Gwamnan Najeriya da ke Samun Ribar Naira Miliyan 10 a Sayar da Kosai

Gwamnan Najeriya da ke Samun Ribar Naira Miliyan 10 a Sayar da Kosai

  • Gwamnan Akwa Ibom, Umo Eno, ya bayyana cewa ya taba samun kudin shiga Naira miliyan 10 a duk wata daga sana'ar sayar da kosai da burodi
  • Gwamnan ya ce ya fara sana'ar ne tun lokacin da yake dan kasuwa, inda ya rika sayar da kosai da burodi ga ma'aikatan kamfanin ExxonMobil
  • Wani mai sharhi a intanet, Emmanuel Udombon, ya kalubalanci ikirarin, yana mai cewa adadin kudin da gwamnan ya ambata ya yi matukar yawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Uyo – Gwamnan Akwa Ibom, Fasto Umo Eno, ya bayyana cewa ya taba samun kudin shiga da ya kai Naira miliyan 10 a duk wata daga sana'ar sayar da kosai da burodi.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a wajen taron koli na wata-wata na jihar da aka gudanar a ranar Talata, yayin da wani gajeren bidiyo na jawabin nasa ke yawo a kafafen sada zumunta.

Kara karanta wannan

Bashin biliyoyi ya taru a kan Kiyosaki da ke koya wa mutane dabarun yin kudi

Gwamna Umo Eno
Wajen da ake toya kosai a hagu da Gwamna Umo Eno a dama. Hoto: Getty Images|Akwa Ibom State Government
Source: Facebook

Shafin News Central ya wallafa bidiyon da gwamna Eno ya yi bayanin yadda ya ke tara makudan kudi waje sayar da kosai a X.

Gwamna ya sayar da kosai

Eno ya ce ya fara sana'ar ne a wani shago da har yanzu yake nan, inda ya rika sayar da kosai da burodi a shekarun baya.

Ya ce suna bude burodi su saka akara a ciki, sannan ma'aikatan kamfanin ExxonMobil da ke zuwa wurin aiki da safe sukan saye.

Ya ce daga baya suka fara hada sana'ar sayar da kofi da sauran abubuwa a wurin.

"Har yanzu muna da wannan shagon a can. Na fara sayar da kosai da burodi, muna bude burodi mu saka kosai.
"Mutanen da ke zuwa aiki a ExxonMobil suna saye da safe, su sha kofi. Daga baya muka fara shagon sayar da kofi.
"A duk wata, wannan sana'ar akara da burodi tana ba ni kudin da bai gaza Naira miliyan 10 ba,"

Kara karanta wannan

Da gaske Opay zai daina aiki kuma yan Najeriya za su rasa kuɗaɗensu? Gaskiya ta fito

In ji Eno

Ikirarin ya jawo ce-ce-ku-ce

Bayyanar wannan ikirari na gwamnan na zuwa ne kimanin watanni uku bayan matar shugaban kasa, Oluremi Tinubu, ta bukaci matasa da talakawa su fara kananan sana'o'i kamar sayar da kosai.

The Sun ta wallafa cewa, mai sharhi kan lamuran yau da kullum, Emmanuel Udombon, ya kalubalanci ikirarin Eno, yana mai cewa ya kamata a duba adadin kudin da ya ambata sosai.

Udombon ya ce ba abin kunya ba ne mutum ya taba sayar da kosai, amma abin tambaya shi ne yadda sana'ar da ake gudanarwa daga wuri guda za ta rika samar da Naira miliyan 10 a wata.

Udombon ya ce ba Eno kadai ne ke samarwa da rarraba akara da burodi a Akwa Ibom ba, don haka adadin da ya ambata yana bukatar karin bayani.

Gwamna Umo Eno na bayani a taro
Gwamnan Akwa Ibom, Umo Eno. Hoto: Akwa Ibom State Government
Source: Twitter

Udombon ya ce idan Naira miliyan 10 din da Eno ya ambata riba ce bayan an cire dukkan kudin gudanar da sana'ar, hakan na nufin zai bukaci samun kusan N333,333 a matsayin riba a kowace rana.

Kara karanta wannan

Yadda batun maido tallafin mai ya zafafa adawa tsakanin Tinubu da Atiku

Ya ce idan aka dauka cewa kowace rana sana'ar na samar da N100 na riba, to sai an sayar da kusan kosai guda 3,334 a kowace rana domin a kai wannan adadi.

Ga bidiyon da ya yi bayanin a kasa:

Ana bin Kiyosaki bashi

A wani labarin, mun ruwaito cewa marubucin littafin Rich Dad Poor Dad, Robert Kiyosaki, ya bayyana cewa ana bin shi bashin dala biliyan 1.2.

Kiyosaki mai shekaru 79 ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa a shirin Get Rich Education, inda ya ce karbar bashi domin sayen kadarori.

Sai dai tsohuwar matarsa kuma abokiyar kasuwancinsa, Kim Kiyosaki, ta bayyana cewa bashin yana da alaka da wani kundin kadarorin gidaje.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng