Magana Ta Kare, Tsohon Gwamna Ya Zama Sarki Mai Martaba a Najeriya
- An nada tsohon gwamnan Oyo, Rashidi Adewolu Ladoja a matsayin Sarkin Ibadan na 44 a hukumance yau Juma'a, 26 ga watan Satumba, 2025
- Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar na III na cikin manyan bakin da suka halarci bikin nadin a Ibadan
- Rahotanni sun nuna cewa nan ba da dadewa ba Gwamna Seyi Makinde zai mika wa Sarkin sandar mulki yayin da ake dakon isowar Shugaba Tinubu
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Osun - Tsohon Gwamnan jihar Oyo kuma tsohon Sanata, Rashidi Adewolu Ladoja (Arusa na 1) ya zama Olubadan na 44 a tarihin masarautar Ibadanland.
An tabbatar da nadin sabon Sarkin a hukumance ne a bikin da ke gudana yanzu haka a jihar Oyo da ke Kudancin Najeriya.

Source: Facebook
Daily Trust ta ruwaito cewa Ladoja ya isa Mapo Hall, wurin da aka shirya bikin sanye da farin rawani na sarauta wanda aka ba shi a Haikalin Ose Meji da ke karamar hukumar Ibadan ta Kudu maso Gabas.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Makinde zai mika sandar mulki
Kafin hakan, ya karɓi ganyen gargajiya na Akoko a gidan Labosinde da ke Oja’ba a Ibadan duk a yau Juma'a, 26 ga watan Satumba, 2025.
Gwamna Seyi Makinde ya mika sandar mulki ga sabon Sarkin Ibadan, Oba Ladoja, wanda ya kara tabbatar da nadinsa a matsayin Olubadan na 44.
Shugaban ƙasa Bola Tinubu wanda ake sa ran zai halarci taron tare da gwamnan, bai isa wurin ba kawo yanzu da muke hada maku wannan rahoto.
Tsohon gwamna ya gaji sarautar Olubadan
Oba Ladoja ya gaji marigayi Oba Owolabi Olakulehin, Olubadan na 43, wanda ya rasu ranar 7 ga Yuli, 2025, bayan shekara guda a kan karaga.
Sabon Sarkin na Ibadan ya hau gadon sarauta a yau, ranar Juma’a, kusan watanni uku bayan rasuwar Oba Olakulehin, in ji rahoton Punch.
Bikin nadin ya samu halartar tsofaffin gwamnoni, manyan sarakuna, sanatoci, mambobin majalisar wakilai da kuma yan majalisar dokoki na jihohi daga sassan ƙasar nan.
Sarkin Musulmi da manyan mahalarta nadin
Cikin manyan sarakunan da suka halarta akwai Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar III da Alaafin na Oyo, Oba Akeem Owoade.
Sai kuma Soun na Ogbomosho, Oba Ghandi Adeoye, Oluwo na Iwo, Oba Abdulrasheed Adewale da kuma Olugbo na masarautar Ugbo, Oba Fredrick Obateru Akinruntan.
Ooni na Ife, Oba Enitan Adeyeye Ogunwusi, bai samu halarta ba saboda wasu dalilai amma ya samu wakilcin ɗaya daga cikin matansa, Olori Ashley.

Source: Facebook
Haka kuma, tsoffin gwamnoni sun halarta, ciki har da Otunba Gbenga Daniel da Sanata Ibikunle Amosun, Rabiu Kwankwaso (Kano), Olagunsoye (Osun) da Kayode Fayemi (Ekiti).
Sarkin Musulmi ya taya Ladoja murna
A wani rahoton, kun ji cewa Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa'ad Abubakar ya taya sabon Olubadan, Rashidi Ladoja murna.
Sultan ya yaba da nadin Alhaji Rashidi Adewolu Ladoja, a matsayin Olubadan na 44 na Ibadanland da ke jihar Oyo.
Sarkin Musulmi ya kuma jinjina wa Gwamnan Jihar Oyo, Injiniya Seyi Makinde, bisa bin muradun jama’a wajen tabbatar da sabon Olubadan na Ibadanland.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

