Magana Ta Girma: Kwankwaso Ya Aika Muhimman Sako ga Atiku game da Siyasa
- Rabiu Musa Kwankwaso ya aika wa Atiku Abubakar saƙo yayin wata ganawa da mabiyansa daga jihar Adamawa
- Kwankwaso ya buƙaci a isar wa Atiku saƙonsa da harshen Fulatanci, yana mai cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasan ya fi fahimtar harshen
- Jagoran NNPP ya shawarci Atiku ya koma kula da sarautar Waziri Adamawa, yana mai cewa shekarunsa sun yi yawa don jagorantar Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Rabiu Musa Kwankwaso ya aika da saƙo ga tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar game da siyasa.
Kwankwaso ya buƙaci waɗanda za su isar wa Atiku saƙonsa da su yi hakan da harshen Fulfulde, saboda ya fi fahimtar wannan harshe.

Source: Twitter
Kwankwaso ya bayyana haka ne yayin wata ganawa da mabiyansa daga Adamawa a wani bidiyo da Musaddiq T Soja ya wallafa a Facebook.
Shaguben da Kwankwaso ya yi ga Atiku
Ya ce Atiku, wanda ke riƙe da sarautar gargajiya ta Waziri Adamawa, ya kamata ya koma ya kula da wannan matsayi na gargajiya.
Kwankwaso ya bayyana cewa Atiku ya kamata ya mayar da hankali kan kula da sarautarsa, maimakon ci gaba da neman shugabancin Najeriya.
Ya ce shekarun Atiku sun yi yawa da zai iya ɗaukar nauyin jagorantar ƙasar, yana mai bayyana hakan yayin jawabin nasa a Adamawa.
Kwankwaso ya ce:
“Kafin ku bar garin nan, idan za ku iya, ku biya ta gidan Wazirin Adamawa, ku gaya masa da Fulatanci, harshen da ya fi fahimta, ku ce masa ya yi hakuri.
"Ya koma kan wannan sarauta ta Waziri, ya koma kanta saboda yanayi na shekaru da kuma na jikinsa, kula da Najeriya zai ba shi wahala."

Source: Facebook
Alkawarin da Kwankwaso ya yi ga Atiku
Haka kuma, Kwankwaso ya bayyana cewa idan suka samu nasara a zaɓen, za su kula da Atiku, ba tare da ƙarin bayani kan yadda za su yi hakan ba, cewar TRT Hausa.
Ya kara da cewa:
"Mu kuma idan Allah ya tabbatar mana mun yi nasara a zaben shekarar 2027, za mu kula da shi sosai."
"Musamman ku da kuka zo daga Adamawa, ga shugaban naku gaba daya, a san yadda za a yi a ba shi hakuri, wannan gargadar da Najeriya ke ciki ta dace da shi ne shekarun 1993 da suka wuce."
Jawabin Kwankwaso ya jawo hankali a Adamawa, musamman saboda yadda yake ƙara tsaurara kalaman siyasa yayin da ƙasar ke tunkarar babban zaɓen ƙasa.
Kalaman sun kuma ƙara nuna bambancin ra’ayi tsakanin Kwankwaso da Atiku, waɗanda dukkansu ke da tarihin shiga manyan fafutukar neman shugabancin Najeriya.
Atiku ya taya Rabi Kwankwaso murna
A baya, an ji cewa Atiku Abubakar ya tura sakon taya murna ga tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso yayin da yake bikin cika shekaru 68.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya ce Kwankwaso ya yi wa al'ummar Kano da ƙasa baki ɗaya aiki a muƙamai daban-daban da ya riƙe.
Kwankwaso wanda ya yi takarar shugaban kasa na NNPP a zaɓen 2023 ya cika shekara 68 a duniya yau Litinin, 21 ga watan Oktoba, 2024.
Asali: Legit.ng

