'Yan bindiga sun kai hari GSC Kagara a Niger, sun kashe dalibi daya sun sace wasu

'Yan bindiga sun kai hari GSC Kagara a Niger, sun kashe dalibi daya sun sace wasu

- Yan bindiga sun afka Kwallejin Kimiyya ta Gwamnati da ke Kagara a jihar Niger

- Yan bindigan sun halaka dalibi guda daya sannan sun raunta wasu da dama

- Har wa yau sun sace dalibai da kuma wasu daga cikin ma'aikatan kwallejin sun yi awon gaba da su

A kalla dalibi daya ne ya riga mu gidan gaskiya yayin da an kuma sace wasu da dama, Channels Television ta ruwaito.

An ruwaito cewa an sace wasu malaman kwallejin da iyalansu da ke zaune a rukunin gidajen ma'aikatan kwallejin.

Wani majiyar gwamnati da ya nemi a sakayya sunansa ne ya sanar wa Channels Television hakan ta wayar tarho a daren ranar Laraba.

DUBA WANNAN: An fara bincikar jami'in Hisbah da aka kama da matar aure a ɗakin Otel a Kano

'Yan bindiga sun kai hari kwalejin gwamnati a Niger, sun kashe dalibi daya sun sace wasu
'Yan bindiga sun kai hari kwalejin gwamnati a Niger, sun kashe dalibi daya sun sace wasu. Hoto: @ChannelsTV
Asali: Twitter

A cewar majiyar, maharan sun afka Kwallejin kimiyya da Gwamnati da ke Kagaran ne misalin karfe 2 na daren ranar Laraba suka fara harbe-harbe.

A sakamakon harbin ne suka halaka dalibi daya sannan wasu da dama suka jikkata.

Sai dai majiyar bai iya tantance adadin mutanen da aka sace ba ko kuma wadanda suka samu rauni a lokacin hada wannan rahoton.

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Ƴan Boko Haram sun ƙona gidaje fiye da 140 a ƙauyukan Borno, sun sace dabobi da kayan abinci

Majiyar ya kara da cewa wasu daga cikin yan bindigan sun saka kaya irin ta daliban makarantar domin kada a gane cewa su ba yan makarantar bane.

Wannan harin na zuwa ne kwanaki kadan bayan wasu yan bindigan sun kai wa wata motar fasinjoji hari a kan hanyar MInna zuwa Zungeru inda suka sace fasinjoji 21.

Amma daga bisani an ceto wasu daga cikin fasinjojin.

A wani labarin, kun ji cewa Sanata Iyiola Omisore, tsohon mataimakin gwamnan jihar Osun, daga karshe ya koma jam'iyyar All Progressives Congress (APC).

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa Omisore, a ranar Litinin, 15 ga watan Fabarairu ya ziyarci mazabarsa ta 6, Moore, a Ile-Ife, a tare da tawagar mataimakin gwamna, Benedict Alabi, domin ya karbi katinsa na APC.

Omisore ya yi takarar kujerar gwamna a shekarar 2018 a karkashin inuwar jam'iyyar Social Democratic Party (SDP).

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe tsawon shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Online view pixel