Jami'an Tsaro Sun Yi Wa 'Yan Bindiga Rubdugu a Katsina yayin Dakile Mummunan Shirinsu
- An samu nasarar hallaka ‘yan bindiga sama da 20 bayan jami’an tsaro sun dakile yunkurin sace mazauna kauyen Gidan Bawa da ke Kandarawa a jihar Katsina
- Kimanin ‘yan bindiga 40 da ke biyayya ga Isiya Kwashen Garwa ne suka mamaye kauyen da nufin sace mata da yara
- Jami’an tsaro sun ceto mutanen da aka yi garkuwa da su tare da kwato shanu 19 da aka sace bayan kazamin artabun da suka yi da 'yan bindigan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Katsina - Jami’an tsaro sun hallaka akalla ‘yan bindiga 24 bayan sun dakile yunkurin sace mutane a jihar Katsina.
Jami'an tsaron sun dakile yunkurin 'yan bindigan ne na sace mazauna kauyen Gidan Bawa da ke gundumar Kandarawa, karamar hukumar Bakori a jihar Katsina.

Source: Original
Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, cZagazola Makama, ya bayyana hakan a shafinsa na X.
Majiyoyi sun ce kimanin ‘yan bindiga 40 masu biyayya ga fitaccen jagoran ‘yan bindiga, Isiya Kwashen Garwa, suka mamaye kauyen a ranar Talata, 18 ga watan Agustan 2026 da nufin yin garkuwa da wasu mazauna yankin, musamman mata da yara.
Aikin da ya hada da dakarun sojojin Najeriya, jami’an DSS da mambobin Katsina Community Watch Corps ya biyo bayan samun bayanan sirri da suka bankado shirin harin.
An shirya sace mutane da yawa
'Yan bindigar sun shirya yin garkuwa da mutane da yawa kamar yadda aka yi a baya-bayan nan a Woro da ke jihar Kwara a yankin Arewa ta Tsakiya.
Bayanan sirrin da aka samu sun nuna cewa manufar shirin sace mutanen ita ce kunyata gwamnati.
Bayan samun bayanan, jami’an DSS sun tattara mambobin Community Watch Corps da Civilian Joint Task Force (CJTF) daga sansanin Guga domin tare ‘yan bindigar.
An ceto mutanen da aka sace
Jami’an tsaron sun yi wa ‘yan bindigar kwanton bauna, inda suka hallaka 24 daga cikinsu tare da ceto mutanen kauyen da aka yi garkuwa da su.
Jami’an tsaron sun kuma kwato shanu 19 da aka sace a yayin samamen da suka kai kan miyagun 'yan bindigan.
Hakazalika jami’an tsaro na ci gaba da kokarin gano inda ‘yan bindigar da suka tsere suke domin cafke su.

Source: Twitter
'Yan bindiga sun kashe mutane a Katsina
A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan bindiga dauke da makamai sun kashe akalla mutane uku, yayin da wasu biyar suka samu raunuka, bayan da suka kai hari garin Dansarai da ke karamar hukumar Malumfashi ta jihar Katsina.
Maharan sun kuma yi awon gaba da wata mata tare da satar dabbobi da ba a bayyana adadinsu ba a yayin harin da suka kai garin da misalin karfe 5:00 na yamma.
'Yan bindigar sun iso ne a kan babura kusan 50, inda kowane babur ke dauke da mutane uku dauke da makamai kuma sun shafe kusan shafe sa’o’i biyar suna gudanar da ayyukansu na barna da ta'addanci a kauyen.
Asali: Legit.ng

