'Mun Rike Wuta': Ministan Amurka Ya Yi Ikirarin Iran na Rokon a Yi Sulhu

'Mun Rike Wuta': Ministan Amurka Ya Yi Ikirarin Iran na Rokon a Yi Sulhu

  • Sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio ya bayyana halin da ake ciki game da yakin Amurka da Iran da ake ci gaba da gwabzawa
  • Rubio ya yi gargaɗin cewa Iran za ta ci gaba da fuskantar ƙarin matsin lamba idan ba ta sauya matsayinta a kan batun yarjejeniya ba
  • Ya kuma yi ikirarin cewa ƙungiyar Houthi ta kasarYemen ta shiga matsala ne sakamakon tasirin Iran, tare da zargin cewa an yaudare ta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

United States of America – Ministan harkokin wajen Amurka, Marco Rubio, ya ce Iran na neman a cimma yarjejeniya da Amurka yayin aka kara matsa matat da hare-hare.

Ya bayyana haka ne a gefen taron ƙasashen ASEAN da ake gudanarwa a birnin Manila a yayin da ake ci gaba da gwabza yaki a Gabas ta Tsakiya.

Kara karanta wannan

Iran ta tayar da gobara a sansanin sojin Amurka bayan sakin bama bamai

Amurka ta ce Iran ne neman sulhu
Shugaban Iran Masoud Pazeskian da Shugaban Amurka Donald Trump Hoto: Getty
Source: Facebook

Aljazeera ta wallafa cewa Rubio ya bayyana cewa gwamnatin Iran ba ta nuna shirinta na cimma yarjejeniya ba duk da irin matsin lambar da take fuskanta.

Sanatan Amurka ta soki Iran

Anadolu Ajansi ta kawo labarin cewa duk da Iran ta na neman alfarma a hau teburin sulhu, ba ta shirya sanya hannu a cimma yarjejeniya ba.

Ya ce:

"Iran na roƙon a cimma yarjejeniya. Da alama Iran ba ta shirya yin yarjejeniya ba, kuma za ta biya farashin hakan. A duk lokacin da suka yi yarjejeniya, ko dai su karya ta ko kuma su canza sharuddan."

Rubio ya sake jaddada cewa Amurka za ta ci gaba da ƙara matsin lamba kan Iran har sai ta sauya matsayinta ta amince a tsagaita wuta.

Ya ce:

"Farashin da Iran za ta biya yana ƙaruwa a kowace dare har sai sun dawo cikin hayyacinsu."

Ministan Amurka ya yi magana kan Houthi

Kara karanta wannan

'Yabon Trump ya nuna aikinmu ya na kyau': Fadar shugaban kasa

Ministan harkokin wajen Amurkan ya kuma yi tsokaci kan halin da ake ciki a Yemen, inda ya bayyana fatan cewa mayakan Houthi za su rage tashin hankalin da ake fama da shi.

Rubio ya danganta matsalolin ƙungiyar Houthi da tasirin Iran, yana mai cewa:

"Iran ta yaudare su."
Ministan Amurka ya yi magana kan Iran
Ministan harkokin wajen, Marco Rubio na jawabi a White House. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Kalaman nasa na zuwa ne a lokacin da ake ci gaba da fuskantar takun saƙa tsakanin Amurka da Iran kan batutuwan tsaro da kuma yiwuwar sake komawa kan tattaunawar cimma sabuwar yarjejeniya.

Har yanzu dai Iran ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance domin mayar da martani kan sabbin kalaman da Rubio ya yi.

Iran ta tayar da gobara a sansanin Amurka

A baya, kun samu labarin cewa dakarun IRGC na Iran sun ce sun kai hare-hare kan sansanonin sojin Amurka da ke Kuwait da Jordan a wani sabon mataki na rikicin da ke tsakanin ƙasashen.

Iran ta yi ikirarin lalata makaman soja, tsarin kariyar makamai masu linzami da wuraren ajiyar jiragen yaƙi tare da kashewa da jikkata sojojin Amurka kwanaki da hallaka wasu daga cikin sojojin kasar.

Yayin da Iran ke ci gaba da kai hare-hare, 'yan Republican a Majalisar Wakilan Amurka sun fara yunkurin amincewa da kasafin kuɗin Dala biliyan 95 don yakin da aka fara tun a watan Fabrairu, 2026.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng