Wani Sanata ya makale a hanyar Abuja saboda ambaliyar ruwan sama

Wani Sanata ya makale a hanyar Abuja saboda ambaliyar ruwan sama

  • Wata mabaliyar ruwa ta yi awon gaba da wasu motoci guda uku a hanyar babban birnin tarayya Abuja
  • Wani sanatan jihar Kogi, rahotanni sun bayyana cewa, shi ma ya makale a yayin wannan ambaliyar
  • Matafiya da dama sun makale yayin da ruwan sama ya dauki kusan awanni hudu yana sauka a yankin

Abuja - Wasu sassan babbar hanyar Abuja zuwa Lokoja zuwa Okene sun kasance cikin ambaliya a ranar Asabar 7 ga watan Agusta wacce ta mamaye su bayan ruwan sama na awa hudu. Daya daga cikin yankunan da abin ya shafa shi ne tsakanin Kwali da Abaji.

Ambaliyar ta sa matafiya sun makale yayin da motoci daga Abuja ba za su iya wucewa zuwa Lokoja, Okene da sassan kudanci ba. Kimanin motocin bas guda uku ne rahotanni suka ce ambaliyar ta kwashe su.

Daga cikin daruruwan matafiya da suka makale har da Sanata daga gundumar Kogi ta yamma, Sanata Smart Adeyemi, inji rahoton The Nation.

Kara karanta wannan

Tsohon sanatan Najeriya ya mayar da martani bayan hotonsa ya sake bayyana tare da dan damfara, Hushpuppi

Sanata ya makale a cikowa a hanyar Abuja saboda ambaliyar ruwan sama
Ambaliyar ruwan sama | Hoto: dailytust.com
Asali: UGC

Adeyemi ya ce:

“Ambaliyar ta yi barna sosai. Na shaida yadda ta yi awon gaba da wasu motoci daga babbar hanya.
”Ni da matafiya da yawa ba za mu iya ci gaba da tafiya ba. Mun makale. Babu wata mafita da ta wuce komawa Abuja.”

Wata da cikin matafiya, Hadiza Abdulkareem ta yi kira ga hukumomin da abin ya shafa da su yi gargadi da fadakar da matafiya a wannan damina.

Ganduje Ya Gwangwaje Dukan Iyalan da Ambaliyar Ruwa Ta Shafa da Tallafin Makudan Kudi

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano, ya bada tallafin kudi dubu N200,000 ga kowanne ɗaya daga cikin iyalan mutum 18 da ambaliyar ruwa ta kashe a Doguwa, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Gwamnan ya kai ziyara ta musamman domin ta'aziyya ga iyalan mamatan ranar Lahadi.

Ya kuma yi addu'ar samun rahama ga waɗanda suka rasu sanadiyyar ruwan sama mai tsanani, wanda ya haifar da ambaliya.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari ta bayyana dalilin da yasa ba za ta tattauna da 'yan bindiga ba

Yadda masu tattara shara suka dawowa da tsohuwa N10,287,000 da ta zuba a shara

A wani labarin daban, Wasu dangi a kasar Amurka, Ohio, an ce sun zubar da tsabar kudi $25,000 (N10,287,000) cikin kuskure lokacin da suke taimaka wa kakarsu a aikin tsaftace gida. Wannan ya faru ne a gundumar Lorain in ji rahoto.

An ce dangin sun ci sa’a, wani kamfanin tattara shara ya yi nasarar lalubo shara sannan ya kwaso kudin bayan zubar da kunshin kudin.

A cewar ABC News 5, tuni aka mika kudin ga tsohuwa mai kudin. A cewar Ohio Insider, mai kula da ayyukan tattara sharan, Gary Capan ya ce tawagarsa ta taimaka wa dangin da ba a ambaci sunansu ba wajen gano kudin tsohuwar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Tags:
Online view pixel