Sabon Salo: Shugaban Karamar Hukuma Ya Shiga Hisbah, Gwamna Ya Karrama Shi

Sabon Salo: Shugaban Karamar Hukuma Ya Shiga Hisbah, Gwamna Ya Karrama Shi

  • Gwamnan Jigawa, Umar Namadi, ya karrama Shugaban Karamar Hukuma saboda shiga horon Hisbah na mako guda da kansa
  • Dan siyasar ya kunshi jami’an Hisbah 2,449 daga kananan hukumomi 27, yayin da gwamnati ta kara alawus dinsu
  • Gwamnati ta samar da motocin Toyota Hilux 27 tare da ci gaba da gyare-gyaren Hisbah domin inganta tsaro, tarbiyya, zaman lafiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Dutse, Jigawa - Gwamnan Jigawa, Malam Umar Namadi, ya karrama Shugaban Karamar Hukumar Birniwa, Hon. Shehu Baba Birniwa, saboda shiga horon hukumar Hisbah da kansa.

Shehu Baba ya shiga horon ne bisa radin kansa, inda ya yi mako guda tare da jami’an Hisbah 2,449 da aka horas a jihar.

An karrama shugaban karamar hukuma kan shiga atisayen Hisbah
Gwamna Umar Namadi yayin bikin karrama shugaban karamar hukuma bayan atisayen Hisbah. Hoto: Umar Namadi.
Source: Facebook

Mataimakin Gwamnan Jigawa, Injiniya Aminu Usman, wanda ya wakilci Gwamna Namadi, ya ba shi lambar yabo yayin bikin kammala horon, cewar The Nation.

Kara karanta wannan

Melaye ya yi gagarumin gargadi ga Tinubu idan EFCC ta kuskura ta cafke Atiku

Gwamna Namadi ya yaba wa ciyaman a Jigawa

Gwamna Namadi ya yaba wa Shehu Baba saboda nuna kyakkyawan jagoranci ta hanyar shiga horon tare da jami’an Hisbah.

Ya bayyana cewa shiga horon da shugaban karamar hukumar ya yi ya nuna jajircewarsa wajen tallafa wa kokarin gwamnati na inganta zaman lafiya.

Haka kuma, ya ce hakan na taimakawa wajen tabbatar da kyawawan dabi’u da yaki da munanan halaye da ke addabar al’umma.

Gwamnan ya ce matakin Shehu Baba na yin horo tare da jami’an Hisbah ya nuna cewa jagoranci ba wai bayar da umarni kadai ba ne.

Jami’an Hisbah da suka halarci horon sun fito ne daga dukkan kananan hukumomi 27 da ke fadin Jigawa.

Gwamnatin Jigawa ta shirya horon ne domin karfafa kwarewa, dabaru, da’a da ilimin jami’an Hisbah wajen yaki da munanan halaye.

Haka kuma, horon na da manufar inganta kokarin jami’an wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro a fadin jihar.

Kara karanta wannan

Sarkin Zazzau ya ji dadin kokarin Uba Sani, ya fadi wahalar da sarakuna ke ciki

An karawa jami'an Hisbah albashi a Jigawa
Taswirar jihar Jigawa da aka gudanar da atisayen hukumar Hisbah. Hoto: Legit.
Source: Original

An karawa jami'an Hisbah alawus

A wani bangare na sauye-sauyen, gwamnati ta kara mafi karancin alawus din jami’an Hisbah daga N6,000 zuwa N25,000 a kowane wata.

Gwamnatin ta kuma samar da motocin Toyota Hilux guda 27, inda aka ware mota daya ga kowace karamar hukuma domin ayyukan sintiri.

Mataimakin Gwamna Aminu Usman ya ce gwamnati za ta ci gaba da zuba jari wajen horaswa, kayan aiki da inganta jin dadin jami’an Hisbah.

Ya ce hakan zai taimaka wa hukumar Hisbah wajen gudanar da nauyin da aka dora mata yadda ya kamata a fadin jihar.

Usman ya ce ya kamata ayyukan jami’an su taimaka wajen tabbatar da zaman lafiya, hadin kai, kyawawan dabi’u da zaman tare tsakanin al’umma.

Ya kuma jaddada cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da tallafa wa gyare-gyaren da za su kara kwarewa da ingancin hukumar Hisbah.

Bayan kammala horon, Shugaban Karamar Hukumar Birniwa, Shehu Baba, ya ce ya shiga horon ne bisa radin kansa domin bayar da gudummawa.

Kara karanta wannan

Uba Sani ya dauko hanyar gyara, ya nada kwamishinoni 3 da hadimai 45

Ya ce manufarsa ita ce taimakawa wajen yaki da munanan halaye da kuma samar da al’ummomin da za su zauna cikin zaman lafiya, cewar Vanguard.

Har ila yau, ya bayyana cewa matakin nasa na kuma da nufin zama abin koyi da karfafa gwiwar jami’an Hisbah a Birniwa da sauran sassan Jigawa.

Ya ce:

“Na yi farin cikin kasancewa cikin wannan horo da kuma bayar da gudummawata a matakin kasa. Hisbah jakadu ne na kyawawan dabi’u.”
“Ta hanyar shiga tare da su, ina son karfafa musu gwiwa da kuma zaburar da sauran ‘yan kasa su shiga ayyukan ci gaban al’umma.”

Hisbah ta musanta hana Kiristoci ibadah

A baya, an ji cewa Hukumar Hisbah ta yi magana kan zargin hana Kiristoci gudanar da ibadarsu, wanda ya jawo maganganu a jihar.

Kwamandan hukumar, Dakta Usman Abdullahi Jatau, ya ce dokar kafa Hisbah ta shafi Musulmi ne kawai, ba ta da ikon tsara addinin Kirista.

Jatau ya bukaci jama’a su yi watsi da bayanan da ba su da tushe, domin kauce wa rikicin addini tare da tabbatar da zaman lafiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.