Gwamnatin Tinubu Ta Cimma Yarjejeniya da Kasar Amurka kan Ma'adanan Najeriya

Gwamnatin Tinubu Ta Cimma Yarjejeniya da Kasar Amurka kan Ma'adanan Najeriya

  • Gwamnatin Najeriya da Amurka sun rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna domin bunƙasa fannin ma’adinan ƙasa a Najeriya
  • Yarjejeniyar za ta mayar da hankali kan bayanan ƙasa, binciken ma’adinai, sarrafa ma’adinai, ababen more rayuwa da ƙwarewar fasaha
  • Dele Alake ya ce Najeriya na son mayar da harkokin ma’adinai zuwa wani mataki na ɗorewar arziki ta hanyar ƙara sarrafa su a cikin gida

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

New York - Gwamnatin Tarayya da ƙasar Amurka sun rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna domin bunƙasa fannin ma’adinan ƙasa na Najeriya.

An rattaba hannun kan yarjejeniyar ne a gefen taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 81, wanda ke gudana a birnin New York na kasar Amurka.

Dele Alake.
Ministan harkokin ma'adanai, Dele Alake tare Mataimakin Ministan Harkokin Wajen Amurka, Christopher Landau Hoto: @AlakeDele
Source: Twitter

Channels tv ta ce Ministan Ma’adinan Ƙasa, Dele Alake, da Mataimakin Ministan Harkokin Wajen Amurka, Christopher Landau, ne suka rattaba hannu kan yarjejeniyar a Ofishin Jakadancin Najeriya da ke New York.

Kara karanta wannan

An yi wa su Kwankwaso alƙawarin ƙuri'u miliyan 10 a zaben shugaban kasa na 2027

Alake ya yi bayanin yarjejeniyar

Da yake magana a wajen taron, Alake ya bayyana yarjejeniyar a matsayin wani tsari da aka tsara domin nan gaba, wanda zai buɗe ƙofa ga ƙasashen biyu su haɗa gwiwa kan bayanan ƙasa da binciken ma’adinai, da sarrafa ma’adinai.

Ya ƙara da cewa tsarin ya cimma matsayar bai ɗaya tsakanin ƙasashen biyu cewa hanyoyin samar da ma’adinai masu muhimmanci dole su kasance amintattu, masu jure wa sauye-sauye da kuma gina su bisa saka hannun jari.

“Bari in bayyana burin Najeriya a fili, ba mun zo nan domin bude wa wasu tsiraru hanyar da za su amfana ba ne, burin mu shi ne gyara wannan fanni ya zama hanyar arziki ta hanyar sarrafa ma'adanai a cikin gida.
"Ta haka zamu karfafa harkokin sarratfa ma’adinai a cikin gida, samar da sabbin ƙwarewa, ayyukan yi masu inganci ga yan kasa da sababbin damammaki ga ’yan kasuwar Najeriya.

Kara karanta wannan

Gwamnoni, ministoci, malamai, sarakuna za su hadu don yi wa Najeriya addu'a

- In ji Dele Alake.

Ministan ya kuma ce aiwatar da yarjejeniyar zai taimaka wajen cimma manufofin fadada tattalin arziki na ajandar Renewed Hope ta Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu tare da bunƙasa masana’antu.

Amurka ta yi maraba da hakan

Da yake magana kan ci gaban, Mataimakin Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Landau, ya nuna cikakken goyon baya ga matsayar Najeriya, kamar yadda The Cable ta rahoto.

Ya ce a matsayin Najeriya na ƙasar da tattalin arzikinta ke bunƙasa cikin sauri a Afirka kuma mafi yawan al'umma, Najeriya ƙasa ce mai tasiri a yankin da ta cancanci haɗin gwiwa da Amurka.

Trump.
Shugaban Amurka, Donald Trump da takwaransa na Najeriya, Bola Ahmed Tinubu Hoto: Bayo Onanuga
Source: Twitter

Ya tabbatar da cewa yarjejeniyar za ta kawo ƙarin wadata ga ƙasashen biyu, yana mai cewa Amurka na farin cikin tallafa wa bunƙasar tattalin arzikin Najeriya.

“Saƙon da muke aikawa shi ne cewa Amurka da Najeriya abokan hulɗa ne.
“Ƙarƙashin jagorancin Shugaba Trump da Shugaba Tinubu, Amurka da Najeriya sun yi abubuwa da dama tare a cikin shekara ɗaya da rabi da ta gabata waɗanda ba mu taɓa yin su a baya ba," in ji shi.

Kara karanta wannan

Karya ta ƙare: Yan bindiga sun ga bala'in da ya fi ƙarfinsu, kusan 20 sun bakunci lahira

Dalilin Tinubu na tura Shettima Amurka

Kun ji cewa Ministan Yada Labarai, Mohammed Idris ya bayyana dalilin da ya sa Shugaba Bola Tinubu ya tura mataimakinsa Kashim Shettima ya jagoranci tawagar Najeriya zuwa UNGA.

Ya ce Shettima yana ɗauke da cikakken ikon Shugaban Ƙasa da na Najeriya, yana mai watsi da ra’ayoyin cewa rashin Tinubu a taron zai rage martabar Najeriya a fagen diflomasiyya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262