Ma'ajin Kungiyar Izala a Najeriya, Hafiz Bala Yusuf Ya Rasu

Ma'ajin Kungiyar Izala a Najeriya, Hafiz Bala Yusuf Ya Rasu

  • Rahotanni sun bayyana cewa babban malamin ƙungiyar Izala na kasa, Hafiz Bala Yusuf, ya rasu a safiyar Laraba bayan fama da jinya da ya yi
  • Shugaban malaman Izala na jihar Gombe, Sheikh Hamza Adam Abdulhamid, ne ya sanar da rasuwar, yana bayyana marigayin a matsayin uba kuma amini
  • 'Yan Izala sun bayyana marigayin da ya kasance alaramma mai amana, dattako, haƙuri da juriya, sannan mai matuƙar sanin darajar mutane

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Filato – An shiga jimami bayan rasuwar Hafiz Bala Yusuf, ɗaya daga cikin manyan malaman Izala a Najeriya, wanda ya rasu a safiyar Laraba.

Hafiz Bala Yusuf ya kasance uba kuma amini na musamman ga Ash-Sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingre, kana Ma’ajin Ƙungiyar Izala a Najeriya.

Kara karanta wannan

Ana maganar 2027, Sanata Bello Mandiya ya riga mu gidan gaskiya

Hafiz Bala Yusuf
Hafiz Bala Yusuf da ya rasu. Hoto: Abdullahi Yakubu Dauda
Source: Facebook

Sheikh Hamza Adam Abdulhamid, shugaban malaman Izala na jihar Gombe, ya sanar da rasuwar a Facebook tare da yin addu’ar Allah Ya gafarta wa marigayin.

An bayyana halayen marigayin

Sheikh Hamza ya bayyana marigayin a matsayin Alaramma mai amana, dattako, juriya da haƙuri, tare da nuna matuƙar sanin darajar mutane.

Ya kuma roƙi Allah Maɗaukakin Sarki Ya gafarta masa, Ya jiƙansa da rahama, Ya haskaka kabarinsa, Ya yalwata masa cikinsa, sannan Ya sanya Aljannatul Firdausi ta zama makomarsa.

Za a sanar da lokacin jana’iza

A bayanan da Sheikh Hamaza Adam ya yi, ya bayyana cewa za a sanar da lokacin da kuma wurin da za a gudanar da jana’izar Hafiz Bala Yusuf da zarar an tabbatar.

Haka kuma, Hamza Muhammad Sani ya wallafa saƙon jimami a Facebook, yana roƙon Allah Ya gafarta wa marigayin kuma Ya sanya Aljannatul Firdausi ce makomarsa.

Mutane da dama sun bayyana alhini tare da yi wa marigayin addu’a a shafukan sada zumunta, inda suka roƙi Allah Ya jiƙansa da rahama, Ya haskaka kabarinsa, Ya kuma ba iyalansa da Izala haƙurin wannan babban rashi.

Kara karanta wannan

Samia Suluhu: An shiga jimami da shugabar kasar Tanzania ta yi babban rashi a rayuwa

Sheikh Sani Yahaya Jingir
Shugaban malaman Izala, Sheikh Sani Yahaya Jingir. Hoto: Hamza Muhammad Sani
Source: Facebook

Wani dan Izala a jihar Gombe, Abdullahi Yakubu Dauda ya bayyana Legit Hausa cewa marigayin ya shafe shekaru da dama yana yi wa addini hidima.

Ya ce kafin rasuwarsa, Hafiz Bala yana zaune a Jos, jihar Filato a layin Sarkin Mangu kuma ya yi fice wajen karantar wa a jihar da Najeriya baki daya.

An kashe jami'in banki a Imo

A wani labarin, mun ruwaito cewa wani manajan reshen bankin Polaris Bank, wanda aka bayyana da sunan Mista Ossy, ya rasu bayan wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane sun harbe shi.

Lamarin ya faru ne a yammacin Lahadi, lokacin da ma’aikacin bankin, wanda ke aiki a Owerri, ya kai ’ya’yansa jami’a, inda rahotanni suka ce ’yan bindigar sun tare shi yayin da yake cikin harabar makarantar.

A yayin harin, ’yan bindigar sun kuma yi awon gaba da wasu ɗalibai mata biyu, yayin da bankin ya bayyana cewa ’ya’yan marigayin sun samu tserewa daga wurin, amma shi bai samu damar tsira ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng