An Kafa Sabon Kamfanin Hada Tufafi a Arewa, za a Dauki Ma'aikata 4000
- Gwamnatin jihar Kwara za ta kaddamar da masana’antar kera tufafi, wacce ke cikin manyan masana’antu a Yammacin Afirka
- Mataimaki na musamman ga Gwamnan Kwara kan harkokin sadarwa, Ibraheem Abdullateef, ne ya bayyana hakan ga al'umma
- Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, ne zai kaddamar da masana’antar, wadda ake sa ran za ta samar da ayyuka 4,000
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kwara – Gwamnatin jihar Kwara ta shirya kaddamar da sabuwar masana’antar kera tufafi ta Kwara a ranar Laraba.
Rahotanni sun nuna cewa gwamnatin ta ta sanar da cewa tana daga cikin manyan masana’antun kera tufafi a Yammacin Afirka.

Source: Facebook
Mataimaki na musamman ga Gwamnan Kwara kan harkokin sadarwa, Ibraheem Abdullateef, ne ya bayyana hakan a wani sako da ya wallafa a Facebook.

Kara karanta wannan
Tinubu na ta samun goyon baya a Arewa, manyan malaman jami'o'i 600 sun bayyana matsayarsu
Shettima zai bude kamfanin
Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, ne zai kaddamar da masana’antar da ke birnin Ilorin, babban birnin jihar Kwara.
Rahotanni sun nuna cewa masana’antar na da karfin daukar ma’aikata sama da 4,000 idan ta fara aiki da cikakken karfin ta.
A halin yanzu, sama da ma’aikata 500 ne ake da su a matakin fara gudanar da ayyukan masana’antar a hukumance.
Dalilin kafa masana’antar
Masana’antar na daga cikin ayyukan da Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq ya fara domin kara kudin shiga ga jihar da kuma samar da ayyukan yi ga mata da matasa.
Haka kuma ana sa ran aikin zai taimaka wajen hanzarta bunkasar tattalin arziki da zamantakewar al’ummar jihar Kwara.
Gwamnatin jihar na kallon masana’antar a matsayin wata hanya ta karfafa samar da ayyukan yi da kuma habaka harkokin masana’antu a jihar.
Ayyukan da masana’antar ke yi
A shafinta na intanet, masana’antar ta bayyana cewa tana samar da kayayyakin tufafi ga manyan diloli da kuma kananan 'yan kasuwa.
Ta ce an tsara ta ne a matsayin wata sana’a da za ta taimaka wajen karfafawa mata da matasa gwiwa ta hanyar amfani da ingantattun hanyoyin aiki.
Masana’antar ta ce hakan zai taimaka wajen bunkasa tattalin arzikin jihar Kwara, Najeriya da yankin Afirka da ke kudu da hamadar Sahara.

Source: Facebook
Ga wasu ayyukan masana’antar
Masana’antar ta ce tana samar da yadudduka masu inganci, tare da hada fasahar zamani da kwarewar ma’aikata wajen samar da tufafi ga abokan ciniki daban-daban.
Daga cikin ayyukan da take bayarwa akwai rina yadudduka domin samar da tufafi na musamman bisa bukatar kwastomomi.
Haka kuma tana tsara samfuran dinki da suka dace da bukatun jama'a da dai sauransu.
An bude gidan man zamani
A wani labarin, mun ruwaito cewa mazauna Abuja sun samu damar amfani da sabuwar hanyar sayen man fetur ta zamani bayan kaddamar da tashar mai ta farko mai tsarin zuba-da-kanka.
Sabuwar tashar da ke Bill Clinton Drive a Abuja ta hada sayar da man fetur, cajin motocin lantarki da sauran ayyukan sufuri da na rayuwar yau da kullum a wuri guda.
Tashar na aiki sa’o’i 24, inda kwastomomi za su iya zabar adadin man da suke bukata, su biya kudin da kansu kuma su samu damar yin hakan a kowane lokaci na dare ko rana.
Asali: Legit.ng
