"Ba Sai Kun Jira Umarni ba," An ba Jami'an Tsaro Damar Kashe Ƴan Ta'adda nan Take
- Ministan tsarom, Janar Christopher Musa ya ba jami'an tsaro izini su harbe 'yan bindiga da 'yan ta'adda nan take ba tare da jiran wani umarni ba
- Janar Christopher Musa ya ce duk jami'in da ya ki daukar mataki zai fuskanci hukunci kamar mai hada baki da 'yan ta'addar da ke kashe kashe
- Gwamnatin Sokoto ta kaddamar da motocin sulke da kayan tsaro na sama da Naira biliyan 27 domin yaki da rashin tsaron da suke fama da shi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Sokoto - Ministan tsaro, Janar Christopher Musa mai ritaya, ya umarci jami'an tsaro da kada su yi kasa a gwiwa wajen hallaka 'yan bindiga da 'yan ta'adda,
Janar Musa ya yi gargadi mai kaushi cewa duk jami'in da ya ki daukar mataki da sunan jiran umarni za a dauke shi tamkar mai hada baki da miyagun.

Kara karanta wannan
Kotu ta umarci a tsare malamin jami'ar ABU saboda kalaman da ya yi kan gwamnatin Katsina

Source: Facebook
An ba jami'an tsaro umarni kan 'yan ta'adda
Janar Musa ya bayyana hakan ne ranar Laraba a jihar Sokoto yayin kaddamar da motocin aiki 62 da sauran kayan tsaro da gwamnatin jihar ta saya kan kudin da ya kai N27.127bn, in ji rahoton The Punch.
Ya ce da zarar an tura jami'ai aiki, bai kamata su jira wani umarni ba kafin su dauki mataki kan duk wani dan bindiga ko dan ta'adda.
A cewarsa, duk jami'in da ya ki harbe ko kashe 'yan ta'adda saboda yana jiran umarni, gwamnati za ta dauke shi a matsayin mai goyon bayan masu aikata laifuka.
An yabawa gwamnatin Sokoto
Ministan ya yabawa Gwamna Ahmed Aliyu bisa ci gaba da tallafa wa hukumomin tsaro da motocin aiki da sauran kayan aiki.
Ya ce wannan mataki alama ce ta shugabanci nagari da kuma kudurin gwamnati na inganta tsarin tsaro a jihar Sokoto da Najeriya baki daya.
Musa, wanda ya bayyana kansa a matsayin dan asalin jihar Sokoto, ya ce jihar na daga cikin wuraren da suka fi samun zaman lafiya sakamakon hadin kan gwamnati, jami'an tsaro da al'umma.
Ya kara da cewa sababbin motocin sulke da kayan aikin tsaron za su taimaka wajen saukaka zirga-zirgar jami'an tsaro, tattara bayanan sirri da kare rayukan jami'ai yayin yaki da 'yan bindiga, 'yan ta'adda da masu garkuwa da mutane.
Gwamna ya yi magana kan tsaro
Wakilin Legit Hausa da ya halarci taron, ya ruwaito cewa Gwamna Ahmed Aliyu ya ce sayen sababbin motocin sulke, Buffalo APCs, babura 320, kayan tsaro 3,200, hular kariya da rigunan kariya 2,000, na'urorin hangen dare 200 da sauran kayan aiki na daga cikin kokarin gwamnatinsa na karfafa tsaro tun bayan hawansa mulki.

Source: Facebook
A cewar gwamnan:
"In ba tsaro ba a zuwa gona, ba a zuwa makaranta, ba a zuwa neman abinci, shi ya sa muka sanya magance tsaro ya zama abu na sahun farko a ayyukan gwamnati.
"Jihar Sokoto tana da tata barazana ta tsaro wadda ta shafi masu garkuwa da mutane da satar dabbobi da sauran ayyukan ta'addanci.
"Lokacin da muka fara jagoranci, mun yi hobbasa sosai kan tsaro, mun fara sayo motoci fiye da 200, babura fiye da 250, mu ga cewa mun rabawa jami'an tsaro musamman wuraren da ke da matsalar tsaro.
"Jihar Sokoto na daga jahohin da suka kaddamar da rundunar tsaron jiha, domin taimakawa ayyukan jami'an tsaro. Mun bada fifiko ga rundunar, domin su ne tare da al'umma, su ke iya gano in wata bakuwar fuska ta zo, don haka ana samun sababbin bayanan tsaro."
Sojoji sun hallaka 'yan ta'adda
A wani labari, mun ruwaito cewa, sojoji sun kashe 'yan ta'adda da masu tayar da ƙayar baya 1,597 tare da ceto mutane 1,516 da aka sace daga Janairu zuwa Yuni.
Sojojin sun gudanar da ayyukan tsaro 14,221 a sassa daban-daban na ƙasar, inda suka ƙwato makamai, alburusai da bama-bamai masu yawa.
Hedikwatar tsaro ta ce hare-haren sun rage ƙarfin Boko Haram, ISWAP da 'yan bindiga, yayin da mambobi 132 na ƙungiyoyin suka miƙa wuya.
Asali: Legit.ng

