Tsare El Rufai: Matar Tsohon Gwamna Ta Yi Rubutun Cikarsa Kwanaki 150 a Garkame

Tsare El Rufai: Matar Tsohon Gwamna Ta Yi Rubutun Cikarsa Kwanaki 150 a Garkame

  • Asia El-Rufai ta yi rubutu game da kama mai gidansu da aka yi na kwanaki 150 ba tare da an yi hukunci ba
  • Rubutun da ta yi ya nuna cewa tsare shi na tsawon lokaci haka babu beli ya saba ka'idojin adalci da shari'a
  • Marubuciyar ta ya yi kira ga abokan hulɗar ƙasa da ƙasa na Najeriya da su fito su yi magana a kan lamarin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Asia Ahmad El-Rufai ta yi wani dogon rubutu a ranar da mai gidansu ya cika kwanaki 150 yana tsare a hannun hukuma.

Matar tsohon gwamnan ta sanar da duniya halin da Mallam Nasir El-Rufai yake ciki tunda jami’an tsaro suka kama shi a Najeriya.

Nasir El-Rufai
Nasir El-Rufai yana addu'a da Bola Tinubu wajen taro Hoto: @CaptJamyl/Getty Images
Source: UGC

Asia El-Rufai ta yi rubutu a jaridar duniya

Asia Ahmad El-Rufai ta wallafa rubutun ne a jaridar The African Report, a nan ta soki abin da ta kira rashin adalci da ake yi masa.

Kara karanta wannan

Buba Galadima: "Akwai kalubale kan tikitin Obi da Kwankwaso"

"Yau ina rubutu ba a matsayin ‘yar siyasa ko lauya ba, sai dai a matsayin matar aure, uwa kuma ‘yar Najeriya
"A ranar da Mallam Nasir El-Rufai ya cika kwanaki 150 a tsare, ina kira ga masu karatu da ke wajen Najeriya su tsaya su yi nazarin abin da hakan yake nufi.
"Kwanaki 150 yana nufin watanni 5 ba a samu abinci ba, ba tsaida sallah ba, ba a samu damar yin makokin mahaifiyar da ta cika ba, babu zama a tattauna da iyali, an samu yankewar kula wa da lafiya, lokacin da ba zai taba dawo wa ba"

- Asia Ahmad El-Rufai

'An manta da damukaradiyya a shari'ar El-Rufai'

Hajiya Asia ta ce mijinta ba bakon tsokano abin magana ba ne, ya yi shekaru 20 yana aikin gwamnati daga lokacin da ya rike BPP.

Bayan hukumar BPP, ya yi Ministan harkokin Abuja daga nan ya zama gwamnan Kaduna inda ta ce ya sha yabo da kuma suka.

Ta ce yabo da suka su ne gishirin damukaradiyya, akasin abin da ta ce yana faruwa da shi yanzu tun da jami’an tsaro suka cafke shi.

Kara karanta wannan

Sanusi II ya gano abin da ake bukata don rage talauci a Najeriya

Rubutun ya zargi gwamnati da yi wa El-Rufai azuba kafin a yi shari’a, baya ga cafke shi da aka yi babu gargadi tamkar bai da kima.

Bello El-Rufai ya wallafa rubutun a shafin X

Azabar da Malam El-Rufai ya sha a tsare

Matar tsohon gwamnan Kadunar ta dauko labarin yadda aka nemi a damke shi tun a filin jirgi, aka karbe masa fasfo ba a kan ka’ida ba

Bugu da karin ta koka da cewa ya kwanta rashin lafiya sosai har yana fitar da jini ta hanci da baki, amma ba a ba shi wata kulawar likitoci ba.

Nasir El-Rufai
Nasir El-Rufai da mai dakinsa Asia Ahmed da wasu 'ya 'yansu a gida Hoto: @elrufai
Source: Twitter

Duk da ta yarda cewa babu jami’in gwamnati da ya fi karfin a bincike shi idan akwai hujja, ta ce bai kamata a nuna son kai a binciken ba.

Rubutun ya koka da yadda a wasu kasashen Afrika ake amfani da gwamnati wajen ganin bayan wadanda suke bangaren ‘yan adawa.

Lauyar ta ce bai dace Bola Tinubu ya taso mijinsu a gaba ba saboda kurum bai tare da shi, ta yi kira ga duniya ta lura da abin da ke faruwa.

Kara karanta wannan

Umahi: A karshe ministan Tinubu da aka tsinci gawar budurwa a gidansa ya fadi abin da ya faru

Hukuma ta damke wasu mutanen El-Rufai

Za a ga Asia El-Rufai ta kafa misali da Joel Adoga, Jimi Lawal da likitan tsohon gwamnan, Abubakar Bello, da duk an garkame su.

Sahara Reporters ta rahoto ta tana mai cewa yin adalci, bin ka’ida da mutunta ‘dan adam ya zama wajibi a kan Gwamnatin Najeriya.

"Ba na kira ga duniya ta wanke mijina. Abin da nake neman kawai shi ne a bi ka’idar dokokin Najeriya da kundin tsarin mulkin da aka yi rantsuwa za a kare."

- Asia El-Rufai

Mahafiyar Nasir El-Rufai ta rasu

An ji mahaifiyar tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai, mai suna Hajiya Umma El-Rufai, ta riga mu gidan gaskiya.

Jikanta kuma ɗan majalisa mai wakiltar Kaduna ta Arewa, Hon. Mohammed Bello El-Rufai, ne ya sanar da rasuwarta a shafinsa na X.

Tsohuwar ta cika ne a ranar Juma'a, 27 ga watan Maris 2026 lokacin tsohon gwamnan yana tsare, daga baya an kyale shi ya je jana'iza.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng