Kiristoci Sun Fusata kan Dokar Hana Wa'azi, Sun Shawarci Bola Tinubu

Kiristoci Sun Fusata kan Dokar Hana Wa'azi, Sun Shawarci Bola Tinubu

  • Kungiyar Organisation of African Instituted Churches ta shawarci Shugaba Bola Tinubu kan dokar hana wa'azi
  • Ta bukaci shugaban kada ya sanya hannu kan kudirin gyaran dokar FRSC da zai hukunta wa'azi a motocin haya
  • Kungiyar ta ce daidaita wa'azi da talla a cikin motocin haya ya saba da kundin tsarin mulki, saboda yana tauye 'yancin addini da fadin albarkacin baki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Kungiyar Organisation of African Instituted Churches (OAIC) reshen Najeriya ta yi martani kan hana wa'azi a motocin haya.

Kungiyar ta bukaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da kada ya sanya hannu kan kudirin gyaran dokar Hukumar FRSC.

Kiristoci sun taso Tinubu a gaba kan dokar hana wa'azi
Shugaba Bola Tinubu ya yi tagumi a taro. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Facebook

Rahoton Punch ya ce ƙungiyar ta ce sashe da ke haramta wa'azi a motocin haya yana barazana ga 'yancin da kundin tsarin mulki ya tanada.

Kara karanta wannan

An sako Tinubu a gaba ya yi murabus kafin zaben 2027 bayan rahoton Bankin Duniya

Kiristoci sun yi korafi kan dokar FRSC

A cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar, Dakta Israel Akinadewo, kungiyar ta nuna damuwa cewa kudirin ya sanya wa'azi a motocin haya cikin rukuni daya da talla da sauran ayyukan da aka haramta.

Kungiyar ta ce daidaita wa'azin bishara cikin lumana da harkar talla abu ne da bai dace ba, kuma ya saba da tanadin kundin tsarin mulkin Najeriya da ke kare 'yancin addini da kuma 'yancin bayyana ra'ayi.

Akinadewo ya bayyana cewa OAIC tana goyon bayan tabbatar da tsaro da doka a kan tituna, amma ta ce bai kamata a dauki wa'azi a matsayin laifi ko wata harkar kasuwanci ba.

Kungiyar ta kara da cewa tsawon shekaru, wa'azi a motocin haya ya kasance wata halastacciyar hanya ta yada sakonnin imani, bege, kyawawan dabi'u, tuba da zaman lafiya tsakanin al'umma.

OAIC ta gargadi cewa duk wata doka da za ta mayar da bayyana addini cikin lumana laifi na iya zama takurawa ga 'yancin 'yan Najeriya da kundin tsarin mulki ya tabbatar.

Kara karanta wannan

An taso Tinubu a gaba game da lafiyarsa kan sake neman takara a 2027

Saboda haka, kungiyar ta roki Shugaba Tinubu da kada ya amince da kudirin a yadda yake yanzu.

Ta kuma bukaci Majalisar Tarayya ta sake duba sassan da ake takaddama a kansu tare da tuntubar kungiyoyin addini, kungiyoyin fararen hula da sauran masu ruwa da tsaki.

Kiristoci sun ba Tinubu shawara kan dokar hana wa'azi
Shugaba Bola Tinubu na Najeriya. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: UGC

Bukatar Kiristoci ga gwamnatin Tinubu

Kungiyar ta sake jaddada biyayyarta ga doka da oda tare da kira ga masu wa'azi su gudanar da aikin yada addini cikin mutunta zaman lafiya.

Ta kuma bukaci gwamnati ta kare 'yancin addini da fadin albarkacin baki da suke ginshikin dimokuradiyyar Najeriya, cewar Vanguard.

A baya, Majalisar Dattawa ta ba da shawarar tarar N50,000 ga duk wanda aka samu da laifin talla, ciniki ko wa'azi a cikin motocin haya. Kudirin yanzu na jiran sahalewar shugaban kasa.

Idan shugaban kasa ya sanya hannu kan kudirin, za a kuma hukunta direbobin da suka ki ba jami'an FRSC hadin kai yayin gwajin shan giya da tarar N50,000, ko daurin watanni shida, ko kuma hukuncin duka biyun.

An ce gyaran dokar na daga cikin matakan inganta bin dokokin hanya da rage hadurran mota a Najeriya.

Kara karanta wannan

An taso ministan Tinubu a gaba ya yi murabus bayan mutuwar budurwa a gidansa

Kiristoci sun goyi bayan daukar Shettima

Mun ba ku labarin cewa wata kungiyar Kiristoci a yankin Arewacin Najeriya ta bayyana matsayarta kan sake daukar Kashim Shettima a matsayin mataimaki.

Shugaban kungiyar, Fasto Jolly Usman, ya ce ƙwarewar Shettima da haɗin gwiwarsa da Tinubu sun taimaka wajen inganta tsaro.

Ƙungiyar ta bukaci 'yan Najeriya su yi hukunci kan shugabanni bisa ayyukansu da nagartarsu, ba wai la'akari da bambancin addini kaɗai ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.