Tashin Hankali da Mutane kusan 50 Suka Mutu a Wajen Satar Mai a Najeriya
- An ruwaito cewa mutane da dama sun mutu bayan sun shaki hayaƙi mai guba yayin da ake zargin suna ɗibar man fetur ba bisa ƙa’ida ba
- Majiyoyin sun ce adadin mamatan ya kai 43, amma ’yan sandan Rivers ba su tabbatar da adadin ba, suna cewa ana ci gaba da bincike
- YEAC-Nigeria ta ce aƙalla mutane 37 sun mutu bayan sun shaki wani abu yayin wani yunƙurin ɗibar man fetur
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Okrika, Rivers - Fargaba ta mamaye ƙaramar hukumar Okrika ta jihar Rivers bayan wani lamari da aka ruwaito cewa ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama.
Ana zargin mutanen da lamarin ya rutsa da su sun je ɗibar man fetur ba bisa ƙa’ida ba, kafin su shaki hayaƙi mai guba da ya fito daga kayayyakin man.

Kara karanta wannan
Daliban ABU Zaria sun kera na'urar da makafi za su rika tafiya da ita cikin salama

Source: Original
Lamarin ya faru ne da misalin tsakar dare ranar Alhamis, 3 ga Satumba, 2026, a Okari Jetty da ke yankin Okrika Mainland, cewar rahoton jaridar Vanguard.
Fiye da mutane 200 suka je wurin
An gano cewa wani jirgin ruwa ya tsaya a wani wuri da ke bakin kogi domin ɗaukar kayayyakin man fetur zuwa ƙasashen waje.
Rahotanni sun ce fiye da mutane 200, galibinsu matasa daga kauyukan da ke makwabtaka da yankin, sun isa wurin da ƙananan kwale-kwale da aka ƙera a gida.
Ana zargin mutanen sun je wurin ne domin ɗibar man fetur daga wani wurin da aka yi wa bututun mai kutse ba bisa ƙa’ida ba.
Wata majiyar al’umma ta ce yayin da ake gudanar da aikin, hayaƙin man mai tsananin wari ya cika yankin.Hakan ya sa wasu daga cikin mutanen da ke wurin suka fara faɗuwa sumammu.
Wasu sun faɗa cikin kogin
A cewar majiyar, wasu daga cikin waɗanda abin ya shafa sun faɗa cikin kogin yayin da suke ƙoƙarin tsira, jaridar TheCable ta kawo rahoton.
Wasu da suka samu damar tserewa kuma sun fuskanci matsananciyar matsalar numfashi, inda aka garzaya da su asibitoci domin samun magani.
Majiyar ta ce an gano gawarwakin mutane 37 da aka tabbatar ’yan asalin Okrika ne. An kuma gano wasu gawarwaki shida waɗanda har yanzu ba a iya tantance ko su waye ba.
Bugu da ƙari, an ruwaito cewa mutane da dama sun ɓace tun bayan faruwar lamarin.
’Yan sanda ba su tabbatar da adadin mamatan ba
Duk da cewa majiyoyin al’umma sun ce mutane 43 ne suka mutu, rundunar ’yan sandan jihar Rivers ta ce ba za ta iya tabbatar da ainihin adadin waɗanda suka rasa rayukansu ba.
Rundunar ta jaddada cewa ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano cikakken bayani kan abin da ya faru da kuma adadin waɗanda abin ya shafa.
YEAC-Nigeria ta tabbatar da faruwar lamarin
Cibiyar Youths and Environmental Advocacy Centre (YEAC-Nigeria) ita ma ta tabbatar da faruwar lamarin.
Ƙungiyar ta ce hanyar sadarwarta ta matasa masu sa-kai da masu kare haƙƙin ɗan Adam a yankin Neja Delta ta bayar da rahoton mutuwar aƙalla mutane 37.
A cewar ƙungiyar, mutanen sun mutu ne bayan sun shaki wani abu da mazauna yankin ke kira “Indorama fuel.”

Source: Twitter
Najeriya ta yi asara saboda satar mai
A wani labarin kuma, kun ji cewa kamfanin mai na NNPCL ya ce ya yi asarar fiye da Dala biliyan 46 na gangan danyen mai miliyan 612 a cikin shekaru 10.
Kamfanin NNPCL ya ce yawan satar mai da ake a kasar ya wuce hankali wanda hakan ke jawo wa kamfanin da Najeriya asara ta makudan kudade.
Asali: Legit.ng

