Yadda Tinubu Ya Barar da Goyon Bayan Arewa cikin Shekaru 3 in ji Kusa a APC

Yadda Tinubu Ya Barar da Goyon Bayan Arewa cikin Shekaru 3 in ji Kusa a APC

  • Salihu Tanko Yakasai ya yi rubutu da ya yi ikirarin Bola Ahmed Tinubu ya rasa goyon bayan da mutanen Arewa suka ba shi a 2023
  • Matashin ‘dan siyasar ya kawo maganar yadda gwamnati mai-ci ta daina damawa da irinsu Nasir El-Rufai da Dr. Abdullahi Ganduje
  • Yakasai wanda aka fi sani da X a Shafin Twitter ya jefi gwamnatin Tinubu da zargin fifita wani yanki idan za a yi rubon mukamai

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Kano - Salihu Tanko Yakasai ya yi wani rubutu inda ya yi bayani game da yadda ya ce Bola Ahmed Tinubu ya rasa goyon bayan Arewacin Najeriya.

Tsohon hadimin na gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya ce babu ta yadda Shugaban na Najeriya zai zarce ba tare da kuri’un ‘yan Arewa ba.

Tinubu
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu tare da na-kusa da shi a masallaci Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Source: Facebook

Salihu Yakasai ya zargi Tinubu da watsi da ‘yan Arewa

Kara karanta wannan

Falle 1 ce’; Jigon matasa a APC ya bar jam’iyya, ya hango shan kashi a 2027

A rubutun da ya yi a shafin X, Salihu Tanko Yakasai ya dauko daga yadda manyan ‘yan siyasar Arewa suka marawa takarar Tinubu baya a zaben 2023.

Salihu Yakasai ya ce Tinubu yana da alaka da irinsu Aliyu Wamakko, Rabiu Musa Kwankwaso, Abdullahi Umar Ganduje da Abubakar Badaru gabanin zabe.

Rubutun ya ce wadannan manya har da su Nasir El-Rufai sun taimaka wajen ganin shugaban kasar ya samu takara, suka yaki wasu boyayyun masu iko.

Ana zargin cewa na kusa da Muhammadu Buhari a lokacin ba su so Tinubu ya samu mulki ba.

Marubucin ya ce goyon bayan da wadannan ‘yan siyasa suka ba shugaban na yau a lokacin da yake neman takara, ya hada su matsala da manyan Arewa.

Ya tunawa jama’a yadda suka tunkari Marigayi Buhari a Aso Rock, suka nemi jin wane ne wanda yake goyon bayan ya zama magajinsa a Mayun 2023.

Salihu Yakasai ya ce wannan karfin hali ya taimaka aka yi amfani da malaman addini a Arewacin Najeriya domin tallata tikitin Musulmi da Musulmi.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya fara shari'a da hadiman Abba Kabir 4, ya nemi a bi masa kadunsa

A cewarsa, ana ganin cewa tsare-tsaren da gwamnatin baya ta fito da su ba komai ba ne illa yunkurin karya takarar Tinubu da Kashim Shettima.

Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Mai girma Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a ofis a Aso Rock Hoto: Abdulaziz Abdulaziz
Source: Facebook

Labari ya canza a Arewa bayan zabe

Duk da 63% na kuri’un APC a zaben shugaban kasa sun fito daga Arewa ne a 2023, akwai koke-koken rashin adalci wajen nadin mukaman gwamnatin tarayya.

Bayan lashe zabe, yake cewa sai ga shi an taso Nasir El-Rufai a gaba kuma an yi waje da Abdullahi Umar Ganduje daga shugabancin jam’iyyar APC.

Rubutun ya ce shari’ar Abubakar Malami ta kara nuna akwai son kai a binciken da ake yi. Tun kwanaki aka matsa masa, har aka karbe kadarorinsa.

Zargin fifita wani yanki da mukamai & ayyuka

Wani abin da yake ci wa yankin tuwo a karya shi ne zargin ana yi wa kiristoci kisan gilla a kasar kamar yadda irinsu Punch suka ruwaito.

A daidai lokacin da jihohin Arewa suke kuka ne kuma ya ce gwamnatin tarayya tana ware makudan kudi domin a gyara tashoshin ruwa a Legas.

Idan aka tashi rabon mukamai daga jihohin Arewa kuwa, Yakasai ya ce Tinubu sai ya zakulo mutanen da suka fito daga Kwara da Kogi.

Kara karanta wannan

Yakin Iran da Isra'ila: Tinubu ya dauko hanyar rage wa yan Najeriya radadin rikicin

A karshe ya ce lamarin ya soma canza wa alhali talakawan Arewa ne suka tsaya tsayin daka APC ta yi nasara a zaben shugaban kasa na 2023.

Ya ce makomar Tinubu ta ta’allaka ne da goyon bayan da zai samu daga wannan yanki ko kuma talakawa su yi watsi da shi, su bi tafiyar hadaka.

Dawisu ya soki gwamnatin Tinubu

Ana da labari cewa tsohon hadimin Abdullahi Umar Ganduje, Salihu Tanko Yakasai, ya yi magana kan zargin rashin adalci da rashin daidaito wajen rabon dukiyar kasa.

Salihu Yakasai ya yi zargin cewa an ware biliyoyin Naira domin ayyuka a jihar Legas cikin shekaru biyu na mulkin Bola Tinubu, amma an bar Arewa hannu-Rabbana.

Hakan na zuwa ne bayan tsohon 'dan takarar gwamnan ya bar APC yayin da ake ta ce-ce-ku-ce kan zargin nuna bambanci tsakanin yankunan Najeriya wajen ayyuka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng