Abba Ya Tasamma Inganta Ilimi, Ya Fitar da Umarni 3 da Za Su Canja Rayuwar Malamai

Abba Ya Tasamma Inganta Ilimi, Ya Fitar da Umarni 3 da Za Su Canja Rayuwar Malamai

  • Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ba da umarnin daukar ma’aikatan tsaro 17,600 don tsaron makarantu da ke kananan hukumomi 44 a Kano
  • Gwamnatin ta bayyana cewa jami’an tsaron za su yi aiki domin kare rayukan dalibai, malamai da kuma kayayyakin makaranta
  • Domin kara inganta koyarwa, gwamnatin Kano ta amince da fitar da Naira miliyan 200 don ba malaman firamare da sakandare bashi

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar KanoGwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya kaddamar da shiri domin inganta harkar ilimi da tabbatar da tsaro a makarantun gwamnati da ke fadin jihar.

Gwamnan ya ba da umarnin daukar sababbin masu tsaron makarantu 17,600, inda za a kai ma’aikata 400 a kowace karamar hukuma domin kare ɗalibai, malamai da kayayyakin makarantu daga barazana.

Gwamna
Gwamna zai ba malamai aron kudi su sayi mota Horo: Ibrahim Adam
Asali: Facebook

Wannan na kunshe a cikin wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama'a na Gidan Gwamnatin Jihar Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Za a horar da jami’ai a jihar Kano

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa za a horar da waɗannan jami’an tsaro sannan kuma za a tura su zuwa makarantu domin gudanar da ayyukansu tare da haɗin gwiwa da hukumomin tsaro na ƙasa.

A cewar sanarwar:

“Wannan mataki na daga cikin kudurinmu na kare rayukan ‘ya’yanmu da malamansu daga barazanar da ke kunno kai. Ba za mu lamunci yadda rashin tsaro ke barazana ga makomar shugabannin gobe ba."

Gwamnan Kano ya kaddamar da wasu ayyuka

Har ila yau, gwamna Abba ya ƙaddamar da wani shiri na kimiyya da fasaha (ICT) da Bankin Duniya ke tallafawa karkashin aikin AGILE.

Aikin ya haɗa da girka na’urorin haska rana a makarantu 200 da kuma bayar da kwamfutoci 250 a kowace makaranta domin ƙarfafa ilimin fasahar zamani.

Dalibi
Gwamna Abba ya ce za a ba dalibai da malamai kariya a Kano Hoto: Ibrahim Adam
Asali: Facebook

A wani ƙarin mataki na ƙarfafa gwiwar malamai da inganta jin daɗin su, gwamnan ya amince da bayar da tallafin aron kudi na Naira miliyan 200.

Za a bayar da rancen ga malamai na makarantun firamare da sakandare su sayi motoci domin sauƙaƙe musu wahalar sufuri da ƙara musu kuzari a aikin su.

Sanarwar da Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar ta kara da cewa:

“Wannan shirin rancen motoci na daga cikin dabarun gwamnati na ƙarfafa malamai da inganta harkar koyarwa."

Ana shirin farfado da ilimin Kano

A baya, kun samu labarin cewa gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya dauki sababbin matakai domin farfado da tsarin ilimi a jihar, an fara da daukar malamai 10,000.

Abba Kabir Yusuf ya ce matakin yana cikin kudurinsa na tabbatar da ingantaccen ilimi da kuma ganin Kano ta kasance sahun gaba a tsakanin jihohin Najeriya.

Gwamna Abba ya bayyana cewa akwai tarin matsaloli da ke hana ci gaban ilimi a jihar, ciki har da rshin isassun kwararrun malamai, kuma duka za a magance su a hankali.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.