Kasar Iran Ta Kunyata Shugaban Amurka bayan Ya Yi Maganar Komawa Teburin Sulhu

Kasar Iran Ta Kunyata Shugaban Amurka bayan Ya Yi Maganar Komawa Teburin Sulhu

  • Babban jami’in tsaron Iran ya yi watsi da tattaunawa da Amurka bayan Donald Trump ya ce a shirye yake a koma teburin sulhu
  • Mohsen Rezaei ya ce kasar Musulunci ba za ta yi wata tattaunawa ba har sai an cika sharuddan da Iran ta gindaya
  • Shugaba Trump ya ce Iran na son a yi yarjejeniya cikin gaggawa domin kawo karshen yakin Gabas ta Tsakiya, lamarin da kasar ta musanta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Iran - Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta bayyana alamun ba za ta koma teburin sulhu da Amurka ba yayin da rikici ke ci gaba da ƙamari a yankin Gabas ta Tsakiya.

Babban jami’in tsaron Iran ya yi watsi da yiwuwar tattaunawa da Amurka bayan Shugaba Donald Trump ya ce a shirye yake ga sake komawa tattaunawa kan yakin Gabas ta Tsakiya.

Kara karanta wannan

Sheikh Gumi ya shiga maganar Sanata Shehu Buba da ake zargi da ta'addanci

Shugaban Iran.
Shugaban kasar Musulunci ta Iran, Masoud Pezeshkian Hoto: Anadolu
Source: Getty Images

Sakataren Majalisar Koli ta Tsaron Kasa ta Iran, Mohsen Rezaei, ya wallafa a shafinsa na X cewa bai kamata kalaman Trump da yake yawan sauya ra'ayi su dauke hankalin jama’a ba.

Iran ta yi fatali da tayin Amurka

Hadimin jagoran addinin kasar Iran, Mojtaba Khamenei ya ce:

“Kada ku bari sakonnin Shugaban Amurka masu karo da juna su dauke hankalinku — daga ‘babu tattaunawa’ zuwa ‘a shirye muke mu yi magana’,” in ji Rezaei.

Ya kara da cewa yanayin da ya shafi man fetur da mashigar ruwa ta Hormuz ya sauya, yana mai cewa ba za a iya dakile abin da ke tafe ta hanyar kokarin shawo kan matsalar kawai ba.

“Babu tattaunawa har sai an cika sharuddan Iran. Haka ne!” in ji shi.

Trump ya bude kofar tattaunawa

A ranar Litinin da ta gabata, Shuganan Amurka Donald Trump ya ce ya bude kofar tattaunawa da Iran, bayan makonni yana cewa lokaci bai yi da za a kulla yarjejeniya domin kawo karshen yakin ba.

Kara karanta wannan

Yaki ya yi tsanani: Trump ya fadi lokacin da rigimarsa da Iran za ta zo karshe

A wata sanarwa da ya fitar, Shugaba Trump ya ce Iran da ke fama da matsaloli bayan matakan da Amurka ta dauka a kanta, na son a yi yarjejeniya cikin gaggawa.

“Kasar Iran da ke fama da gazawa tana son yin yarjejeniya, cikin gaggawa kuma matuka. Zan yanke shawarar ko Amurka za ta zabi shiga tattaunawar ko a’a, mune za mu bude kofa,” in ji Trump.
Trump.
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump yana magana da manema labarai a White House Hoto: Alex Wong
Source: Getty Images

Iran ta dage kan sharuddan da ta kafa

Iran ta sha bayyana wasu bukatu a matsayin sharuddan kawo karshen yakin da kuma toshe mashigar Hormuz.

Daga cikin bukatun akwai biyan diyya kan barnar da yakin ya haddasa da kuma dage takunkuman da aka kakaba wa kasar.

Iran ta farmaki jiragen yakin Amurka

Kun ji cewa jiragen saman sojin Amurka da dama sun samu lahani sakamakon wani harin da Iran ta kai da daddare kan wani sansanin sojin Amurka da ke Jordan.

Wani jirgin A-10 Thunderbolt, wanda aka fi sani da Warthog, an kai masa hari har aka rasa ɗaya daga cikin fikafikansa, yayin da kusan jiragen F-15 guda takwas suka samu ƙananan lahani.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262