Hukumar PSC Ta Fitar da Sunayen 'Yan Najeriya 50,000 da Ta Ɗauka Aiki, Ta Fadi Mataki na Gaba
- Gwamnatin tarayya ta fitar da sunayen mutane 50,000, wadanda suka yi nasara a daukar aikin ‘yan sandan a Najeriya
- Hukumar Kula da Ayyukan Yan Sanda (PSC) ta ce za a bude shafin duba sunaye da misalin karfe 12:00 na daren Alhamis
- Wadanda suka yi nasara har sunayensu suka fita za su je cibiyoyin horaswa domin gwajin lafiya da tantance takardu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Hukumar Kula da Ayyukan ‘Yan Sanda (PSC) ta fitar da sunayen wadanda aka dauka aiki a matssyin sababbin jami’an rundunar ‘yan sandan Najeriya.
Hukumar PSC ta ce sababbin 'yan sandan za su fita ne a matsayin kuratan 'yan sanda, bayan kammala horarwa da sauran matakan da ke gaba.

Source: Twitter
PSC ta saki sunayen sababbin yan sanda
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa Shugaban Sashen Hulda da Jama’a da Furotokol na PSC, Torty Kalu, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Laraba.
Sanarwar ta ce an gudanar da aikin daukar kuratan yan sandan ne tare da hadin gwiwar Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya, Hukumar Ɗa'ar Ma'sikata, Ma’aikatar Harkokin ‘Yan Sanda, da kuma Kwamitin Hulda da Jama’a da ‘Yan Sanda (PCRC).
Hukumar ta bayyana aikin daukar ma’aikatan a matsayin wanda aka gudanar cikin gaskiya, adalci da kuma bai wa kowa dama.
Yadda mutane za su duba sunayensu
Hukumar PSC ta bukaci duk wadanda suka rubuta jarabawar daukar aikin da su shiga shafin daukar ma’aikata na hukuma, npfapplication.psc.gov.ng domin sakamakonsu.
Sanarwar ta ce:
"Za a bude shafin daga karfe 12:00 na daren Alhamis, 16 ga watan Yulin 2026."
Hukumar ta kara da cewa wadanda suka yi nasara za su kuma samu sanarwa ta adireshin imel da kuma lambar wayar da suka bayar lokacin cike fom.
Za a yi gwajin lafiya kafin horaswa
PSC ta ce wadanda suka yi nasara za a sanar da su ranar da za su je cibiyoyin horaswar ‘yan sanda domin gudanar da gwajin lafiya da tantance takardu.
Hukumar ta gargadi cewa duk wanda bai halarta cikin lokacin da aka kayyade ba, za a dauka cewa ya yi watsi da damar aikin.

Kara karanta wannan
Umahi: Ma'aikaciyar jinya ta mutu a gida Minustan Tinubu, an zarge shi da boye gaskiya
Haka kuma, duk wanda bai tsallake gwajin lafiyar da tawagar likitocin ‘yan sanda za ta gudanar ba, za a bayyana shi a matsayin wanda bai cancanci aikin ba, kuma za a sallame shi daga horaswar.

Source: Twitter
Shugaban PSC ya yabawa Tinubu
Shugaban PSC kuma tsohon Mataimakin Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, DIG Hashimu Argungu (mai ritaya), ya gode wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa amincewa da daukar sabbin jami’an ‘yan sanda 50,000.
Argungu ya kuma bukaci wadanda suka samu aikin su gudanar da aikinsu cikin kwarewa, gaskiya da sadaukarwa, kamar yadda Punch ta rahoto.
Ya ce:
"Ina kira ga wadanda suka yi nasara da su dauki wannan dama a matsayin kira na yi wa kasa hidima cikin mutunci, rikon amana da jajircewa domin tabbatar da Najeriya mai zaman lafiya da tsaro."
Yan sanda akalla 5,000 za su yi ritaya
A wani labarin, kun ji cewa hukumar kula da fanshon ’yan sandan Najeriya ta bayyana adadin jami'an da za su yi ritaya daga aiki a shekarar 2026.
Hukumar ta bayyana cewa fiye da jami’an ’yan sanda 5,000 ake sa ran.za su yi ritaya daga aiki a shekarar nan da muke ciki.
Ta bayyana hakan ne yayin wani shirin wayar da kai da aka gudanar a Kano ga tsofaffin jami’an ’yan sanda da kuma waɗanda aka tsara za su yi ritaya a 2026.
Asali: Legit.ng
