Gwamnatin Kaduna Ta Yi Fatali da Bukatar El Rufa'i na Sauya Masa Alkali, An Ji Dalili
- Alkalin alkalan jihar Kaduna ya ce babu dalilin sauya alkalin da ke sauraron shari’ar Nasir El-Rufa’i zuwa wani alkali kamar yada tsohon gwamnan na nema
- An umarci Mai Shari’a Darius Hyet Khobo ya ci gaba da sauraron shari’ar tare da yanke hukunci bisa doka da adalci bayan ya gama sauraron batun
- El-Rufa’i ya nemi sauya alkalin, yana zargin son kai da kuma cewa alkalin ya riga ya yanke masa hukunci tun kafin a kammala shari’ar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano –Babban Alƙalin Jihar Kaduna, Mai Shari’a Muhammad Tukur Aliyu, ya ƙi amincewa da buƙatar sauya shari’ar tsohon Gwamnan jihar, Malam Nasir El-Rufa’i, daga hannun alkalin da ke sauraron ta zuwa wani alkali.
Alƙalin ya ce babu wani dalili na kwace fayil ɗin shari’ar daga hannun Mai Shari’a Darius Hyet Khobo na Babbar Kotun Jihar Kaduna, wanda ke jagorantar shari’ar El-Rufa’i.

Source: Twitter
A cikin wata wasiƙa ta cikin gida mai ɗauke da ranar 19 ga Agusta, wadda jaridar ThisDay ta gani, Babban Alƙalin ya umarci Mai Shari’a Khobo da ya ci gaba da sauraron shari’ar tare da tabbatar da an kammala ta bisa tanadin doka da adalci.
An yi magana kan shari'ar El-Rufa'i
The Nation ta kawo labarin cewa El-Rufa’i na fuskantar tuhume-tuhume tara da aka yi wa kwaskwarima a ranar 10 ga Afrilu, 2026, waɗanda suka shafi zargin damfara ta hanyar karɓar kuɗi da kuma aikata wasu laifukan cin hanci da rashawa.
Ko da yake tsohon gwamnan ya musanta aikata laifukan, ya ci gaba da kasancewa a hannun Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa da sauran Laifuka, ICPC, tun bayan kama shi da kuma kin amincewa da buƙatunsa na beli da Mai Shari’a Khobo ya yi.
Kin bayar da belin El-Rufa’i da Mai Shari’a Khobo ya yi ne ya sa tsohon gwamnan ya shigar da ƙorafi ga Babban Alƙalin, inda ya zargi alkalin da nuna son kai da kuma yanke shawarar hukunta shi tun kafin a kammala shari’ar.

Kara karanta wannan
Abubuwan da ya dace a sani game da yarjejeniyar da aka yi tsakanin Musulmi da Kiristocin Najeriya
Lauyoyin El-Rufa'i sun yi magana
Lauyoyin tsohon gwamnan karkashin Ubong Akpan ne suka gabatar da ƙorafin farko a ranar 30 ga Yuni, yayin da El-Rufa’i da kansa, wanda kuma jigo ne a ADC, ya rubuta ƙorafi na biyu a ranar 6 ga Yuli, 2026.
Sai dai bayan nazarin ƙorafe-ƙorafen, Babban Alƙalin ya ce bai ga wani dalili da zai sa ya yi amfani da ikonsa na gudanarwa wajen sauya shari’ar zuwa hannun wani alkali ba.

Source: Original
A cikin wasiƙar da ya aika wa Mai Shari’a Khobo, ya ce:
“Na nazarci kuma na yi la’akari da ƙorafe-ƙorafen da aka gabatar a ranakun 30 ga Yuni, 2026 da 6 ga Yuli, 2026, daga lauyan wanda ake tuhuma da kuma wanda ake tuhumar da kansa, tare da amsoshin Mai Shari’a ga waɗannan ƙorafe-ƙorafe na ranar 16 ga Yuli, 2026.”
Ya ce bisa ikon da doka ta ba shi ƙarƙashin Sashe na 111(1) da (4) na Dokar Gudanar da Shari’o’in Laifuka ta Jihar Kaduna ta 2017, an kafa kwamitin ƙwararrun lauyoyi uku domin bincikar ƙorafe-ƙorafen.
Kwamitin ya gabatar da rahotonsa a ranar 18 ga Agusta, 2026 kuma an gano babu wani dalili da zai jawo a canja alkalin da ke sauraron shari'ar.
El-Rufa'i ya tafi kotu
A baya, mun samu labarin cewa tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, ya shigar da ƙarar kotu ya na kalubalantar kan ICPC bisa zargin hana matarsa da ɗansa ziyartarsa.
Nasir El-Rufai ya ce jami’an hukumar yaki da rashawa ta ICPC sun hana iyalansa kawo masa abinci, magunguna da sauran abubuwan da yake buƙata, ba tare da wata doka ko umarnin kotu ba.
Tsohon gwamnan jihar Kaduna ya kuma zargi jami’an hukumar da tare matarsa da ɗansa tare da tsoratar da su a ranar 7 ga Yuli, 2026 lamarin da ya ce ya saɓa wa haƙƙoƙinsa na dan adam.
Asali: Legit.ng

