NiMet Ta Lissafo Jihohin Arewa da za a Yi Kwana 3 ana Ruwan Sama

NiMet Ta Lissafo Jihohin Arewa da za a Yi Kwana 3 ana Ruwan Sama

  • Hukumar Kula da Yanayi ta Najeriya (NiMet) ta yi hasashen yanayin gajimare da ruwan sama mai tsawa a sassa daban-daban na ƙasar daga Laraba zuwa Juma’a
  • NiMet ta ce za a samu yiwuwar ruwan sama da tsawa a jihohin Kano, Gombe, Bauchi, Kaduna, Jigawa, Yobe da sauran jihohin Arewa a cikin kwanakin
  • Hukumar ta kuma yi gargaɗin yiwuwar ambaliyar ruwa a wasu sassan Imo, Abia, Ebonyi, Akwa Ibom da Cross River, tare da yiwuwar iska mai ƙarfi kafin ruwan sama

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Hukumar Kula da Yanayi ta Najeriya, NiMet, ta yi hasashen samun yanayin gajimare da ruwan sama mai tsawa a sassa daban-daban na Najeriya daga Laraba zuwa Juma’a.

NiMet ta bayyana hakan ne a cikin hasashen yanayinta da ta fitar a Abuja ranar Talata, inda ta ce za a samu gajimare a wasu sassan Arewacin ƙasar ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Jirgin sojoji ya saki bama bamai a Zamfara, an kashe Kachalla Gurgu

Yara na wasa a ruwan sama
Wasu yara na tsalle a ruwan sama a Nafada, Gombe. Hoto: Lukman Haruna
Source: Facebook

Punch ta wallafa cewa hukumar ta ce akwai yiwuwar ruwan sama mai tsawa tare da ɗan ƙaramin ruwa da safe a wasu sassan Taraba da Kebbi.

Yiwuwar ruwan sama a jihohi

Daga baya da rana ko yamma, NiMet ta yi hasashen ruwan sama mai tsawa da matsakaicin ƙarfi a wasu sassan Taraba, Borno, Yobe, Bauchi, Sokoto, Katsina, Zamfara, Jigawa, Kano da Kaduna.

A yankin Arewa ta Tsakiya, hukumar ta ce za a samu ruwan sama mai tsawa tare da ruwa da safe a wasu sassan Nasarawa, Neja, Benue da Babban Birnin Tarayya.

Daga baya da rana ko yamma, ana sa ran ruwan sama mai tsawa da matsakaicin ƙarfi a mafi yawan sassan yankin.

Yanayin jihohin kudu

NiMet ta yi hasashen samun gajimare a kudancin ƙasar, tare da yiwuwar ruwan sama da safe a wasu sassan Legas, Ondo, Ogun, Oyo, Rivers, Bayelsa, Delta, Edo, Cross River, Abia, Imo, Ebonyi da Akwa Ibom.

Kara karanta wannan

Iran ta fuskanci Koriya ta Kudu, ta mata gargadi kan hada kai da Amurka

PM News ta wallafa cewa hukumar ta ce ana sa ran samun matsakaicin ruwan sama a mafi yawan sassan yankin daga baya da rana.

Hasashen ranar Alhamis

A ranar Alhamis, NiMet ta ce za a samu gajimare a wasu sassan arewacin ƙasar, tare da yiwuwar ruwan sama mai tsawa da safe a wasu sassan Jigawa, Kano, Borno, Yobe, Bauchi, Gombe da Kaduna.

Daga baya da rana ko yamma, ana sa ran ruwan sama mai tsawa da matsakaicin ƙarfi a Jigawa, Kano, Kaduna, Yobe, Bauchi, Gombe, Adamawa da Taraba.

A yankin Arewa ta Tsakiya, za a samu sararin samaniya mai ɗan gajimare, yayin da ake sa ran ruwan sama mai tsawa da ɗan ƙaramin ƙarfi a wasu sassan Babban Birnin Tarayya, Nasarawa, Plateau, Neja da Benue.

A kudancin ƙasar, NiMet ta ce za a samu ruwan sama da safe a wasu sassan Ondo, Ogun, Abia, Imo, Enugu, Ebonyi, Legas, Akwa Ibom da Cross River, yayin da ake sa ran ci gaba da ruwan sama a mafi yawan wuraren daga baya.

Wani waje ana ruwan sama
Ruwan sama na zuba a kan wata rumfa. Hoto: Kamal Muhammad
Source: Facebook

Hasashen ranar Juma’a

Kara karanta wannan

Yan firamare sun danne dalibi, sun yi masa kaciya a ban dakin makaranta

A ranar Juma’a, hukumar ta yi hasashen samun gajimare a wasu sassan Arewacin ƙasar, tare da yiwuwar ruwan sama s tsawa da matsakaicin ƙarfi da safe a Taraba da Adamawa.

Daga baya da rana ko yamma, ana sa ran ruwan sama mai tsawa da matsakaicin ƙarfi a Borno, Yobe, Bauchi, Gombe, Kano, Jigawa, Sokoto, Kebbi, Zamfara, Adamawa da Taraba.

A yankin Arewa ta Tsakiya, za a samu hasken rana da ɗan gajimare, tare da yiwuwar ruwan sama mai tsawa da ɗan ƙaramin ƙarfi a wasu sassan Babban Birnin Tarayya, Benue, Kogi, Nasarawa da Neja.

An yi ambaliya a Nepal

A wani labarin, mun ruwaito cewa mummunar ambaliyar ruwa ta mamaye sassan Arewacin Nepal a ranar 26 ga Agusta, 2026, lamarin da ya shafi dubban mutane a cikin 'yan sa'o'i.

Ambaliyar ta mamaye yankunan Rasuwa, Nuwakot, Dhading, Gorkha da Tanahun, inda ta lalata gidaje, hanyoyi da gadoji tare da katse hanyoyin shiga wasu ƙauyuka.

Fiye da mutane 84,270, ciki har da kusan yara 32,000, ne abin ya shafa, yayin da masana suka ce faɗuwar wani babban tarin kankara da duwatsu a tsaunukan Himalaya ce ta haddasa ambaliyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng