NAHCON za ta maido wa wasu alhazai da kudinsu makonni da kammala aikin Hajji
- NAHCON ta yi zama na musamman domin a duba yadda aikin hajjin shekarar 1447 ya gudana
- Shugaban hukumar ya yi alkawari za a maido wa mutane kudin da suka biya na aikin da ba a yi masu ba
- Ismail Abba Yusuf ya ce NAHCON ba za ta rika hulda da kamfanin da ba a ji dadin aiki da shi ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Hukumar NAHCON mai kula da aikin hajji ta tabbatar wa ‘yan Najeriya za a maido kudin da aka karba ba a yi masu aiki ba.
Akwai mahajjatan shekarar 2026 da suka biya kudi amma hukumar ba ta biya masu bukatunsu ba saboda haka kudinsu za su dawo.

Source: Getty Images
Shugaban NAHCON ya yi taro bayan aikin hajji
Daily Trust ta rahoto Ambasada Ismail Abba Yusuf yana cewa an fara duba kudin da aka batar a kan kamfanonin aikin hajji a Saudiyya.
Shugaban na hukumar NAHCON ya bayyana cewa tun farko an yi wannan yarjejeniya sa’ilin da aka gama sauke farali a kasa mai tsarki.
Ismail Abba Yusuf ya ja kunnen kamfanonin da Najeriya ta ke aiki da su, ya fada masu babu kobonsu da zai tafi a iska haka kurum.
Hukumar NAHCON ta nuna za ta yi watsi da duk kamfanin da ba a ji dadin aiki da shi ba.
Dole mahajjata su samu sa’ida na aikin da ba a yi masu da kyau ba. Kyawun aiki shi zai yi tasiri wajen mu’amala daga yanzu.

Source: Getty Images
Nasarori da kalubale a aikin hajjin 1447
Sabon shugaban na NAHCON ya bayyana cewa an samu wasu nasarori a aikin hajjin 1447 alal misali jigilar maniyyata a kan lokaci.
A karkashin tsarin Nusuk da aka kawo, Ismail Abba Yusuf ya ce an samu sauki wurin sha’anin biza kuma an inganta harkokin lafiya.
Sai dai an samu mahajjata 109 da suka tsallake matakin gwajin lafiya lokacin zuwa ibadar, wannan yana cikin tasgaron da aka fuskanta.
A wajen cin abinci ma NAHCON ta ce akwai inda abubuwa ba su tafi daidai ba kuma an samu matsi wajen sufuri da neman matsguni.
Bayan haka, hukumar ta koka da ‘yan matsaloli da aka samu wajen harkokin sa ido lokacin hajjin.
An wakilci Kashim Shettima a taron NAHCON
Mai girma mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya yi magana wajen taron da aka shirya domin nazarin abubuwan da suka faru.
Tsohon ministan harkokin birnin Abuja, Dr. Aliyu Modibbo Umar ya wakilci Shettima, inda aka ji yana kira ga jami’an aikin hajji na Najeriya.
Aliyu Modibbo Umar ya tuna masu cewa aikinsu yana bukatar su yi bakin kokarinsu, su tabbatar da gaskiya kuma su tsaya tsayin-daka.
Saudiyya ta yi gyare-gyaren bayan Hajji
Ana da labarin sababbin gyare-gyare da kasar Saudiyya ta bullo da su domin saukaka wa mahajjata gudanar da ibada a 'yan watannin nan.
Hukumar yada labarai ta kasar Saudiyya ta shirya wa 'yan jarida na gida da na waje rangadi na musamman don nuna musu ayyukanta.
An fahimci cewa cibiyar kula da aikin Adahi, ana sarrafa dabbobi kusan 300,000 a rana guda lokacin da Musulman duniya suke yin aikin Hajji.
Asali: Legit.ng

