Zamu Goyi Bayan Gwamnatin Tarayya Kan Yaki Da Matsalar Tsaro, Gwamnonin PDP

Zamu Goyi Bayan Gwamnatin Tarayya Kan Yaki Da Matsalar Tsaro, Gwamnonin PDP

- Gwamnonin PDP sun bayyana zasu cigaba da ba gwamnatin shugaba Buhari goyon baya a kan yaƙi da matsalar tsaro

- Shugaban ƙungiyar gwamnonin, Aminu Tambuwal ne ya faɗi haka jim kaɗan bayan fitowarsu daga taro a Abuja

- Gwamnonin sun ce ko kaɗan baza su saka siyasa a matsalar tsaron da ake fama dashi a ƙasar nan

Gwamnonin da aka zaɓa a ƙarƙashin inuwar jamiyyar PDP sun miƙa goyon bayansu ga gwamnatin tarayya domin kawo ƙarshen matsalar tsaron da ake fama da ita a kasar nan.

Gwamnan jihar Sokoto kuma shugaban gwamnonin jamiyyar PDP, Aminu Tambuwal ne ya faɗi hakan a ƙarshen taron da gwamnonin suka gudanar a gidan gwamnan Sokoto, Asokoro, Abuja.

KARANTA ANAN: Da duminsa: Ragowar daliban makarantar da 'yan bindiga suka kai farmaki sun koma barikin sojoji

Taron wanda ya samu halartar kusan dukkanin gwamnonin PDP, ya zo ne bayan wani taro da shugabannin amintattu na jamiyyar suka gudanar a sakateriyar jamiyyar a Abuja.

Da yake magana da yan jarida bayan taron wanda ya kwashe fiye da awanni biyar, Tambuwal yace:

"Gwamnonin PDP ba zasu siyasantar da matsalar tsaro ba, dalilin hakan yasa su ka haɗa hannu da gwamnatin tarayya domin kawo ƙarshen matsalar.

Taro ne mai matukar amfani, mun duba halin da kasa ke ciki, matsalar tsaron da ke cikin kasa."

"A matsayin mu na gwamnonin PDP, mun yadda tare da amincewa mu cigaba da aiki da gwamnatin tarayya da niyyar samar da sabon aminci a wuraren da ke fama da rikice rikice a Kasa," inji Tambuwal

"Dole ne mu ƙi siyasantar da lamarin tsaro, dole ne muyi aiki tare domin tabbatar da dawowar zaman lafiya a kasar mu. Hakan yasa muka amince da cigaba da aiki da gwamnatin tarayya ta wannan fannin," Inji shi.

Zamu Goyi Bayan Gwamnatin Tarayya Kan Yaki Da Matsalar Tsaro, Gwamnonin PDP
Zamu Goyi Bayan Gwamnatin Tarayya Kan Yaki Da Matsalar Tsaro, Gwamnonin PDP Hoto: @AWTambuwal
Asali: Twitter

KARANTA ANAN: Jami'an 'yan sanda biyu sun mutu a wani mummunan hatsari da ya ritsa dasu

Tambuwal ya ɗanyi tsokaci ga yan jarida kan abubuwan da gwamnonin na PDP suka tattauna, inda yake cewa:

"A dangane da maganar tattalin arzikin kasa, muna rokon shugaban kasa da ya sake duba wasu matakai, sannan kuma muna rokon sa da ya kawo abubuwan rage radadi ga mutanen Najeriya sannan kuma ya tallafi gwamnatocin jihohi wajen sauke nauyin da ke kawunansu ta hanyar samar masu da abubuwan da suke buƙata."

"Hakan zai ba mu damar sauke nauyin da ke kanmu da kuma tabbatar da mun samar da mulki mai inganci da kuma samar da yanayi mai kyau na rayuwa a jihohin kasar nan," a cewarsa.

A dangane da kokarin sulhunta mambobin jamiyyar, gwamnan yace kwamitin da Saraki yake jagoranta ya mika rahotonsa ga ƙungiyar, ya kuma karfafa ma mambobin kwamitin guiwa domin cigaba da ƙoƙarin gina jamiyyar.

Yayi watsi da maganar ficewar wani gwamnan PDP zuwa wata jamiyya. Kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito

"Kusan duka gwamnonin PDP sun halarci wannan taro, wannan tabbaci ne cewa ba wani gwamna da yake tunanin barin jamiyyar zuwa wata jamiyya."

Gwamnan ya kara da cewa kwamitin gudarnawa ya nada kwamiti kan wakilci wanda gwamnan jihar Bauchi Bala Mohammed zai jagoranta.

Da kuma kwamitin abubuwan sharia wanda gwamnan Ribas Nyesom Wike zai jagoranta da kwamitin kudi wanda gwamnan jihar Abia, Okezie Ikpeazu zai jagoranta.

Ya bayyana cewa kwamitocin guda uku an sanya su suyi aiki wajen kawo cigaban jamiyyar.

Taron wanda ya samu halartar gwamnonin PDP da dama wadanda suka hada da; Nyesom Wike (Rivers), Ifeanyi Okowa (Delta), Aminu Tambuwal (Sokoto), Okezie Ikpeazu (Abia) da Bello Matawalle na jihar Zamfara.

Sauran sun hada da Godwin Obaseki, Adamu Fintiri, Bala Mohammed, Ben Ayade, Samuel Ortom and Ifeanyi Ugwuanyi, gwamnonin jihohin Edo, Adamawa, Bauchi, Cross River, Benue da Enugu.

A wani labarin kuma Gwamna Zulum ya dauki nauyin karatun 'ya'yan talakawa, 'yan mata 800

Gwamna ya tabbatar da biyan makudan kudade na makaranta da kuma kayayyakin karatu

Gwamnan ya shaida cewa, za a ci gaba da biyan kudin makarantar har zuwa kammalawarsu

Ahmad Yusuf dan mutan katsinawa ma'aikacin legit.ng ne a bangaren Hausa. Ya fara aiki da legit kwa nan nan. Ahmad nada burin shahara a aikin jarida.

Kuna iya samunsa a kafar sada zumunta na twitter @ahmadyusufMuha77

Asali: Legit.ng

Online view pixel