Abu Ya Yi Muni: Mutanen Gari Sun Gigice da Wani Bam Ya Tashi a Jihar Neja

Abu Ya Yi Muni: Mutanen Gari Sun Gigice da Wani Bam Ya Tashi a Jihar Neja

  • Kyaftin da sojoji biyu sun rasa rayukansu bayan motarsu ta taka wani bam da ake zargin an dasa a kan titi a Borgu ta jihar Neja
  • Wasu sojoji biyu sun jikkata sakamakon fashewar bam ɗin, wanda ake zargin 'yan ta'adda ne suka birne shi a kan hanyar da sojojin ke bi
  • Har yanzu rundunar soji ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance ba amma mazauna yankin sun tabbatar da aukuwar lamarin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Niger, Nigeria - Wani bam da aka birne a kan titi ya tashi da motar dakarun sojojin Najeriya a yankin karamar hukumar Borgu ta jihar Neja.

Rahotanni sun nuna cewa kyaftin da sojoji biyu sun mutu sakamakon fashewar bam din da aka birne a ƙasa a ƙauyen Maciyan-Kyada da ke gundumar Babanna a karamar hukumar Borgu.

Kara karanta wannan

Kaduna ta ɗauki zafi, mutanen gari sun sake kama mutum 2 sun masu kisan gilla

Sojoji.
Dakarun rundunar sojojin Najeriya suna aikin sintiri don tabbatar da tsaro Hoto: @NigerianArmy
Source: Twitter

Motar sojoji ta taka bam a Neja

Wata majiya ta tsaro ta shaida wa jaridar Daily Trust cewa wasu sojoji biyu sun samu munanan raunuka sakamakon fashewar bam din, wanda ya jefa mutanen yankin cikin zullumi.

A cewarta, sojojin sun bar garin Babanna da misalin ƙarfe 10:00 na safe a ranar Talata, 7 ga Yulin 2026, domin gudanar da sintiri na yau da kullum.

Majiyar ta bayyana cewa bayan dakarun sojojin sun tafi wannan sintiri ne ɗaya daga cikin motocinsu ta taka bam ɗin da ake zargin 'yan ta'adda sun birne a kan hanya.

Majiyar ta ce:

"Fashewar bam ɗin ta rutsa da sojoji ne yayin da suke sintiri. Motar da suke ciki ta taka bam da 'yan ta'adda suka birne a kan hanya.
"Sojoji uku sun mutu, ciki har da wani Kyaftin na rundunar sojoji, yayin da wasu biyu suka jikkata. Lamarin ya faru ne a wani ƙauye da ke ƙarƙashin gundumar Babanna."

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda na barazana a iyakokin Najeriya, sojoji sun shirya murkushe su

Fashewar ta ƙara tada hankulan al'umma

Wani mazaunin yankin da ya tabbatar da faruwar lamarin, ya bayyana sunan ɗaya daga cikin sojojin da suka mutu da Yusuf Kabir.

Ya ce wannan hari ya ƙara tayar da hankalin mazauna yankin, waɗanda ke ci gaba da fuskantar matsalolin tsaro sakamakon hare-haren 'yan bindiga da garkuwa da mutane.

Niger.
Taswirar jihar Neja da ke Arewa ta Tsakiya a Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, rundunar sojin Najeriya ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance kan lamarin ba.

Haka zalika, babu sanarwa daga rundunar yan sanda ko gwamnatin jihar Neja kan wanan hari na bam da ya rutsa da dakarun sojoji a yankin karamar hukumar Borgu.

Bam ya tashi da motar yan sanda a Zamfara

A wani rahoton, kun ji cewa jami’an rundunar ’yan sanda uku sun rasa rayukansu yayin da motarsu ta taka bam kuma ya tashi da su a jihar Zamfara.

Mai taimaka wa Gwamnan jihar Zamfara kan harkokin yada labarai, Mugira Yusuf, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar.

A cewar sanarwar, jami’an suna gudanar da sintiri ne a hanyar Anka zuwa Bagega domin dakile ayyukan kungiyoyin yan bindiga lokacin da hatsarin ya afku.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262