Arziki Ya Karu: Aliko Dangote Ya Samu Biliyoyin Daloli saboda Yakin Iran

Arziki Ya Karu: Aliko Dangote Ya Samu Biliyoyin Daloli saboda Yakin Iran

  • Attajirin Afirka, Aliko Dangote, ya ƙara samun sama da dala biliyan 5 sakamakon karuwar buƙatar man fetur tun bayan barkewar yaƙin Iran
  • Matatar man Dangote da ke Legas ta samu karuwar buƙatar kayayyakin man fetur a Afirka da sauran sassan duniya saboda yakin
  • Matatar wadda ta kai darajar dala biliyan 20 ta zama ɗaya daga cikin manyan masu fitar da man jiragen sama da dizal zuwa kasuwannin duniya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Attajirin Afirka kuma ɗan kasuwa mafi arziki a nahiyar, Aliko Dangote, ya ƙara samun sama da dala biliyan 5 a arzikinsa sakamakon karuwar kasuwancin matatar man Dangote tun bayan barkewar yaƙin Iran.

Dangote, mai shekaru 69, ya gina mafi yawan arzikinsa ne ta hanyar samar da kayayyaki kamar gishiri, sukari da siminti, amma a yanzu matatar man da ya gina a Legas ce ke ƙara masa kuɗin shiga.

Kara karanta wannan

Yadda dalibin tsangaya ya tsallake rijiya da baya lokacin da abokansa 4 suka rasu a Kano

Alhaji Aliko Dangote
Aliko Dangote yana bayani a wajen wani taro a Amurka. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

The New York Times ta ruwaito cewa karuwar buƙatar kayayyakin man fetur a Afirka da sauran sassan duniya bayan fara yaƙin Iran ta taimaka wajen ƙara darajar arzikin Dangote.

Yaƙin Iran ya karfafa Aliko Dangote

Duk da yawan ɗanyen mai da Afirka ke da shi, nahiyar har yanzu tana dogaro sosai da shigo da tataccen man fetur daga ƙasashen waje.

Hare-haren Ukraine kan matatun mai da jiragen dakon mai na Rasha sun rage yawan man da ake fitarwa zuwa Afirka.

Haka kuma, jigilar mai daga Turai da yankin Tekun Fasha ta ragu sosai tun bayan rufe mashigar Hormuz da Iran ta yi, wanda ke ɗaukar kusan kashi 1 cikin 5 na man da ake samarwa a duniya.

Wannan yanayi ya sa farashin abinci, takin zamani da man fetur ya yi tashin gwauron zabo, lamarin da ya ƙara jefa wasu daga cikin al'ummomin Afirka cikin matsin tattalin arziki.

Sai dai Dangote da kamfaninsa sun kasance cikin waɗanda suka samu damar cin gajiyar wannan yanayi saboda karuwar buƙatar man da matatar ta ke samarwa.

Kara karanta wannan

Dalibai 4 na makarantar haddar Kur'ani sun mutu lokaci guda a jihar Kano, an gano dalili

Matatar Dangote ta samu karbuwa

Rahoton ya ce jigilar man jiragen sama daga matatar Dangote zuwa kasuwar Amurka ta fara ne a karon farko a bana.

Daniel Evans, mataimakin shugaban kamfanin S&P Energy, ya bayyana cewa Matatar Dangote ta kasance mafi girman mai fitar da man jiragen sama a duniya a watan Afrilu da Mayun 2026.

Haka kuma, Devakumar Edwin, mataimakin shugaban Dangote Industries, ya ce a watan da ya gabata matatar ta kasance mafi girman mai samar da man jiragen sama da dizal ga Turai.

Matatar Dangote a Legas
Wani sashe na matatar Dangote da ke jihar Legas. Hoto: Dangote Industries
Source: Getty Images

Rahoton Billionaires Africa ya bayyana cewa Alhaji Aliko Dangote ya samu karin dala biliyan 5 bayan rufe mashigar Hormuz.

Trump zai yaki tattalin Iran

A wani labarin, mun ruwaito cewa Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa zai ƙara tsaurara matakan tattalin arziki kan Iran da kuma duk wata ƙasa da ke taimaka wa Tehran ko kasuwanci da ita.

Kara karanta wannan

Yadda Najeriya ta fara shirin kera makamai da motoci masu sulke

Trump ya ce zai ƙaddamar da abin da ya kira "mafi tsananin yaƙin tattalin arziki da aka taɓa yi wa wata ƙasa", yana mai barazanar ɗaukar matakai kan cibiyoyin kuɗi da kamfanonin da ke tallafa wa Iran.

Matakin na zuwa ne bayan karewar yarjejeniyar tsagaita wuta ta kwanaki 60 tsakanin Amurka da Iran, ba tare da samun wata mafita ta diflomasiyya ko ta soji da za ta kawo ƙarshen rikicin ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng