Shigo da Makamai: Matashi Dan Sokoto Ya Kawo Fasahar Dakile Matsalar a Iyakoki

Shigo da Makamai: Matashi Dan Sokoto Ya Kawo Fasahar Dakile Matsalar a Iyakoki

  • Wani matashi daga Sokoto ya kirkiri fasahar zamani mai suna ‘Smart Border and Toll Gate Security System’ domin inganta tsaro
  • Matashin ya ce fasahar za ta taimaka wajen sa ido kan iyakoki, tare da amfani da jirage marasa matuka wajen dakile masu safarar makamai
  • Matashin ya bukaci gwamnati ta inganta kirkire-kirkire da hadin gwiwar jama’a da jami’an tsaro na da muhimmanci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Sokoto – Wani matashi daga jihar Sokoto ya bajinta ta gaske bayan kirkirar wata fasahar zamani domin dakile matsalar tsaro musamman a Arewa.

Haruna Abubakar Jibril da ke da kwarewa a fannin fasaha da kwamfuta ya bayyana dalilin kirkirar fasahar domin taimakawa hukumomin Najeriya.

Matashi ya kirkiri fasahar magance matsalar tsaro
Wani matashi Haruna Abubakar Jibril da ya kirkiri fasahar zamani. Hoto: @harun_sokoto.
Source: Instagram

Matashin ya bayyana haka ne yayin zantawa da wakilin Legit Hausa a yau Asabar 12 ga watan Satumbar shekarar 2026 da muke ciki.

Kara karanta wannan

'Ni na ci zaɓe a 2023': Kalaman Obi da suka dugunzuma fadar shugaban ƙasa

Matashi ya kawo fasahar dakile matsalar tsaro

Ya ce ya dade yana da sha’awar kirkire da amfani da fasaha wurin magance matsalolin da suka fi shafar al’umma musamman na tsaro.

Haruna ya ce ya kirkiri wani tsari da ake kira ‘Smart Border and Toll Gate Security System’ domin amfani da ita inganta tsaro musamman a iyakoin jihohi da kasashe.

Ya ce:

“Ina da sha’awar kirkire-kirkire da amfani da fasaha wajen magance matsalolin tsaro, yanzu kirkiri wani tsari wanda manufarsa ita ce amfani da fasaha wajen kara inganta tsaro a kan iyakokin jihohi da kasashe .
“Sannan Akwai wasu jirage marasa matuka da mutum-mutumi da nake so in yi wadanda za su taimaka wajen dakile yan ta’addan da ke shigo da makamai masu hatsari ta cikin daji da sararin samaniyar mu
“Sannan akwai wani wanda zai taimaka mana wurin maganche hadura na Ababen hawa ta hanyar cin mutane tara kai tsaye idan yana gudu sosai ko yana amfani da wayar sa yayin da yake tuki.”

Kara karanta wannan

'Abin da tsofaffin shugabanni ke tsoro Tinubu ya aiwatar saboda tausayin 'yan kasa'

Matashin ya ce babu wani tallafi da ya samu daga gwamnati ko wata hukuma inda ya ke fatan hukumomi da masu ruwa da tsaki su fahinci muhimmancin fasaha domin hadin guiwa da inganta ta.

Har ila yau, Haruna ya ba hukumomi shawara su mayar da hankali wurin amfani da fasahar zamani wurin tattara bayanai, sa ido domin gano laifuffuka tare da yada bayanai a tsakanin hukumomin tsaro.

“Kira na ga hukumomi shi ne su kara ba matasa masu kirkire-kirkire dama, akwai matasa da suke da tunane-tunane da fasahohin da za su iya taimaka wajen magance matsalolin da muke fuskanta,
“Kiran da zan yi ga jama’a shi ne su hada kai da hukumomin tsaro, su rika bayar da sahihan bayanai, kuma su guji duk wani abu da zai kara tabarbarewar tsaro.
“A gani na, tsaro ba aikin gwamnati kadai ba ne, aikinmu ne baki daya, idan gwamnati, jami’an tsaro, matasa da sauran jama’a suka hada kai, ilimi da fasaha da kyakkyawan shugabanci, za mu iya samun sauki sosai wajen magance matsalar rashin tsaro.”

- Cewar matashin

Gwamnati za ta samar da ayyuka miliyan 1

An ji cewa Gwamnatin Tarayya ta sanya burin samar da ayyukan yi ga ’yan Najeriya da za a danganta da fitar da ayyuka zuwa ketare.

Kara karanta wannan

An shirya samar da kotu, gwamna zai kama yara a titi da ba su zuwa makaranta

An ƙaddamar da shirin domin haɗa ƙwararrun ’yan Najeriya da kamfanoni da ma’aikata na ƙasashen duniya, ba tare da ƙaura daga Najeriya ba.

Gwamnati ta ce sama da ’yan Najeriya 200,000 na samun horo a cibiyoyin ƙwarewa 1,200, yayin da ake shirin kafa makarantar fasahar zamani.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.