Bayan Wa'adin Walson Jack Ya Kare, Tinubu Ya Nada Sabon Shugaban Ma’aikatan Tarayya
- Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya nada Abel Olumuyiwa Enitan a matsayin sabon Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya
- Enitan zai maye gurbin Didi Esther Walson-Jack wadda za ta yi ritaya bayan ta cika shekara 60 da haihuwa, inda gwamnati ta yi mata fatan alheri
- Sanarwar da gwamnatin tarayya ta fitar ta kuma bayyana lokacin da sabon shugaban ma’aikatan zai fara aiki gadan-gadan domin ci gaban kasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya nada Mista Abel Olumuyiwa Enitan a matsayin sabon Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya, inda zai fara aiki daga ranar 27 ga Agusta, 2026.
Enitan, wanda ya fito daga Jihar Osun, shi ne ma’aikacin gwamnati mai mukamin Sakataren Din-din-din mafi girma a cikin Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya.

Source: Facebook
Sanarwar da hadimin shugaban kasa Dada Olusegun ya fitar a shafin X ta ce Enitan zai maye gurbin Mrs Didi Esther Walson-Jack, wadda za ta yi ritaya daga aikin gwamnatin tarayya nan ba da jimawa ba bayan ta kai shekarun ritaya da doka ta tanada, wato shekara 60.
Waye sabon shugaban ma'aikatan gwamnati
Enitan ya shafe shekaru bakwai da watanni bakwai yana rike da mukamin babban sakatare inda ya yi aiki a ma’aikatar harkokin ’yan sanda, ma’aikatar harkokin jin kai da kuma ofishin mataimakin Shugaban Kasa.

Kara karanta wannan
FAAC ta cika aljihun gwamnatin Tinubu da jihohi, an raba abin da ba a taba samu ba
Shugaba Tinubu ya bayyana jin dadinsa da irin hidimar da Walson-Jack ta yi wa kasa, yana mai yabawa irin sauye-sauye, tasiri da sabbin abubuwan kirkire-kirkire da aka samu a Ma’aiatan Gwamnatin Tarayya a lokacin mulkinta.
Ya yi mata fatan samun nasara da cikakkiyar rayuwa bayan ta kammala aikin gwamnati, tare da mika godiyar al’ummar Najeriya bisa shekaru da ta sadaukar wajen yi wa kasa hidima.
Tinubu ya ba da umarni
Shugaban ya kuma umarci Enitan da ya tabbatar da ci gaba da inganta sauye-sauye da sabbin tsare-tsaren da aka fara a ma’aikatan gwamnati, tare da kara kwarewa da inganci a ayyukan gwamnati.

Source: Twitter
Ya ce ya kamata sabon shugaban ma’aikatan ya gina tsarin ma’aikatan gwamnati mai kwarewa, mai bayar da dama bisa cancanta, mai rikon amana, mai kirkire-kirkire da kuma mai saurin amsa bukatu da muradun ’yan Najeriya.
Fadar Shugaban Kasa ta ce ana sa ran Enitan zai yi amfani da kwarewarsa da kuma zurfin fahimtarsa kan yadda Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya ke gudanar da ayyukansu wajen taimaka wa gwamnati wajen cimma manufofin Renewed Hope Agenda.
Gwamnatin Tinubu ta amince da kashe
A baya, mun kawo labarin cewa Majalisar zartarwa ta tarayya wato FEC ta amince da aikin gini da gyaran hanyoyi da za su ci N438bn a kasar nan a sassadaban-daban na kasar nan.
Matakin da aka dauka ya hada da amincewa da aikin tashoshin tireloli da wasu manyan hanyoyi a wani tsari da ‘yan kasuwa inda za a sake gyara da gina muhimman hanyoyi a jihohin Ekiti, Rivers da Ogun.
An kuma yi na’am da wasu sauye-sauye da aka samu a aikin titin Abeokuta-Iboro-Ilaro sakamakon canjin kwalta zuwa siminti. A Rivers, Majalisar FEC ta amince da aikin titin Port Harcourt-Eleme Junction-Onne a N74bn.
Asali: Legit.ng

