Yan sanda sun ce sun kashe kasurgumin dan bindiga a Niger
- Ƴan sandan jihar Niger sun ce sunyi nasarar kashe ƙasurgumin ɗan bindiga, Zokala
- Rundunar tace jami'anta tare da yan banga ne suka yi nasarar ritsa shi suka halaka shi
- Rundunar tace tana farautar sauran ƴan tawagar Zokala domin su fuskanci hukunci
A ranar Talata, tawagar haɗin gwiwa na yan sanda da yan banga sun kashe ƙasurgumin ɗan bindiga a Rafin-Gora mai suna Zokala.
Kakakin ƴan sandan jihar, Wasiu Abiodun ne ya sanar da hakan a ranar Laraba, Premium Times ta ruwaito.
A cewarsa, an ritsa Zokala ne yayin da ya ke ƙoƙarin kaucewa jami'an tsaro a kan babur ɗinsa.
"Ɗan bindigan yana samun mafaka ne a dajin Kontagora kuma ya daɗe yana adabar garuruwan Beri, Lamba, Kamfanin-waya, Farin-shige, bukoki da kewaye."
DUBA WANNAN: Dakatar da ni da jam'iyya ta yi ya saba doka, tsohon mataimakin shugaban APC, Eta
Ya ce ana cigaba da farautar sauran yan tawagar marigayin.
Mista Abiodun ya kuma sanar da kama wasu da ake zargin ƴan kungiyar asiri ne da aka kama dauke da sassan jikin ɗan adam.
Bayan samun sahihan bayanai, yan sandan Gwada sun kama wani Buhari Ibrahim, 35, mazaunin kauyen Daza a ƙaramar hukumar Munya ɗauke da idon ɗan adam, in ji shi.
KU KARANTA: Majalisa bata da ikon tilasta wa Buhari ya bayyana gabanta, in ji Malami
Ya ce da ake masa tambayoyi wanda ake zargin ya yi ikirarin cewa shi mai bada maganin gargajiya ne kuma wani Bitrus Imoh mazaunin Geneko ne ya bashi don ya haɗa masa magani.
A wani labarin daban, Shugaba Muhammadu Buhari ya sauke shugaban hukumar daukan ma'aikata, Dakta Nasiru Mohammed Ladan Argungu daga mukaminsa.
Sanarwar saukewar na kunshe ne cikin wata wallafa da babban mataimakin shugaban kasa a bangaren watsa labarai, Mallam Garba Shehu ya fitar a ranar Talata kamar yadda The Punch ta ruwaito.
Sanarwar ta ce Buhari ya umurci karamin ministan Kwadago da Ayyuka, Festus Keyamo, SAN, ya nada shugaban riko daga cikin manyan direktocin hukumar don maye gurbin Argungu a yanzu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng