Dan Najeriya Ya Rasu bayan Masa Allurar Girman Mazakuta Karo na 5 a Azzakari
- Wani ɗan kasuwa ɗan Najeriya mai tasiri a kafafen sada zumunta, Igho Ubiribo, ya yi aikin ƙara girman mazakuta har sau biyar a wani asibiti da ke Bangkok kafin rasuwarsa
- Hukumomin lafiya na Thailand sun bayyana cewa Ubiribo, mai shekaru 43, ya yi allurar ƙara girman mazakuta sau huɗu tsakanin shekarar 2024 da 2025
- An ce ya rasa ransa ne bayan an yi masa allurar sinadarin ƙara girman mazakuta mai nauyi, yayin da binciken baya ya nuna cewa ya fita a hayyacinsa bayan allurar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Bangkok – Wani ɗan kasuwa ɗan Najeriya da ke Birtaniya kuma mai tasiri a kafafen sada zumunta, Igho Ubiribo, wanda aka fi sani da “Tiny”, “Denisi” da “Ego”, ya rasu bayan an yi masa aikin ƙara girman mazakuta a wani asibiti da ke Bangkok.
Hukumomin lafiya na Thailand sun bayyana cewa Ubiribo ya kasance yana zuwa wannan asibiti tun shekarar 2024, inda ya yi allurar ƙara girman mazakuta sau biyar kafin rasuwarsa.

Source: Facebook
Punch ta rahoto cewa Ubiribo ya rasu ne a watan Maris bayan ya yi amfani da sinadarin ƙara girman mazakuta yayin da yake hutu a Thailand tare da matarsa.
Ana gudanar da bincike
Ma’aikatar Kula da Ayyukan Lafiya ta Thailand ta ce an fara binciken asibitin ne bayan mutuwar Ubiribo, bisa umarnin Ministan Lafiya na ƙasar, Pattana Promphat.
Hukumomin sun ce sun gudanar da binciken asibitin da ke kan titin Rama 1, a yankin Pathum Wan na Bangkok, ranar 7 ga Satumba, 2026, domin duba yadda yake gudanar da ayyukansa da kuma tattara shaidu.
Ubiribo ya yi allura sau 5
A cewar bayanan da asibitin ya bai wa masu binciken, Ubiribo ya kasance abokin huldarsu na yau da kullum tun shekarar 2024.
Hukumomin sun ce allurar farko huɗu an yi su ne tsakanin shekarar 2024 da 2025, yayin da aka yi masa allurar ta biyar a ranar 5 ga Maris, 2026, wato kwana ɗaya kafin rasuwarsa.
Aikin na ƙarshe ya ƙunshi allurar sinadarin filler mai nauyin mililita 40 cikin mazakutarsa.
Hukumomin Thailand sun bayyana cewa likitan da ya kula da Ubiribo ya ba da shawarar a raba allurar zuwa zama biyu. Sai dai an ce Ubiribo ya fi son a yi masa allurar gaba ɗaya a zama guda.
Asibitin ya ce an ba shi umarnin kula da kansa bayan aikin, kuma an ci gaba da bibiyar lafiyarsa. A cewar bayanan asibitin, bai kai rahoton wata matsala da ta taso daga aikin ba.

Source: Instagram
Yadda ya fita a hayyacinsa
A ranar 5 ga Maris, an kira motar asibiti daga wani asibiti mai zaman kansa da ke yankin Sukhumvit domin kai Ubiribo asibiti bayan ya fita a hayyacinsa.
Matarsa ta shaida wa ma’aikatan lafiya cewa mijinta ya yi allurar filler a ranar, sannan suka je yin tausa bayan aikin.
Likitoci sun yi zargin cewa yana iya fama da toshewar jijiyar jini, inda suka shirya yin gwaji na musamman domin duba jijiyoyin jini.
Sai dai kafin a gudanar da gwajin, Ubiribo ya fita a hayyacinsa kuma zuciyarsa ta daina bugawa kwata-kwata.
An kama mai satar yara
A wani labarin, mun ruwaito cewa wata da ake zargi da kasancewa cikin ƙungiyar satar yara da safarar mutane a Jihar Oyo, Adejoke Popoola, ta amsa cewa ta sayar da wasu daga cikin ’ya’yanta.
Popoola ta bayyana hakan ne a ranar Litinin, 7 ga Satumba, 2026, lokacin da aka gabatar da ita tare da waɗanda ake zargi da aikata laifin a hedikwatar ’yan sandan Jihar Oyo da ke Eleyele, Ibadan.
Ta ce ta shiga harkar ne tun watan Oktoba na 2024, inda ta yi zargin cewa ita da abokan aikinta sun sace tare da sayar da yara da dama, ciki har da jariri da tagwaye.
Asali: Legit.ng


