Wata mai juna biyu ta mutu bayan maciji ya sare ta cikin bandaki
Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un! Allah ya yiwa wata mata mai dauke da cikin watanni takwas rasuwa dalilin saran maciji da sukayi gamo a Ban daki a unguwar Kinkinau, jihar Kaduna. Rariya ta ruwaito.
Macijin ya cijeta ne a bayi bayan da ta tsuguna biyan bukata kan matsugunin bayin zamani wato 'Toilet seat'.
Da wuri aka garzaya da ita Asibitoci da dama amma duk suka ce basu da maganin dafin wannan Maciji.
Kanin mijin Matar mai suna ZunNoorayne ne ya wallafa labarin a kafar sada zumuntar zamani ta tuwita, da yammacin ranar Alhamis.
Kamar yadda ya wallafa, marigayiyar ta je zagayawa bayi ne a sa'o'in farko na ranar Alhamis amma kuma a rashin sani, macijin na cikin matsugunin.
Yace: "Nan take aka garzaya da ita asibiti bayan an fahimci abinda ya faru. Tashin hankali na farko shine rashin titi mai kyau. Sai kuma asibitoci da suka ce basu ajiye maganin dafi."
Daga Karshe ZunNoorayne ya bayyana cewa, ta rasu.
Allah yajikanta da rahama yasa aljannace makomarta. Amin
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng