Hukumar Kwastam
A wannan rahoton za ku ji cewa gwamnatin tarayya ta ayyana dokar ta baci a kan tashar ruwa ta Onne da ke jihar Ribas saboda shigo da makamai ba bisa ka'ida ba.
Jami'an hukumar kwatsam sun yi nasarar damke wata babbar motar DAF da aka ɓoye kunshi 1, 153 na hodar iblis da kudinsa ya kai aƙalla N57,668,448.
Bayan daukar alkawarin daukar matakan saukaka farashin abinci a kasa, gwamnatin tarayya ta fitar da sharudan shigo da kayan abinci ba tare da haraji ba.
Hukumar kwastam ta fitar da sanarwa kan sharuddan shigo da abinci daga ketare zuwa Najeriya ba tare da biyan haraji ba ga yan kasuwa domin saukakawa talaka.
Shugaban hukumar kwastam ya bayyana cewa dage haraji kan shigo da kayayyakin abinci zai fara a sati mai zuwa. Bashir Adeniyi ya ce ana sa ran abinci ya yi sauki.
Shugaban hukumar kwastam na ƙasa, Bashir Adeniyi ya ce ana sa ran za a samu saukar farashin kayayyaki a nan ba da jimawa ba yayin da aka dakatar da haraji.
Hukumar kwastam ta kasa ta bayyana cewa zanga-zanga da ƴan Najeriya ke shirin gudanarwa ba za ta dakatar da Aikinta a tashar jirgin ruwan Apapa ba.
Wasu miyagun 'yan bindiga dauke da makamai sun kai farmaki a sansanin jami'an hukumar kwastam a jihar Kebbi. Sun hallaka jami'i daya tare da sace wani jami'in.
Hukumar kwastam ta Najeriya ta yi asarar daya daga cikin jami'anta a jihar Jigawa. Jami'in ya rasa ransa ne bayan wani dan fasa kwauri ya buge shi da mota.
Hukumar Kwastam
Samu kari