Sauki Ya Zo: Gwamnatin Tarayya Ta Rage Harajin Shigo da Motoci zuwa Najeriya
- Shugaban hukumar kwastam ta Najeriya (NCS) Adewale Adeniyi ya sanar da cewa an rage harajin shigo da gwanjon motoci kashi 15 zuwa kashi 5 cikin 100
- Adeniyi ya bayyana hakan ne a gaban kwamitin majalisar wakilai a Abuja yayin da yake kare kasafin kudin NCS na 2026
- Shugaban kwamitin Leke Abejide ya yaba wa gwamnatin Tinubu akan wannan matakin da ya ce zai saukaka wa al'umma
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Shugaban hukumar Kwastam ta Najeriya (NCS), Adewale Adeniyi, ya sanar da cewa gwamnatin tarayya ta rage harajin shigo da motoci a cikin kasar.
Adewale Adeniyi ya bayyana cewa ragin harajin ya shafi motocin da aka taba amfani da su da kuma sababbi fil.

Source: Facebook
Jaridar TheCable ta kawo rahoton cewa Adeniyi ya fadi haka ne a ranar Litinin, 6 ga watan Yulin 2026 a gaban kwamitin majalisar wakilai kan hukumar Kwastam.

Kara karanta wannan
'Dalilin da ya sa Majalisar Dattawa ta amince da kasafin N1.3bn don ma'aikatar bogi'
Adeniyi ya bayyana a gaban kwamitin ne domin kare tsarin kasafin kudaden hukumar na shekara ta 2026.
Yadda aka rage harajin shigo da motoci
A cewar shugaban na NCS, motocin da aka taba amfani da su za a biya kashi 5 cikin 100 a matsayin haraji maimakon kashi 15 da ake biya a baya.
Haka kuma, Adewale Adeniyi ya bayyana cewa sababbin motoci, harajinsu ya sauka daga kashi 20 zuwa kashi 10 cikin 100.
Ya ce an tsara wadannan canje-canje ne a cikin takardar manufofin haraji ta shekara ta 2026, kuma an fara aiwatar da su tun daga watan Mayun 2026, The Punch ta kawo labarin.
Adeniyi ya nuna cewa ko da yake manufofi da dama a cikin takardar za su kara samun kudi ga gwamnati, saukar da harajin motocin na iya rage kudaden da kwastam ke tattarawa.
"Muna da sabuwar dokar harajin da aka tsara a cikin manufofin kasuwancin 2026. Muna tsammanin wadannan matakai za su kara kudaden da muke tattarawa."
"Amma a daya bangaren, an rage harajin motoci da kudin da ake karba a kai sosai."
- Adewale Adeniyi
'Yan majalisa sun yi tambayoyi da yabo
Alex Mascot, dan majalisa daga jihar Abia, ya yi tambaya kan ko rage harajin zai isa ya hana masu shigo da kaya zuwa Cotonou.
"Idan an rage kashi 5 daga harajin da ake biya lokacin shigo da kaya kasar, me ya sa mutane har yanzu suke kai kayan nasu Cotonou?"
"Na san masu shigo da kaya da yawa suna guduwa daga kasar saboda yawan harajin."
- Alex Mascot

Source: Facebook
Shugaban kwamitin, Leke Abejide, ya bayyana wannan gyaran haraji a matsayin abin da zai saukakawa 'yan Najeriya.
"Ina so jama'a su sani cewa gwamnatin Najeriya tana yin wani abu mai amfani. Mutane sun dade da bukatar hakan, yanzu an yi shi. Ya kamata mu yabi gwamnatin tarayya, mu gode wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu saboda wannan matakin."
- Leke Abejide
Kwastam ta tara kudin shiga
A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar kwastam da ke tashar jiragen ruwa ta Tin Can Island, ta bayyana makudan kudaden da ta tara.
Hukumar wadda ke a tashar da ke jihar Legas ta bayyana cewa ta samu kuɗaɗen shiga har Naira biliyan 111.2 a watan Mayun shekarar 2026.
Kwanturolan yankin ya bayyana cewa kwastam za ta ci gaba da aiki tukuru bayan wannan nasara tare da ƙoƙarin ƙara yawan kuɗaɗen shiga fiye da yadda aka samu a baya.
Asali: Legit.ng

