauki mafi yawan 'yan Rohingya, ciki har da wasu da suka fito daga sansanonin 'yan gudun hijira.
A cewar hukumomin UNHCR) da IOM ɗaya daga cikin kwale-kwalen mai ɗauke da mutum kusan 250 ya ɓace jim kaɗan bayan tashinsa, yayin da ɗayan da ke ɗauke da mutum kusan 280.
Asali: Legit.ng


