Ministan Tinubu Ya Fito Ya Fadi Gaskiya, Ya Ce Farashin Man Fetur Zai Iya Kara Tsada a Najeriya
- Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa tashin farashin makamashi matsala ce da ta shafi duniya baki ɗaya ba iya Najeriya kadai ba ne
- Karaminin Ministan Albarkatun Mai ya yi gargadin cewa farashin man fetur na iya ƙara tashi idan rikicin Gabas ta Tsakiya ya ci gaba
- Heineken Lokpobiri ya kare cire tallafin man fetur, yana cewa an dauki matakin a lokacin da ya dace
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Karamin Ministan Albarkatun Man Fetur, Heineken Lokpobiri, ya ce tashin farashin man fetur matsala ce da ta shafi duniya baki ɗaya.
Ministan ya bayyana cewa lamarin tsadar man fetur na iya ƙara ta’azzara idan rikicin Gabas ta Tsakiya ya ci gaba.

Source: Twitter
Lokpobiri ya yi wannan furucin ne yayin da yake jawabi a cikin shirin Politics Today na gidan galabijin na Channels ranar Talata.

Kara karanta wannan
Tinubu na tsaka mai wuya, sama da 67% na yan Najeriya na so a dawo da tallafin fetur
Ya ce matsalolin da ’yan Najeriya ke fuskanta wajen ƙarancin ƙarfin saye sakamakon tsadar man fetur na kuma shafar Amurkawa da Turawa.
Dalilin tsadar fetur a Najeriya
Ministan ya ce:
“Saboda abin da ke faruwa a Gabas ta Tsakiya, ana sa ran farashin makamashi ba zai sauko ba. Ya kamata mu sani cewa man fetur da iskar gas kayayyaki ne da ake kasuwancinsu a duniya, abin da ake sayarwa a New York shi ne ake sayarwa a nan,”
Ya ƙara da cewa farashin makamashi ba ya bambanta sosai a sassan duniya, saboda haka matsalar ƙarancin ƙarfin saye da tsadar mai ba ta shafi ’yan Najeriya kaɗai ba.
“Ko a Amurka, ƙarfin sayee Amurkawa ya yi ƙasa, idan ka je Turai ma ƙarfin sayen Turawa ya yi kasa, farashin makamashi abu ne da ya shafi duniya, kuma tasirinsa ma na duniya ne,” inji shi.
Ministan ya ce ana sayar da ɗanyen mai da man fetur da aka tace a kasuwannin duniya, yana mai cewa Najeriya ba za ta iya ware kanta daga tsarin duniya ko kuma ta kayyade farashin man fetur yadda take so ba tare da dawo da tallafi ba.

Kara karanta wannan
"Za a iya cikin kwanaki 7"; Iran ta sanar da Amurka sharadin bude mashigar Hormuz
Tinubu na da ikon rage farashin mai?
Da aka tambaye shi ko gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ba ta da ikon rage ko ƙara farashin man fetur, ministan ya amsa da cewa ba ta da wannan ikon.
Lokpobiri ya ce:
“Ba mu da wannan ikon saboda an cire kayyade farashin gaba ɗaya, mun koma daidai da mafi kyawun ƙa’idojin duniya.
“Saboda ni jagoran OPEC ne, kuma ni ne shugaban tawagar Najeriya kan harkokin mai, ina zagayawa duniya baki ɗaya, kuma kowace ƙasa na fuskantar irin waɗannan matsaloli.

Source: Getty Images
Ministan ya kuma kare matakin Shugaba Bola Tinubu na sanar da cire tallafin man fetur a ranar rantsar da shi, yana mai cewa an dauki matakin ne a lokacin da ya dace.
Yan Najeriya na so a dawo da tallafi
Kun ji cewa Atiku Abubakar ya ce wani binciken SBM Intelligence ya nuna kashi 67.4% na ’yan Najeriya na son a dawo da tallafin man fetur.
Atiku ya ce sakamakon binciken ya nuna yadda iyalai, ma’aikata da ’yan kasuwa ke fuskantar matsin tattalin arziki yayin da tsadar man fetur ke ci gaba da ƙara tsadar rayuwa.
Asali: Legit.ng