Izala Ta Fadi Halin da Sheikh Jingir ke Ciki bayan Yada Cewa ba Shi da Lafiya
- Kungiyar Izala mai hedkwata a Jos ta yi karin bayani game da rade-radin da ake yi na cewa shugaban malaman ta ba shi da lafiya
- Jami'in kungiyar ya bayyana hakikanin halin da malamin ke ciki tare da fadin wasu ayyukan addini da zai gudanar a jihar Filato
- Izala ta yi martani ne bayan yada jita-jitar cewa Sheikh Muhammadu Sani Yahaya Jingir ba shi da lafiya yana bukatar addu'a
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Filato - Kungiyar Izala ta karyata rade-radin cewa shugaban malaman ta, Sheikh Muhammad Sani Yahaya ba shi da lafiya.
Hakan ya biyo maganganun da jama'a suka rika yadawa a kafafen sadarwa suna rokon a taya malamin da addu'a domin samun sauki.

Source: Facebook
Sheikh Jingir yana lafiya lau
A wani sako da ya wallafa a Facebook, jami'in yada labaran kungiyar Izala a Jos, Ibrahim Maina Muhammad ya sanar da cewa Sheikh Sani Yahaya Jingir yana cikin koshin lafiya.
Ya ce:
"Mun ga wani faifan bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta, inda ake bayyana cewa Ash-Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ba shi da lafiya."
Babu shakka, babu wani ɗan Adam da yake rabuwa da larura ko rashin lafiya a wasu lokuta. Sai dai kuma, waɗanda suka yaɗa wannan labari cewa Sheikh na fama da jinya, ba su yi daidai da hakikanin abin da yake faruwa ba."
Ya kara da cewa:
"Muna sanar da al'umma cewa wannan magana ba ta da tushe."
Sheikh Jingir zai yi nasiha a Jos
Bayan tabbatar da cewa Sheikh Jingir yana cikin koshin lafiya, Ibrahim Maina ya bayyana cewa malamin zai jagoranci nasihar Juma'a a yau, 3 ga Yulin 2026.
Ya ce:
"Alhamdulillah, Ash-Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir yana cikin koshin lafiya, kuma yana ci gaba da gudanar da ayyukansa na ilimi da da'awa kamar yadda aka saba."
"Da yardar Allah, zai gabatar da nasiha a Masallacin 'Yan Taya kamar yadda ya saba.
"Muna roƙon Allah Maɗaukakin Sarki Ya karawa rayuwar Sheikh Albarka da kariya, Ya kuma amfanar da al'umma da iliminsa da shawarwarinsa. Amin."

Source: Facebook
Izala a Gombe ta yi magana
Shugaban malaman kungiyar Izala a jhar Gombe, Sheikh Hamza Adam Abdulhamid ma ya tabbatar da cewa Sheikh Jingir na cikin koshin lafiya a wani ako da ya wallafa a Facebook.
Ya ce:
"Kwamitin yada labarai na JIBWIS Jihar Gombe ya ja hankalin al'umma kan wani bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta dangane da Sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir."
"Muna sanar da al'umma cewa, zuwa lokacin fitar da wannan sanarwa, babu wani ingantaccen bayani da ke tabbatar da abin da ake yaɗawa.
"Saboda haka, muna kira ga jama'a da su yi taka-tsantsan wajen karɓa ko yaɗa labaran da ba a tabbatar da sahihancinsu ba."
An yi hukunci a masalacin ATBU
A wani labarin, mun kawo muku cewa shugabannin jami'ar ATBU sun yi bayani kan matsayar da suka dauka game da ibada a masallacin jami'ar.
An saka dokar hana yin duk sauran ibada a masallatan makarantar koma bayan salloli biyar har sai bayan wani kwamitin da aka nada ya fitar da rahoto.
An fara ce-ce-ku-ce game da jami'ar ATBU ne bayan samun rahoton da ke nuna cewa an ba 'yan Tijjaniyya fili su gina masallaci na musamman.
Asali: Legit.ng

