Zaben Osun: An Cafke Dan Majalisa da Mutane Sama da 100 a Gidansa
- Rundunar ‘yan sanda ta ce jami’an FBI-IRT sun kama dan majalisar dokokin Jihar Osun mai wakiltar Irewole/Isokan, Abiola Ibrahim, a Ikire
- An kama dan majalisar ne tare da wasu mutane kusan 146 da ake zargi da kasancewa ‘yan amshin shata a ranar zaben gwamnan jihar
- Dan majalisar ya musanta daukar mutanen, yana mai cewa mutanen da aka samu a gidansa masu kada kuri’a ne da suka zo domin kada kuri’a a zaben
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Ikire, Osun – Jami’an Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya daga sashen FBI-IRT sun kama dan majalisar dokokin Jihar Osun mai wakiltar Irewole/Isokan, Abiola Ibrahim.
An kama dan majalisar ne a Ikire tare da wasu mutane kusan 146 da ake zargi da kasancewa ‘yan amshin shata a yayin zaben gwamnan jihar.

Source: Facebook
Vanguard ta wallafa cewa ‘yan sanda sun tabbatar da kama dan majalisar, yayin da lamarin ya faru a safiyar Asabar.
‘Yan sandan Psun sun yi bayani
Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Osun, DSP Abiodun Ojelabi, ya tabbatar da kamen yayin wata tattaunawa ta wayar tarho da jaridar Punch.
Rahoto ya nuna cewa Ojelabi ya ce an kama Ibrahim ne bisa zargin boye wasu mutanen da ake zargi da kasancewa ‘yan amshin shata.
Ya ce:
“An kama shi a Ikire saboda boye wasu ‘yan amshin shata da ake zargi. An kama shi tare da mutane kusan 146.
“FBI-IRT ne suka kama shi. Yana hannunsu. An kama shi ne da sanyin safiyar Asabar.”
An gano mutane sama da 100
Wani faifan bidiyo da ya bazu a kafafen sada zumunta ya nuna jami’an ‘yan sanda suna tambayar dan majalisar game da mutanen da aka tarar a wani gida mai zaman kansa.
A cikin bidiyon, jami’an tsaron sun yi tambayoyi ga Ibrahim kan dalilin kasancewar dimbin mutanen a gidan a ranar da ake gudanar da zaben.
Lokacin da jami’an suka tambaye shi, dan majalisar ya dage cewa mutanen da aka tarar masu kada kuri’a ne da suka zo domin shiga zaben.
Dan majalisar ya kare kansa
Yayin da yake kare kan shi bayan jami'an 'yan sanda suna masa tambayoyi, dan majalisar ya bayyana cewa:
“Su masu kada kuri’a ne a zaben da ake gudanarwa a yau.”
Ya kara da cewa wasu daga cikinsu ‘yan asalin yankin ne, yayin da wasu suka fito daga wasu wurare.
“Ban dauke su aiki ba. Ban yi musu alkawarin komai ba. Zabar wanda suke so hakkinsu ne. Ni ba wakilinsu ba ne,”
In ji shi.

Source: Facebook
Dan majalisar ya kuma bayyana kansa a matsayin dan jam’iyyar Accord yayin da jami'an tsaron suka kama shi.
Adeleke ya ce zai lashe zabe
A wani labarin, mun rahoto cewa gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke, ya bayyana kwarin gwiwar cewa zai yi nasara a zaben gwamnan jihar da ake gudanarwa a yau Asabar.
Gwamnan ya bayyana hakan ne bayan ya kada kuri’arsa a mazabar shi ta Sagba Agbogunde, da ke karamar hukumar Ede ta Arewa.
Adeleke ya isa rumfar zaben da misalin karfe 8:32 na safe tare da dimbin magoya bayansa, inda aka kammala tantance shi da misalin karfe 8:35 kafin ya kada kuri’arsa.
Asali: Legit.ng

