Makiyaya Sun Cinnawa Dakin Kwanan Dalibai Dauke da Mutum 80 Wuta? Yan Sanda Sun Yi Bayana

Makiyaya Sun Cinnawa Dakin Kwanan Dalibai Dauke da Mutum 80 Wuta? Yan Sanda Sun Yi Bayana

  • An yada wasu rahotanni masu nuna cewa wasu da ake zargin makiyaya ne sun kona wai dakin kwanan dalibai a jihar Imo
  • Rundunar 'yan sandan jihar Imo ta fito ta yi magana kan rahotannin masu cewa lamarin ya ritsa da kusan mutane 80.
  • Kakakin rundunar Henry Okoye ya bukaci jama'a da su rika tabbatar da sahihancin labarai kafin su rika yada su

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Imo - Rundunar 'yan sandan jihar Imo ta yi magana kan zargin cewa wasu makiyaya sun kai hari a wani dakin kwanan dalibai.

Rundunar 'yan sandan ta yi watsi da zargin cewa wasu da ake zargin makiyaya ne sun kai hari wani dakin kwanan dalibai, inda ta bayyana rahoton a matsayin na kanzon kurege.

Yan sanda sun musanta zargin kona dakin kwanan dalibai a Imo
Shugaban rundunar 'yan sandan Najeriya, Olatunji Rilwan Disu Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

An yi zargin cewa makiyaya sun yi kone-kone

Kara karanta wannan

An rike dan ta'adda da ya nufi fadar sarki da bindiga zai kai hari

Jaridar The Punch ta ce kakakin rundunar, DSP Henry Okoye, ne ya bayyana haka a ranar Lahadi, 5 ga watan Yulin 2026 biyo bayan rahotanni da ke yawo a dandalin Facebook game da zargin harin.

Rahoton ya yi zargin cewa fiye da dalibai 80 ne suka makale a cikin wani dakin kwanan dalibai da aka cinnawa wuta a kusa da makarantar kimiyya da fasaha ta gwamnatin tarayya da ke Nekede, Owerri, ta hanyar wasu da ake zargin makiyaya ne.

Me 'yan sanda suka ce kan lamarin?

Okoye ya ce rahoton gaba dayansa na bogi ne, na yaudara, kuma yana iya haifar da fargaba marar amfani a tsakanin mazauna yankin.

Ya yi kira ga jama'a da su yi watsi da rahoton sannan su guji yada bayanan da ba a tantance ba, yana mai gargadin cewa irin wannan labari na iya haifar da tsoro, fargaba, ko tayar da hankalin jama'a.

Rundunar ta kuma yi kira ga mazauna yankin da su rika tantance gaskiyar bayanai ta hanyar amfani da madogara masu inganci kuma na hukuma kafin su yada su a shafukan sada zumunta ko wasu wuraren.

Kara karanta wannan

Mutumin da ya sayar da yaron abokinsa a kan N1.3m ya tona yadda suke satar yara a Najeriya

An bukaci mutane su rika tantance labarai

“Rundunar yan sandan jihar Imo ta lura da wani labari na yaudara da aka yada a dandalin Facebook a yau, Lahadi 5 ga Yuli, 2026, wanda ke zargin cewa makiyaya Fulani sun cinnawa dakin kwanan dalibai wuta a Nekede, Owerri, inda suka kulle dalibai sama da 80 a cikin ginin da ke cin wuta."
“Rundunar tana son bayyana karara ba tare da wata-wata ba cewa rahoton gaba dayansa na bogi ne, na yaudara, kuma yana iya haifar da fargaba marar amfani a tsakanin mazauna yankin."
“Saboda haka, rundunar tana kira ga al'umma da su yi watsi da wannan labari na bogi kuma su guji yada bayanan da ba a tantance ba wadanda ke da ikon haifar da tsoro, fargaba, ko tayar da hankalin jama'a."

- Henry Okoye

An zargi makiyaya da kona dakin kwanan dalibai
Taswirar jihar Imo, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

'Yan sanda sun kama mutane a Kaduna

A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan sanda sun cafke wasu mutane da ake zargin akwai hannunsu a kisan malamar Islamiyya, Ummulkhairi a Kaduna.

Kara karanta wannan

Rikicin kabilanci ya barke a Niger, an kona mutane da ransu

Wasu fusatattun mutane da suka take doka sun hallaka malamar addinin Musulunci bayan sun yi mata dukan tsiya a yankin Maraban Jos.

Gwamna Uba Sani wanda ya sha alwashin ganin an yi adalci, ya bayyana cewa an kama sama da mutum 100 da ake zargi da hannu a lamarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng