"Ba Musulmai ba ne"; Babban Basarake Ya Fusata kan Danganta 'Yan Bindiga da Musulunci

"Ba Musulmai ba ne"; Babban Basarake Ya Fusata kan Danganta 'Yan Bindiga da Musulunci

  • Sarkin Iwo, Oba Abdulrosheed Akanbi, ya ce bai dace a rika bayyana 'yan bindiga a matsayin Musulmi ba
  • Ya bayyana cewa 'yan bindiga ba sa gudanar da ibadar Musulunci kuma ba su da siffofin da ke nuna su Musulmi ne
  • Sarkin ya bukaci 'yan Najeriya su daina danganta ta'addanci da Musulunci, tare da neman gwamnati ta dauki mataki kan masu yada kalaman batanci a shafukan sada zumunta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Osun – Sarkin Iwo da ke jihar Osun, Oba Abdulrosheed Akanbi, ya yi Allah wadai da yadda ake danganta 'yan bindiga da addinin Musulunci.

Oba Abdulrosheed Akanbi ya bayyana cewa bai kamata a alakanta masu aikata laifuffuka da wani addini ba.

Oluwo na Iwo ya koka kan 'yan bindiga
Oluwo na Iwo, Oba Abdulrosheed Akanbi Hoto: Emperor Abdulrasheed Adewale Akanbi Telu 1
Source: Facebook

A cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labaransa, Ibrahim Alli, ya fitar a ranar Asabar, 11 ga watan Yulin 2026.

Kara karanta wannan

Ministan Tsaro: Abin da ya hana sojoji gwabza wa da ƴan bindiga don ceto ɗaliban Oyo

Babban basaraken ya bayyana cewa 'yan bindiga ba su da siffofin da za su sa a kira su Musulmai.

Ya bayyana cewa sanya rawani ko kuma amfani da sunan Larabci ba ya tabbatar da cewa mutum mabiyin addinin Musulunci ne.

"Yan bindiga ba sa gudanar da ibadar Musulunci"

Oba Akanbi ya ce 'yan bindiga ba sa gudanar da sallolin farilla, kuma ba sa nuna halayen da ake sa ran Musulmi ya kasance da su.

Ya ce:

"Ina yin Allah wadai da danganta 'yan bindiga da addinin Musulunci. Musulmi na gaskiya ba 'yan bindiga ba ne. Ba za ka ga masallaci a maboyar 'yan bindiga ba. Haka kuma makiyaya ba su da masallatai a matsugunansu. Ba su da wata alamar da ke nuna su Musulmai ne."

Rawani da Larabci ba hujjar Musulunci ba ne

Sarkin ya kara da cewa sanya rawani ba Musulmai kadai ke yi ba, yana mai bayanin cewa mutane da dama da ba Musulmai ba a yankunan hamada ma suna sanya rawani.

Haka kuma ya yi watsi da ikirarin cewa amfani da harshen Larabci da wasu 'yan bindiga ke yi yana nuna cewa Musulmai ne.

Kara karanta wannan

Sarkin Musulmi ya kausasa murya kan 'yan bindiga, ya ce a hada kai a yake su

A cewarsa:

"'Yan bindiga ba su da addini. Shin ka taba ganin inda suke gudanar da sallah? Ko da suna sanya rawani, ba Musulmai kadai ke sanya rawani ba. Akwai mutanen hamada da ba Musulmai ba da suke sanya rawani."
"Coci da dama a kasashen Larabawa suna amfani da harshen Larabci wajen wa'azi. Haka kuma akwai mutane masu bin wasu addinai a kasashen da Musulmai suka fi yawa, amma suna magana da Larabci."
Oluwo na Iwo ya ce a daina hada yan bindiga da Musulunci
Oluwo na Iwo, Oba Abdulrosheed Akanbi a wajen wani taro Hoto: Emperor Abdulrasheed Adewale Akanbi Telu 1
Source: Facebook

Ya bukaci a daina danganta ta'addanci da Musulunci

Oba Akanbi ya bayyana cewa ci gaba da alakanta ayyukan 'yan bindiga da addinin Musulunci ba adalci ba ne.

Ya ce matsalar ta samo asali ne daga gazawar wasu gwamnatocin baya wajen magance matsalolin tsaro, ba daga addini ba.

Sarkin ya bukaci 'yan Najeriya su daina danganta ta'addanci da Musulunci, sannan ya roki gwamnati ta dauki matakan doka kan masu sharhi a shafukan sada zumunta da ya ce suna amfani da kafafen intanet wajen bata sunan Musulmai.

Kara karanta wannan

Ma'aikatar bogi: Kujerun manyan jami'an Tinubu na rawa, ana kira a kore su

'Yan bindiga sun sace gawa

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu masu garkuwa da mutane sun kai hari kan motar da ke dauke da gawar tsohon mataimakin kamandan hukumar FRSC, Augustine O. Ikwue.

'Yan bindigan dauke da makamai sun sace gawar da kuma mutanen da ke rakiyar ta zuwa garinsu na Otukpo da ke jihar Benue.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng