Abuja: Maciji ya sari ɗan babban limami a daji bayan ya tsere daga hannun masu garkuwa

Abuja: Maciji ya sari ɗan babban limami a daji bayan ya tsere daga hannun masu garkuwa

  • Maciji ya sari Aliyu Abubakar Usman, dan babban limamin Yangoji a daji yayin da ya tsere daga sansanin masu garkuwa da mutane
  • Wani daga cikin 'yan uwan limamin ya tabbatar da afkuwar lamarin inda ya ce a halin yanzu Usman yana karbar maganin gargajiya
  • Har yanzu dai limamin da daya dansa guda daya suna hannun masu garkuwan da suke neman a biya Naira miliyan 10 na fansa kafin su sako su

FCT, Abuja - Maciji ya sari daya daga cikin 'ya'yan babban limamin masallacin Yangoji da ke karamar hukumar Kwali a Abuja, Aliyu Abubakar Usman mai shekaru 22.

Daily Trust ta ruwaito cewa yan bindiga sun sace babban limamin, Abdullahi Abubakar Gbedako, wanda kuma shine mataimakin shugaban makarantar sakandare ta JSS Kwaita tare da yaransa biyu.

Kara karanta wannan

Da duminsa: IGP ya bukaci sunayen 'yan sandan da har yanzu ba a biya ba a Anambra

Abuja: Maciji ya sari dan babban limami a daji bayan ya tsere daga hannun masu garkuwa
Maciji ya sari dan babban limami a daji bayan ya tsere daga hannun masu garkuwa a Abuja. Hoto: Daily Trust
Asali: Depositphotos

Makonni biyu da suka gabata, 'yan bindiga sun kutsa gidan limamin na Yangoji.

Wani daga iyalan limamin ya tabbatar da lamarin

Daya daga cikin iyalan babban limamin wanda ya nemi a sakayya sunansa ya shaidawa Daily Trust cewa maciji ya sari yaron da aka sace yayin da ya ke hanyarsa ta tserewa daga sansanin masu garkuwar.

Ya ce:

"Babban dan limanin, Usman Abubakar, ya yi nasarar tserewa daga hannun masu garkuwar a ranar Alhamis da ta gabata amma maciji ya sare shi a cikin dajin kuma yana nan ana masa maganin gargajiya amma ba zan iya bayyana wurin ba saboda tsaro.
"Kamar yadda ka sani har yanzu kaninsa da mahaifinsa suna hannun masu garkuwa da mutanen."

Har yanzu limamin da dansa guda na hannun yan bindigan

Kara karanta wannan

Babban magana: Wasu mutane 2 masu sana'ar tura amalanke sun mutu yayin faɗa kan N200 kacal

Ya cigaba da cewa iyalan limamin suna nan suna fafutikan ganin yadda za su nemo kudi domin fanso limamin da dayan dansa.

Yan bindigan sun nemi a biya su Naira miliyan 10 kafin su sako babban limamin da yayansa biyu.

Mai magana da yawun yan sandan birnin tarayya Abuja, DSP Adeh Josephine bata daga waya ba ko amsa sakon kar ta kwana da aka aika mata har zuwa lokacin hada rahoton.

Sokoto: Yadda ƴan bindiga suka amshe miliyoyi daga basarake kuma suka ƙi sako waɗanda suka yi garkuwa da su

A wani rahoto daga Sokoto, 'Yan bindiga sun amshe Naira miliyan 2.2 (N2,200,000) a matsayin kudin fansa amma sun ki sakin mutane 20 da su ka sata.

Buzu, na biyu a hatsabibanci daga Bello Turji, duk da an biya shi makudan kudade don sakin mutane 20 da su ka sata a Gatawa ya murje ido ya lamushe kudin babu wani bayani.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kashe Limamin Masallacin Juma'a da yaki yarda a tafi da shi, sun sace yaransa

Premium Times ta ruwaito yadda ‘yan bindigan su ka aika wa dagacin Burkusuma da sarkin Rafi wasika inda su ka bayyana cewa su na bukatar N20,000,000 a matsayin kudin fansar wadanda su ka sata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel