Matar da Ta Je Makkah Sau 3 da Sayar da Dumame, Ta Shekara 50 Tana Sana'ar

Matar da Ta Je Makkah Sau 3 da Sayar da Dumame, Ta Shekara 50 Tana Sana'ar

  • Hajiya Zara Mai Tuwo, mai shekaru sama da 80, ta shafe fiye da shekaru 50 tana sana’ar sayar da tuwon dawa a Lungun Filasku da ke yankin Fagge a Kano
  • Tsohuwar ta ce sana’ar ta taimaka mata wajen biyan kudin karatun ’ya’yanta, aurar da su da kuma sayen gidan da iyalinta ke zaune a ciki
  • Duk da tsufa ya rage mata karfin aiki, Hajiya Zara ta ce ba za ta iya daina sana’ar ba saboda yadda kwastomominta suka saba da abincinta, musamman Dumame

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Kano – Fiye da shekaru 50 kenan Hajiya Zara Mai Tuwo ke tashi tana nika garin dawa, kunna wuta da kuma dafa tuwo domin kwastomominta a Lungun Filasku, yankin Fagge da ke birnin Kano.

Kara karanta wannan

Barayin waya sun shiga gida sun kashe uwa mai yara 5 da wuka a Gombe

Duk da cewa yanzu ta haura shekaru 80 kuma tsufa ya rage mata karfin aiki, Hajiya Zara ta ce har yanzu tana da alaka ta musamman da sana’ar da ta dogara da ita wajen ciyar da iyalinta.

Hajiya Zara mai tuwo
Hajiya Zara a wajen da take sayar da tuwo. Hoto: Trust TV
Source: Facebook

Hajiya Zara ta fara sana’a da fura

Wani rahoto da Daily Trust ta wallafa ya nuna cewa Hajiya Zara ta shahara da tuwon dawa da ake ci da miyar kuka ko kubewa, tare da man shanu da nama.

Ta kuma yi suna wajen shirya Dumame, wato tuwon da aka bari daga dare ko kuma aka shirya da daddare, sannan a sake dumama shi da safe cikin miya domin a ci.

Hajiya Zara ta ce ta fara sana’ar sayar da fura kafin ta koma sana’ar tuwo lokacin da ’ya’yanta suke kanana.

“Wannan sana’a ta shafe sama da shekaru 50. Na fara da fura, daga baya na daina na koma tuwo lokacin da ’ya’yana suke kanana,”

In ji ta.

Sana’ar tuwo ta mata gata

Hajiya Zara ta ce sana’ar ta taimaka mata wajen biyan kudin makarantar ’ya’yanta da aurar da su, tare da sayen gidan da suke zaune a ciki.

Kara karanta wannan

Manyan 'yan siyasa na korafi kan tsare El Rufa'i bayan ya saki wasika

Ta bayyana cewa a baya tana fara aiki daga rana har zuwa dare, amma tsufa ya tilasta mata rage aikin zuwa lokacin yamma.

A kullum, tana fara shirye-shiryen da rana, inda take nika garin dawa, kunna wuta da dora tukwane domin dafa tuwo.

Kusa da ita kuma ana dafa miya mai dauke da nama da man shanu, lamarin da ke cika wajen da kamshin abinci.

“Ko ruwan sama ko sanyi ba ya hana ni yin wannan sana’a,”

In ji Hajiya Zara.

Ta ce sana’ar ce ta taimaka mata wajen zuwa Makka sau uku, aurar da ’ya’yanta da kuma mallakar gidan da iyalinta ke zaune.

Taswirar jihar Kano
Taswirar jihar Kano a Najeriya. Hoto: Legit
Source: Original

Maganar ’ya’yanta mai tuwon

Datti Usman, karamin dan Hajiya Zara, ya ce tun yana yaro bai taba sanin mahaifiyarsa ba tare da sana’ar tuwo ba.

Ya ce bayan rasuwar mahaifinsu a 1998, sana’ar mahaifiyarsu ta ci gaba da daukar nauyin bukatunsu.

Kara karanta wannan

Tinubu ya roki 'yan Najeriya alfarma a 2027, ya fadi dalilin neman tazarce

“Tun ina karami na san mahaifiyata da wannan sana’a, kuma duk bukatunmu ana biya ne da ita. Mahaifinmu ya rasu a 1998, amma wannan sana’a ce ta dauki nauyin karatuna,”

In ji Datti.

Datti, wanda aka haifa a 1982, ya yi karatun NCE a Kwalejin Ilimi ta Sa’adatu Rimi da ke Kano, kafin ya wuce Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya inda ya yi digiri.

Yanzu yana aiki a Hukumar Kula da Ilimin Firamare ta Jihar Kano, amma yana taimaka wa mahaifiyarsa a sana’ar idan ya dawo daga aiki.

Wani dan nata, Alhaji Ado, wanda yanzu ya kusa shekaru 50, shi ma ya ce ya taso ne yana ganin mahaifiyarsa tana wannan sana’a dare da rana domin kula da iyalinta.

An zargi Abba da kama 'yan adawa

A wani labarin, mun ruwaito cewa Amnesty International ta nuna damuwa kan zargin kama, tsarewa da kuma tsoratar da masu sukar Gwamnatin Jihar Kano.

Kungiyar ta ce wasu mutane sun fuskanci gayyata ko kamu daga jami’an tsaro bisa kalamai da rubuce-rubucen kafafen sada zumunta da suka soki Gwamna Abba Kabir Yusuf.

Amnesty ta ambaci Abba Ibrahim Kofar Nasarawa, wanda aka fi sani da Aiha K Nass, da kuma Murtala Muhammad Dawanau da Fatima Dayyabu a cikin mutanen da ta ce sun fuskanci matsalolii.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng