Yadda Abba Kabir Ya Ba 'Yan APC Miliyoyi da Filaye Sama da 1,500 a Kano
- Gwamna Abba Kabir Yusuf ya raba filaye 1,540 da Naira miliyan 100 ga kungiyar 'yan dangwale ta APC a Kano don karfafa jam'iyya kafin zaben 2027
- Bayan ya kaddamar da kungiyar, ya ce su ne ginshikin nasarar APC a zaben da ke tafe, hade da cin nasarar shugaba Bola Tinubu a wa'adi na biyu
- Mai ba gwamna shawara kan lamuran siyasa Mustapha Hamza Bakwana ya ce suna da karfin kawo kuri'u miliyan 1 ga Bola Tinubu a Kano
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Kano - Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya raba filaye 1,540 tare da bayar da tallafin kudi Naira miliyan 100 ga shugabannin kungiyar masu goyon bayan APC a rumfunan zabe, wadanda ake kiransu da 'yan dangwale.
Gwamna ya yi wannan bayarwa ne a lokacin da aka yi bikin kaddamar da kungiyar. A wajen bikin, ya bayyana cewa tsarin rumfunan zabe shi ne ginshiki da APC ke dogaro da shi wajen cin nasara.

Source: Facebook
Mai magana da yawun gwamnan Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa ne ya sanar da wannan a wata sanarwa da ya fitar a Facebook a ranar Laraba, 15 ga Yuli 2026.
Dalilin raba miliyoyi a Kano
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya nuna cewa dalilin wannan taimako shi ne don baiwa mambobbin kungiyar karfin gudanar da ayyukan jam'iyya yadda ya kamata a matakin rumfuna.
Ya kara da cewa, karfafa masu goyon bayan APC zai taimaka wajen tabbatar da sake nasarar shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaben 2027, da kuma sauran 'yan takarar APC.
A cewarsa, sake zabar Tinubu zai ba da damar ci gaba da ayyukan gyaran tattalin arziki da tsare-tsaren raya kasa da gwamnatin tarayya ke gudanarwa a fadin kasar.
Yadda za a taimaki APC a 2027
Mai ba gwamna shawara kan harkokin siyasa, Mustapha Hamza Buhari Bakwana, ya yi bayani cewa wannan taimako kashi na farko ne kawai na wani tsari mai fadi da aka shirya domin karfafa goyon bayan APC.
Ya nuna cewa kungiyar 'yan dangwale tana da karfin tattara kuri'u fiye da miliyan 1 ga shugaba Tinubu a jihar Kano.
Bikin ya hada shugabannin jam'iyya da masu ruwa da tsaki a harkokin siyasa, da kuma wakilan da suka zo daga dukkanin karamar hukumomi 44 na jihar.
Rabon da gwamnan ya yi ya ja hankalin jama'a, inda wasu suka ce bai dace ba, domin shi gwamnan kowa ne a Kano, amma ya ware 'yan APC kawai yana ba su kudin jama'a.

Source: Facebook
APC na zawarcin Sanata Hanga
A wani labarin, mun kawo muku cewa gwamnatin Kano karkashin Abba Kabir Yusuf ta fara zawarcin Sanata Rufai Hanga na jam'iyyar NDC.
Rahotanni sun nuna cewa jiga-jigan APC sun kai wa Hanga ziyara, inda suka bayyana cewa Rabiu Musa Kwankwaso bai kyauta masa ba.
Bayan doguwar tattaunawa, APC ta bayyana cewa za ta yi maraba da sanatan idan ya sauya sheka, kuma za ta girmama shi.
Asali: Legit.ng

