Da Ɗumi-Ɗumi: Matar tsohon Shugaban Ƙasar Nigeria na mulkin Soja, Aguiyi Ironsi, ta rasu

Da Ɗumi-Ɗumi: Matar tsohon Shugaban Ƙasar Nigeria na mulkin Soja, Aguiyi Ironsi, ta rasu

  • Allah ya yi wa Victoria, matar tsohon shugaban kasan Nigeria na soji, Aguiyi-Ironsi rasuwa
  • Victoria Aguiyi-Ironsi ta rasu ne a ranar Litinin tana da shekaru 97 a duniya
  • Marigayi Manja Janar Johnson Aguiyi-Ironsi ya shugabanci Nigeria tsawon wata shida kafin a masa juyin mulki a 1966

Victoria Aguiyi-Ironsi, matar marigayi tsohon shugaban kasan mulkin soji na Nigeria, Manjo Janar Johnson Aguiyi-Ironsi, ta mutu, The Guardian ta ruwaito.

Tsohuwar first lady din ta rasu ne a ranar Litinin tana da shekaru 97 a duniya.

Da Ɗumi-Ɗumi: Matar tsohon Shugaban Ƙasar Nigeria na mulkin Soja, Aguiyi Ironsi, ta rasu
Victoria Aguiyi Ironsi, matar tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Janar Johnson Aguiyi Ironsi. Hoto: The Guardian
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Za ta cika shekaru 98 a ranar 21 ga watan Nuwamban 2021.

Kara karanta wannan

Allah ya yi wa tsohon ɗan jarida, Tankon Sa'i, rasuwa a Kaduna

Mijin Victoria Aguiyi-Ironsi shine babban kwamandan gwamnatin sojin Nigeria na tsawon watanni shida kafin a hambarar da shi tare da kashe shi a juyin mulkin ramuwa ta shekarar 1966.

A halin yanzu ba a bayyana abin da ya yi sanadin rasuwar Victoria ba.

A cewar The Nation, Victoria wacce ta rasu a ranar Litinin ba ta sake yin aure ba tun bayan mutuwar mijinta.

Allah ya yi wa tsohon ɗan jarida, Tankon Sa'i, rasuwa a Kaduna

A wani labarin daban, kun ji cewa tsohon kwararren dan jarida mazaunin Kaduna, Muhammadu Dan Tankon Sa'i ya riga mu gidan gaskiya kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Tankon Sa'i ya rasu ne a ranar Lahadi 22 ga watan Agusta bayan fama da gajeruwa rashin lafiya.

Wani daga cikin iyalansa da ya sanar da rasuwarsa, ya bayyana marigayin a matsayin tsohon dan jarida, wanda ya kayyatar da nishadantar da masu sauraren rediyo da shirye-shiryensa na labaran Hausa da wasu shirye-shiryen tun daga shekarun 1960s.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Tsohon gwamnan Oyo na mulkin soja, Tunji Olurin ya mutu

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164