Mutane da Yawa Sun Maƙale Yayin da Ambaliya Ta Shanye Rukunin Gidaje a Abuja

Mutane da Yawa Sun Maƙale Yayin da Ambaliya Ta Shanye Rukunin Gidaje a Abuja

  • Gidaje da dama da motoci a rukunin gidajen Trade More sun nutse a ruwa sakamakon ambaliyar ruwa ranar Jumu'a
  • Rahoto ya nuna mazauna yankin da ba'a san adadinsu ba har yanzu sun maƙale amma jami'an bada agaji sun duƙufa domin lalubo su
  • An ce mamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya ne ya haddasa ambaliyar kuma tuni NEMA ta bai wa mazauna wurin shawara

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT Abuja - Mutane da yawa da har kawo yanzun ba'a gama tantance adadinsu ba da ke zaune a rukunin gidajen Trade Moore estate, Lugbe a Abuja sun maƙale sakamakon ambaliyar da ta auku ranar Jumu'a.

The Cable ta tattaro cewa ambaliyar wacce ta samo asali daga mamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya ta shanye wasu gidaje da motoci da dama a yankin.

Kara karanta wannan

Hukumar DSS Ta Tona Shirin ‘Yan Ta’adda a Lokacin Bukukuwan Sallah a Najeriya

Yadda ruwa ya lakume gidaje a Abuja.
Mutane da Yawa Sun Maƙale Yayin da Ambaliya Ta Shanye Rukunin Gidaje a Abuja Hoto: thcableng
Asali: UGC

Jami'ai sun duƙufa domin ceto waɗanda suka maƙale

Har kawo yanzu da muke haɗa muku wannan rahoton, jami'an hukumar bada agajin gaggawa da sauransu suna ci gaba da aikin tsamo waɗanda suka makale a ruwan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A wani rahoton dakin agaji, hukumar kai ɗaukin gaggawa (NEMA) ta ce diraban wata Mota Peugeot 406 mai lambar rijista YLA 681 FS ya nutse a cikin ruwan ambaliyar kuma har yanzu ba'a ganshi ba.

A ruwayar Daily Trust, Rahoton ya ce:

"An samu nasarar ceto mutum huɗu cikin yanayi mai kyau. A halin yanzu jami'an hukumar NEMA, hukumar kwana-kwana, hukumar FCT FEMA da sauran hukumimin agaji sun kai ɗauki wurin."

NEMA ta roki mazauna yanki mau haɗari su tashi

Da yake zantawa da yan jarida ranar Jumu'a, wani jami'in NEMA ya yi kira ga mazauna yankin da ke fuskantar barazanar ambaliya a rukunin gidajen su tattara kayansu su koma wani wurin.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Kai Sabon Mummunan Hari a Arewa, Sun Banka Wa Mutane Sama da 10 Wuta Har Lahira

"Idan ka san gidanka na kan layin da ke fuskantar barazanar Ambaliya, tun da wuri ka tashi ka koma wani wuri mai tsaro, ko ba komai ka ceci rayuwarka. Kadara ba komai bace a kan rai."
"Kuna ganin yadda ruwa ya shanye waɗan can motocin, ba'a raina karfin ruwa, zai iya awon gaba da mutane. Muna haɗa ku da Allah, bamu fatan rasa rayuka a wannan shekarar," inji shi.

Manjo Janar Lagbaja Ya Kama Aiki a Matsayin Shugaban Sojin Ƙasa Na 23

A wani rahoton na daban kuma sabon shugaban hukumar sojin Najeriya ya fara aiki bayan naɗin da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya masa.

A wani ɗan biki da aka shirya a hedkwatar soji da ke Abuja, Manjo Janar Lagbaja ya karbi ragama a matsayin shugaban rundunar sojin kasa na 23 a tarihu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel