Yadda ranar 15 ga watan Junairun 1966 da 1970 suka canza tarihi har abada
A rana irin ta yau ne a shekarar 1966, aka yi juyin-mulkin farko a Najeriya, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar shugabannin da ke mulki a wancan lokaci.
A wannan rana wasu sojoji masu dumin-kirji, wanda kusan dukkanninsu sun fito ne daga kabilar Ibo ne, suka hambarar da gwamnatin Abubakar Tafawa-Balewa.
Wadanda suka jagoranci wannan danyen aikin kashe Firayim Minista da Firimiyoyin larduna su ne: Chukwuma Kaduna Nzeogwu da Emmanuel Ifeajuna.
Sai kuma Timothy Onwuatuegwu, Chris Anuforo, Don Okafor, Humphrey Chukwuka, da Adewale Ademoyega.
Ko da sojojn tawayen sun kashe manyan sojoji da ‘yan sanda da kuma shugabannin gwamnati, amma hakarsu ba ta cinma ruwa na darewa kan mulki ba.
Janar Johnson Aguiyi-Ironsi ya ga bayan wannan juyin-mulki, kuma ya hau kan kujerar shugaban kasa na mulkin soja, wanda shi ne karon farko a tarihi.
KU KARANTA: Takaitaccen tarihin mutuwar shahadar Ahmadu Bello a 1966
Lamarin ya yi sanadiyyar mutuwar Janar JTU Aguiyi-Ironsi, inda sojojin Arewa suka shirya ramuwar gayya, su ka zargi gwamnati da kin hukunta masu laifi.
Wannan ne ya jawo kisan Inyamurai a Najeriya, a karshe gwamna Emeke Ojukwu ya jagoranci kabilar ta barke daga Najeriya, ta kafa kasar Biyafara mai ‘yancin kanta.
Bayan shekaru uku ana gwabza yaki tsakanin 1967 zuwa 1970, Ojukwu ya tsere, sojojin Biyafara suka sallama a rana mai kamar ta yau - 15 ga watan Junairu, 1970.
Ga jerin wasu daga cikin wadanda aka kashe a juyin mulkin kamar yadda Wikipedia ya kawo:
KU KARANTA: Kisan Sardauna, Tafawa Balewa, da abubuwan da suka faru a 1966
Firayim Minista, Abubakar Tafawa Balewa
Firimiyan Arewa, Ahmadu Bello da Mai dakinsa, Hafsatu
Firimiyan Yamma, Samuel Ladoke Akintola
Ministan kudi, Festus Okotie-Eboh
Latifat Ademulegun
Dogari, Zarumi Sardauna
Ahmed Pategi (Direba)
Jami’an tsaron da aka kashe sun hada da:
Birgediya Samuel Ademulegun
Birgediya Zakariya Maimalari
Kanal Ralph Shodeinde
Kanal Kur Mohammed
Laftanan Kanal Abogo Largema
Laftanan Kanal James Pam
Laftanan Kanal Arthur Unegbe
Sannan akwai Sajan Daramola Oyegoke, PC Yohana Garkawa, Lans Kofur, Musa Nimzo, PC Akpan Anduka, PC Hagai Lai da Philip Lewande.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng