NAF Ta Bude Shafin Daukar Sababbin Sojojin Sama, An Ji Abubuwan da Ake Bukata
- Rundunar Sojin Sama ta Najeriya ta sanar da bude shafin yanar gizo domin daukar sababbin ma'aikata maza da mata na BMTC 47/2026
- Daukar ma'aikatan zai shafi masu sana'o'i da wadanda ba su da sana'a, amma ban da wadanda suka kammala jami'a.
- Rundunar ta gargadi masu nema da kada su bai wa masu shiga tsakani kudi saboda tsarin neman aikin kyauta ne
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Rundunar Sojin Sama ta Najeriya (NAF) ta bude shafin daukar sababbin ma'aikata karkashin Basic Military Training Course (BMTC) 47/2026.
Daukar sababbin ma'aikatan zai shafi sojojin sama maza da mata karkashin rukuni biyu, wato masu sana'o'i da wadanda ba su da sana'a.

Source: Twitter
Rundunar sojin sama (NAF) ta sanar da hakan ne a shafinta na X ranar Laraba, inda ta ce za a bude shafin da kowa zai iya shiga ya cike daga yau Alhamis, 2 ga watan Satumba, 2026.

Kara karanta wannan
INEC ta bude shafin ɗaukar ma'aikatan da za su yi aikin zaɓen 2027? Bayanai sun fito
Sai dai NAF ta bayyana cewa babu yan Direct Short Service Commission (DSSC), wanda wata hanya ce ta daban ta daukar wadanda suka kammala jami'a a matsayin hafsoshi.
NAF gargadi masu neman aikin
Rundunar sojin sama ta shawarci masu son neman aikin da su yi amfani da shafin daukar ma'aikata na NAF na hukuma kawai wajen yin rajista.
Ta kuma bukaci masu nema su jira sai an fitar da cikakkun ka'idojin daukar ma'aikata na BMTC 47/2026 kafin su gabatar da bukatarsu.
NAF ta ce sharuddan cancanta, sana'o'in da ake nema da sauran ka'idoji na iya bambanta da wadanda aka yi amfani da su a daukar ma'aikata na baya.
Sharuddan da aka saba bukata
A daukar ma'aikata na BMTC da aka gudanar a baya, ana bukatar mai nema ya kasance dan Najeriya ta haihuwa, bai yi aure ba, yana cikin koshin lafiya kuma yana da cikakkiyar lafiyar jiki.
Haka kuma, galibi ana bukatar kada mai nema ya kasance yana da tarihin aikata laifi.
Sai dai rundunar ta bukaci masu nema su tabbatar da takamaiman sharuddan BMTC 47/2026 idan aka fitar da ka'idojin a hukumance.
A yawancin daukar ma'aikata na baya, ana kuma bukatar mai nema ya kasance yana da ingantaccen Lambar Shaidar Dan Kasa (NIN).
Ga masu neman aikin da ba su da sana'a, daukar ma'aikata na baya kan bukaci masu shekaru tsakanin 18 zuwa 22.
Haka kuma ana bukatar su tabbata sun ci darussa biyar, ciki har da Turanci da Lissafi, a jarabawar sakandare da ta dace.
A bangaren masu sana'a kuwa, galibi ana bukatar karin takardun shaidar kwarewa.
Wadannan na iya hada da diplima (ND), Nigeria Certificate in Education (NCE), Trade Test Certificate ko wasu takardun shaidar da aka amince da su, gwargwadon mukamin da ake nema.

Source: Twitter
Neman aikin sojan sama kyauta ne
Masu neman aikin za su kammala rajistarsu ta shafin NAF na hukuma sannan su sanya takardun da ake bukata.

Kara karanta wannan
Daga karshe: 'Yan N-Power da gwamnatin Tinubu ta hana kudadensu sun yanke Atiku za su zaba a 2027
NAF ta ce tsarin neman aikin kyauta ne, kuma rundunar ba ta amfani da wakilai ko masu shiga tsakani wajen daukar sabbin ma'aikata.
Saboda haka, an shawarci masu nema da su dogara da bayanan da ake wallafawa ta shafin daukar ma'aikata na NAF da sauran hanyoyin sadarwa na hukuma kawai.
Yadda aka karawa sojoji albashi
Kun ji cewa shugaba Bola Tinubu ya amince da sabon tsarin albashin sojojin Najeriya wanda zai fara aiki daga ranar 1 ga Satumba 2026
Babu kurtun soja da za a rika biya kasa da N180, 000 domin kuwa an yi wa kowa karin kudin da ya kai 30% zuwa 80% a Najeriya.
Asali: Legit.ng
