Matasa 20 da Suka Fito Neman a Saki Malamin Musulunci Sun Shiga Babbar Matsala

Matasa 20 da Suka Fito Neman a Saki Malamin Musulunci Sun Shiga Babbar Matsala

  • Rundunar yan sandan jihar Sokoto ta kama kimanin mutane 20 kan zanga-zangar neman a saki Malamin Musulunci, Dahiru Mai Barewa
  • An ce zanga-zangar ta rikide zuwa tashin hankali bayan wasu matasa sun yi yunkurin kwace Mai Barewa daga hannun jami'an tsaro
  • Yan sanda sun ce an gurfanar da wadanda aka kama a gaban kotu domin doka ta yi aiki a kansu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Sokoto - Rundunar yan sandan jihar Sokoto ta kama kimanin mutane 20 dangane da zanga-zangar da aka gudanar ranar Litinin domin neman a saki Malam Dahiru Mai Barewa.

An kama masu zanga-zangar ne bayan rahotanni sun nuna cewa zanga-zangar neman sakin Mai Barewa ta rikide zuwa tashin hankali.

Yan sanda.
Dakarun rundunar yan sandan Najeriya yayin da suke bakin aiki Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

Punch ta ruwaito cewa ana zargin wasu matasa da kai wa jami'an tsaro hari tare da kokarin kwace Mai Barewa daga hannunsu.

Kara karanta wannan

Abin al'ajabi: Mutum mutumi sun yi zanga zanga, suna neman kare ayyukan mutane

Matasa sun tare hanyoyi a Sokoto

Tun da farko, tashin hankali ya barke na wani dan lokaci a wasu sassan birnin Sokoto, inda aka ce matasan da ke zanga-zangar adawa da ci gaba da tsare Mai Barewa suka yi artabu da jami'an tsaro.

Rahotanni sun ce masu zanga-zangar sun tare wasu hanyoyi tare da gudanar da zanga-zanga a sassan birnin kafin jami'an tsaro su shiga tsakani domin dawo da zaman lafiya.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Sokoto, DSP Ahmed Rufai, ya tabbatar da kama mutanen yayin ganawa da wakilin jaridar ranar Talata.

Ya ce an kama kimanin mutane 20 a yayin rikicin kuma an gurfanar da su a gaban kotu, kamar yadda Daily Post ta kawo.

Rufai ya ce:

"An kama kimanin mutane 20 dangane da zanga-zangar, kuma an gurfanar da su a gaban kotu."

Me ya jawo zanga-zangar matasan?

Zanga-zangar ta haddasa tashin hankali a wasu sassan birnin Sokoto bayan matasa sun tare wasu hanyoyi tare da taruwa domin neman a saki Mai Barewa.

Kara karanta wannan

Zanga zanga ta barke a Sokoto kan tsare malamin addinin musulunci

A cewar majiyoyin yan sanda, jami'an tsaro sun shiga tsakani ne bayan masu zanga-zangar sun fara tayar da hankali tare da kokarin fitar da Mai Barewa daga inda ake tsare da shi.

Matakin rundunar yan sanda ya biyo bayan umarnin kotu na sake kama Mai Barewa tare da tsare shi.

Ana zarginsa da yin barazanar kashe wasu malaman addinin Musulunci biyu, Sheikh Musa Ayyuba Lukuwa da Malam Murtala Bello Assada.

Sokoto map.
Taswirar jihar Sakkwato da ke Arewacin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Yan sanda sun gargadi mazauna Sokoto

Shigar jami'an tsaro cikin lamarin ya zo ne a yayin da ake fargabar zanga-zangar za ta iya kara kamari tare da kawo cikas ga zaman lafiya a babban birnin jihar.

DSP Ahmed Rufai ya ce an bi hanyoyin doka wajen tafiyar da shari'ar wadanda aka kama.

Ya jaddada matsayin rundunar cewa ya kamata jama'a su bi hanyoyin doka wajen gabatar da korafe-korafensu maimakon fada ko rikici.

Mai magana da yawun yan sandan ya kuma bukaci mazauna jihar Sokoto su kwantar da hankalinsu tare da bin doka.

Gwamnatin Sokoto ta tashi tsaye

Kun ji cewa gwamnatin Sokoto ta ce ta ayyana yaƙi da ’yan ta’adda da sauran masu aikata laifuka bayan wani mummunan hari da ya kashe mutane a Kebbe.

Gwamnatin jihar ta kuma bayar da tallafin kuɗi na N9m ga iyalan waɗanda suka mutu da kuma waɗanda suka tsira da raunuka domin rage musu tasirin wannan mummunan lamari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262