Za a mayar da gidan shugaban kungiyar Boko Haram na tarihi

Za a mayar da gidan shugaban kungiyar Boko Haram na tarihi

Kwamishinan yada labarai na jihar, Dr. Mohammed Bulama, ya fadi hakan a Dutse, jihar Jigawa, inda ya halarci wani taro da ma'aikatar sadarwa ta kasa ta shirya.

Gwamnatin jihar Borno, ta bakin kwamishinan yada labarai na jihar, Dr. Mohammed Bulama, ta sanar da cewar ta kammala shirin mayar da gidan tsohon shugaban kungiyar Boko Haram da aka rushe gidan tarihi.

Za a mayar da gidan shugaban kungiyar Boko Haram na tarihi
Kashim Shettima

Kwamishinan ya ce za su adana duk wasu kayayyakin kungiyar Boko Haram domin amfanin masu neman bayani a kan kungiyar da kuma ma su yawon bude ido.

DUBA WANNAN: Dakarun Sojin Najeriya sun dakile harin mayakan kungiyar Boko Haram ranar Asabar

Bayan kama Muhammed Yusuf a shekarar 2009 jami'an tsaro sun rushe gidansa dake cikin garin Maiduguri.

Bulama ya ce gidan na Muhammed Yusuf nan ne tushen kungiyar Boko Haram, a saboda haka suka yanke shawarar sake gina gidan tamkar yadda yake kafin a rusa shi.

Kisan Muhammed Yusuf dai ya zama tamkar an kashe maciji ba a sare kai ba domin har yanzu mayakan kungiyar da ya kafa suna nan suna cigaba da kisan mutane musamman a yankin arewa maso gabashin Najeriya.

Kungiyar ta Boko Haram na cigaba da kai munanan hare-hare 'yan kwanakin nan domin ko a yammacin ranar Asabar saida mayakan kungiyar suka kai hari karamar hukumar Magumeri bayan wani harin da suka kai a Mubi ta jihar Adamawa satin da ya wuce.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: