Gwamna Inuwa zai Dauki Ma'aikata a Gombe ana Saura Wata 8 Ya Sauka

Gwamna Inuwa zai Dauki Ma'aikata a Gombe ana Saura Wata 8 Ya Sauka

  • Gwamna Inuwa Yahaya na Gombe ya rantsar da sababbin sakatarorin gwamnati 19, mafi yawan adadin da aka taɓa naɗawa a lokaci guda a tarihin jihar
  • Sababbin naɗe-naɗen sun kai adadin manyan sakatarorin da gwamnatin Inuwa Yahaya ta naɗa zuwa 55 cikin shekaru bakwai da rabi
  • Gwamnan ya kuma bayyana shirin ɗaukar sababbin ma’aikatan gwamnati bayan kammala tantance ma’aikata ta na’urar tantance bayanai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Gombe – Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya rantsar da sababbin manyan sakatarorin gwamnati 19 a jihar.

A bayanin da ya yi, gwamnan ya ce naɗe-naɗen wani ɓangare ne na ƙoƙarin ƙarfafa ma’aikatan gwamnati da inganta ayyuka a jihar.

Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya
Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya. Hoto: Ismaila Uba Misilli
Source: Twitter

An naɗa sakatarorin gwamnati

Ismaila Uba Misilli ya wallafa a Facebook cewa gwamnan ya ce sababbin naɗe-naɗen sun kawo adadin manyan sakatarorin da gwamnatinsa ta naɗa zuwa 55 cikin shekara bakwai da rabi.

Kara karanta wannan

Zance ya kare: Sanata Yari ya fadi abu 1 da za a tallata Tinubu da shi a Najeriya

Ya ƙara da cewa an kuma ɗaga daraktoci sama da 100 zuwa manyan mukamai a tsarin ma’aikatan gwamnatin jihar.

Inuwa Yahaya ya ce matakan na daga cikin ƙoƙarin cike gibin ma’aikata da kuma samar da ƙwararrun ma’aikatan gwamnati da za su ci gaba da gudanar da ayyukan ci gaba bayan wa’adin gwamnatinsa.

Za a ɗauki ma’aikata a Gombe

Gwamnan ya bayyana cewa gwamnatinsa na shirin gudanar da gagarumin ɗaukar sababbin ma’aikatan gwamnati bayan kafa ingantaccen kundin bayanan ma’aikata ta hanyar tsarin tantance bayanai.

Ya ce ya umurci Shugaban Ma’aikatan Gwamnati ya haɗa kai da Hukumar Ma’aikatan Gwamnatin Jiha domin gudanar da cikakken bincike kan buƙatun ma’aikata a ma’aikatu da hukumomin gwamnati.

A cewarsa, hakan zai taimaka wajen gano gibin ma’aikata da adadin mutanen da ake buƙata kafin ɗaukar sababbin ma’aikata.

Ya ce ana sa ran sabon ɗaukar ma’aikatan zai gudana kafin karewar wa’adin gwamnatinsa a ranar 29 ga Mayu 2027.

Kara karanta wannan

Kiristan da ya yi aiki da El Rufa'i ya fadi me ya faru a Kudancin Kaduna

Taswirar jihar Gombe
Taswirar jihar Gombe. Legit
Source: Original

Batun tantance ma’aikata

Inuwa Yahaya ya ce tsarin tantance ma’aikata da na’urar bayanan halittu, wanda ya fuskanci suka lokacin da aka ƙaddamar da shi, ya taimaka wajen samar da sahihan bayanai kan ma’aikatan jihar.

Ya ce tsarin ya taimaka wajen gano ma’aikatan bogi da rage yawan rashin zuwa aiki, tare da ceto wa jihar biliyoyin Naira.

Gwamnan ya ce bayanan da aka samu sun samar da damar ɗaukar ma’aikata bisa ainihin buƙatun ma’aikatu da hukumomin gwamnati.

Za a ba dalibai kyautar data

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnatin tarayya ta sanar da cire kuɗin data ga miliyoyin ɗaliban Najeriya da ke amfani da wasu shafukan ilimi na yanar gizo da aka amince da su.

Ministan Ilimi, Dr Tunji Alausa, ya bayyana hakan yayin ƙaddamar da shirin samar da damar amfani da shafukan ilimi da bayanan karatu ba tare da biyan kuɗin data ba.

Alausa ya ce shirin na da nufin rage matsalar tsadar amfani da intanet, domin kuɗin data kada ya zama abin da ke hana yara da ɗalibai samun damar ilimi mai inganci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng