Daga Dawowa daga Motsa Jiki, Sufatan Ɗan Sanda Ya Yi Mutuwan Fuju'a
- Wani sufetan ɗan sanda a Najeriya ya rasa rayuwarsa bayan ya fadi jim kadan bayan kammala atisayen motsa jiki na mako-mako a Sokoto
- An garzaya da Adamu Isah asibiti bayan ya fadi, amma likitoci sun tabbatar da rasuwarsa jim kadan bayan isa asibitin
- Kwamishinan ’yan sanda Hayatu Hassan Shaffa ya bayyana marigayin a matsayin jami’i mai kishin aiki, wanda ya kuma kasance dan wasan dambe
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Sokoto - An tabbatar da rasuwar wani sufetan ’yan sanda ta rundunar da ke jihar Sokoto a Arewa maso Yammacin Najeriya.
An ce marigayin Adamu Isah ya rasu bayan rahotanni sun bayyana cewa ya fadi jim kadan bayan kammala atisayen motsa jiki.

Source: Original
Sokoto: Yadda babban dan sanda ya rasu
A cewar wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar, DSP Ahmad Rufa’i, ya fitar a Facebook, Isah ya fadi jim kadan bayan ya dawo daga atisayen Walkathon na mako-mako.
An gudanar da atisayen ne a hedikwatar rundunar ranar Laraba, inda jami’in ya fara samun matsala bayan dawowarsa daga atisayen.
Nan take aka garzaya da shi zuwa wani asibiti domin samun kulawar likitoci, amma daga baya likitocin da ke kula da shi suka tabbatar da rasuwarsa.
Kwamishinan ’yan sanda na Sokoto, CP Hayatu Hassan Shaffa, ya bayyana matukar bakin cikinsa kan rasuwar jami’in kwatsam.
Shaffa ya bayyana Isah a matsayin jami’in ’yan sanda mai kishin aiki da jarumtaka, wanda ya yi wa kasa hidima cikin sadaukarwa da kwarewa.

Source: Facebook
Martanin kwamishinan yan sandan Sokoto
Kwamishinan ya ce marigayin ya kasance dan wasa mai himma, kuma mamba ne na kungiyar wasan volleyball ta rundunar, sannan yana kuma yin damben boksin.
“Rundunar ’yan sandan Sokoto tana matukar bakin cikin wannan babban rashi mai radadi da ya samu abokin aikinmu, Sufeto Adamu Isah."
in ji kwamishinan.
Ya mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalan marigayin, abokansa da sauran abokan aikinsa, tare da tabbatar wa iyalan cewa rundunar za ta ba su dukkan goyon bayan da ya dace.
Kwamishinan ya kuma bukaci jami’ai da sauran ma’aikatan rundunar su ci gaba da jajircewa, tare da samun kwarin gwiwa daga rayuwar Isah da hidimar da ya yi wa kasa.
Ya yi addu’ar Allah ya jikansa, ya ba shi hutu na har abada, sannan ya bai wa iyalansa da sauran wadanda rasuwar ta shafa karfin jure wannan babban rashi yayin da mutane ke bayyana kyawawan halayen marigayin.
An buge babban dan sanda a bakin masallaci
Mun ba ku labarin cewa wani direba da ya saba dokar hanya ya buge wani sufetan dan sanda a kusa da Masallacin Kasa da ke Abuja.
Direban mai suna David Auta, yana tuka mota kirar 'Toyota Hummer' daga Cibiyar Kiristoci ta Kasa zuwa Wuse Zone 4, inda ya saci hanya.
Hakan ya haddasa wa sufeta James Haruna raunuka da karyewar kafar hagu, kuma an garzaya da shi zuwa Asibitin kasa da ke Abuja.
Asali: Legit.ng

